Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaɓen Najeriya 2023: Sakamakon zaɓen gwamnan jihar Adamawa
Yayin da ake ci gaba da bayyana sakamakon zaɓen gwamna da aka kammala a jihar Adamawa, an jibge jami'an tsaro a wurin da ake bayyana sakamakon zaben a Yola, babban birnin jihar.
A cibiyar ce ake sa ran sanar da sakamakon zaɓen a ranar Lahadi.
An ɗage bayyana sakamkon zaɓen da daddare a ranar Asabar, inda babban jami'in bayyana sakamakon zaɓe na jihar ya sanar cewa za a ci gaba da ƙarfe 11 na safiyar ranar Lahadi.
Al'ummar jihar dai na nan suna dakon sakamakon, kamar sauran al'ummun wasu jihohin da aka gudanar da zaɓen na ranar Asabar 15, ga watan Afurilu.
An gudanar da zaɓen ne a rumfunan zaɓe 67, inda aka kasa kammala zaɓe na ranar 18 ga watan Maris, wanda a sanadiyyar haka ne INEC ta ce zaɓen bai kammala ba.
A sakamakon zaɓen 18 ga watan Maris da INEC ta bayyana, gwamna mai ci na jam'iyyar PDP, Ahmadu Fintiri ne ke kan gaba da ƙuri'a 421,524, yayin da Sanata A'isha Dahiru Binani ta jam'iyyar APC ta samu ƙuri'a 390,275.
Adamawa na da yawan mutanen da suka yi rajistar zaɓe 2,196,566.
Mutum goma sha biyar ne ke takarar kujerar gwamnan, ciki har da gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jam`iyyar da Sanata Aishatu Dahiru Binani ta jam`iyyar APC, da Umar Ardo na jam`iyyar SDP da kuma Mohammed Usman Shuwa na jam`iyyar ADC.
Za ku iya ganin sakamakon zaɓen gwamnonin sauran jihohin na Najeriya a ƙasa: