An yi arangama tsakanin matasa da masu kishin Islama a Mali

Asalin hoton, AFP
Daruruwan matasa 'yan kasar Mali ne suka yi wata taho mu gama da masu kishin islama dake iko da yankin a wata zanga-zangar adawa da tursasa musu amfani da shari'ar musulunci.
An gudanar da zanga-zangar ne a birnin Gao, bayan da masu kishin islaman suka sanar da shirin su na yanke hannun wani barawo.
Dakarun da ke iko da yankin sun yi harbi a sama domin tarwatsa masu zanga-zangar.
Mutane da dama ne suka samu raunuka a zanga-zangar, ciki har da wani dan jarida da 'yan bindiga suka daka saboda ya sanar da shirin yanke hannun barawon a Radiyo.mali






