Amurka ta gargadi Syria da kada ta tura wa Hezbollah makamai

Amurka ta shaidawa Syria cewa kada ta tura makamai zuwa ƙungiyar Hezbollah, ƙawarta a Lebanon, tana mai cewa irin wannan yunƙuri zai ƙara dagula al'ammura a yankin.
Jiya Laraba Isra'ila ta kai harin jiragen sama, wanda Amurka ta ce an kai shi ne a kan wasu jerin gwanon motoci dake ɗauke da makamai masu linzami na kakkaɓo jiragen sama da aka ƙera a Rasha .
Syria dai ta yi wa Majalisar Dinkin Duniya ƙorafi game da harin, wanda ta ce an kai shi ne kan wata cibiyar bincike ta sojoji dake kusa da Damascus, babban birnin ƙasar.
Wakilin BBC ya ce harin ya auku ne kusa da iyakar Syria da Lebanon, kuma jami'an diflomasiyya a Amurka sun yi ammanar cewa 'yan ƙungiyar Hezbollah aka yi niyyar kaiwa makaman.







