Zaɓen Najeriya 2023 - 'Kun bari an sace ni, kuma yanzu kuna so na zaɓe ku'

Aisha Mama da ke hagu, sai da ta bar gida saboda harin da aka kai wa ƙauyensu

Asalin hoton, NDUKA ORJINMO/BBC

Bayanan hoto, Aisha Mama da ke hagu, sai da ta bar gida saboda harin da aka kai wa ƙauyensu
    • Marubuci, Nduka Orjinmo
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Bakiyawwa, Katsina state

Matsalar sace-sacen mutane domin neman kuɗin fansar ta fi ƙamari ne musamman a yankin arewa maso yammacin Najeriya inda dubban mutane suka tsere wa muhallansu.

Rashin tsaron na nufin yankuna da dama, wanda suke da yawan masu rijistar zaɓe, ba za su yi zaɓe ba a ranar 25 ga watan Fabirairun da za a gudanar da zaɓe mai zuwa.

Wani dogon titi mara shinge wanda ya ƙare da wasu bishiyoyi, shi ne hanya guda ta kai wa ga ƙauyen Bakiyawwa da ke jihar Katsina a arewacin Najeriya

Ƙauyen da babu kowa sai manoma, ba wuri ba ne da za ka yi tunanin cewa masu neaman kuɗin fansa za su je domin ɗaukar mutane.

Abu ne da ya zo wa kowa da mamaki, dan haka a watan Satumbar da ya gabata da masu garkuwa da mutane suka je ƙauyen sai da suka kwashi mazauna yankin 57.

"Sun kama matata har tsawn kwana 38," in ji Abduljabbar Muhammed wani ma'aikacin gwamnati da ake wa kallon mai wadata. Sai da ya biya kimanin naira miliyan daya, ($2,100; £1,700) kafin a sake ta.

Zahraddeen Musa ya ce ba zai iya faɗin nawa ya bai wa masu garkuwa da mutane ba, amma ya ba su kuɗi masu yawa

Asalin hoton, NDUKA ORJINMO/BBC

Bayanan hoto, Zahraddeen Musa ya ce ba zai iya faɗin nawa ya bai wa masu garkuwa da mutane ba, amma ya ba su kuɗi masu yawa

"Na basu gaba ɗaya kudi na da babur ɗina, sannan na roƙesu kada nima su ɗauke ni," in ji Zaradeen Musa ɗan shekara 30, wanda aka karya kofar gidansa cikin dare da misalin 01:00 yayin da 'yan fashin daji suka kai wani hari da suka shafe sa'o'i huɗu suna gabatarwa babu wanda ya ƙalubalance su.

Mariya Sani wata mata mai shekara 45 an kamata, amma ta zille lokacin da 'yan bindigar ke shigar da mutanen da suka kama cikin daji, inda maɓoyarsu take.

An barta da tunanin mai zai faru da ita da a ce ba ta tsere daga hannun waɗan nan mutane ba, kamar dai yadda sauran suka tsinci kansu, itama ba za ta iya biyan kuɗin fansar ba.

Duka waɗanda aka kaman a ƙarshe an sake su bayan shafe kimanin wata ana yarjejeniya da ta kai su ga biyan kudin fansa ko kuma su bayar da wasu abubuwan masu ƙima kamar babura.

Wannan ya nuna irin yadda satar mutane ta yi ƙamari - ta yadda ko talakawa ma ba su sha ba.

Amma duk da haka, mutanen Bakiyawwa za su godewa Allah idan suka yi la'akari da wasu hare-haren da ake kaiwa da suke kai ga rasa rayuwa, irin wanda aka ce an kashe yan cintiri sama da 100 a Katsina a ranar Juma'a.

Zaben Najeriya 2023: Waɗanne alƙawura ne jam'iyyu suka yi muku

Zaɓi wani batu da jam'iyya domin ganin tsare-tsare

Tsare tsaren Jam'iyyu

  • All Progressives Congress

  • Labour Party

  • New Nigeria Peoples Party

  • Peoples Democratic Party

End of Zaben Najeriya 2023: Waɗanne alƙawura ne jam'iyyu suka yi muku

Wannan masu garkuwa da mutanen da ke arewaci da kuma masu kashe-kashen da ke kudu maso bagas, kan iya kawo tsaiko ga babban zaben Najeriya da za a yi ranar 25 ga watan Fabirairu, kamar yadda masu fashin baƙi ke cewa.

Harin da aka kai wa ofishin INEC a 2019 ya sanya an ɗage zaɓe da mako guda, kuma ƙone wani ofishin INEC ɗin da aka yi a yankin kudu maso gabashin ƙasar ya sanya firgicin cewa za a iya ɗage zaben a wannan lokacin, ko da yake jami'ai sun ce babu gudu babu ja da baya.

Ko a watan Disamba sai da INEC ɗin ta ce, abu ne mai haɗari a gudanar da zaɓuka a wasu yankunan Katsina, sai dai babu kuma wanda ya san mai zai faru a ranar zaɓe mai zuwa.

"Kun bar masu garkuwa sun kama ni, yanzu kuma kuna so na zaɓe ku," in ji Mariya.

Kamar dai mafi yawan mutane a nan ita ma a baya Shugaba Muhammadu Buhari ta zaɓa a baya, amma a wannan karon ta dawo daga rakiyar 'yan siyasar.

...

Shugaba Buhari sai sauka daga mulki bayan shafe wa'adi biyu, yanzu kuma Bola Tinubu ne ke neman gadarsa a ƙarƙashin jam'iyyar APC da ke mulki a Najeriya.

"Ta yaya zan zaɓi APC duk da irin wahalar da muka shiga?" in ji Lawal Suleiman, tsohon ɗan jam'iyyar ta APC, amma yanzu yana tare da jam'iyyar Labour ta Peter Obi.

Mutane da yawa a Bakiyawwa na cewa su yanzu babbar jam'iyyar hamayya ta PDP za su zaɓa a dukkan matakai.

"Idan Buhari bai iya kawo ƙarshen waɗan nan matsalolin ba na Najeriya, ta wanene zai iya, in ji Nana Sama'ila wata wadda ta tsere daga ƙauyensu na Batsari shekaru uku baya.

A bayan nan, 'yarta Aisha Mama ta gudu ta bar mijinta da ke ƙauyen Dangayya saboda yawan hare-haren da ake kai musu cikin dare da gonakinsu sama da mako guda a jere.

Ta ce ganin Buhari ya fito daga Katsina ya sa ta riƙa zaɓarsa tun daga 2003, da fatan zai kawo ƙarshen matsalolin da ake fuskanta, amma yanzu ta ce ta dawo daga rakiyarsa saboda gazawar gwamnatinsa.

An sace ɗaruruwan yara 'yan makaranta an kuma sake su daga baya, gwamnatin jihar a baya ta taɓa umartar mutanenta da su ɗauki makamai domin kare kansu daga sherrin maharan, wani abu da ya nuna tsananin gazawarta.

Ɗan takarar ta su, ya aminta da matsalar tsaro da ake fama da ita, wadda ta haɗu da tsadar kayan abinci da ta janyo hauhawar kayayyaki, waɗanda sune matsalar da ta sanyo Najeriya a gaba.

Atiku Abubakar ɗan takarar jam'iyyar PDP da Tinubu nda APC da Obi na LP dukansu na ganin akwai buƙatar a yi wa tsarin 'yan sanda garanbawul, haka na na soji da tsarin walwala da dai sauransu.

"Ya lalata tattalin arziƙi, ga rashin tsaro ya baibaye ko ina," in ji Mohammed Yusuf, wani tsohon manoni a Katsina wanda matsalar tsaro ta sa ya koma sana'ar sayar da shayi da Indomi a jihar Kano.

Manomin ya ce zai zaɓi jam'iyyar PDP a wannan karon

Asalin hoton, NDUKA ORJINMO/ BBC

Bayanan hoto, Manomin ya ce zai zaɓi jam'iyyar PDP a wannan karon

Kano da Katsina da kuma Kaduna, jihohi ne da ake ɗauka da muhimmanci ga duk wanda yake son zama shugaban Najeriya saboda yawan waɗanda suka yi rijista a yankin. Yawan rijistar waɗan nan jihohi ya fi na jihohi biyar a yankin kudu maso gabshi.

Ƙuri'un waɗan nan jihohin ne suka bai wa Buhari damar cin mulki har sau biyu a jere, sai dai har yanzu wasu na nuna goyon baya ga APC, akwai masu tunanin jam'iyyar ta mutu a yankin da rashin tsaro ya haifarwa koma baya.

Makonni biyu da suka gabata, jifan da aka yi wa jirgin shugaba Buhari da ya je ziyara Kano ya isa ya zama shaida kan hakan.

Akwai kuma wani ɗan takarar da yake da ƙarfi a yankin, Rabi'u Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP.

Mabiyansa na fatan shi ne zai zama shugaban ƙasa na gaba, sai dai wasu na kallon za a nemi goyon bayansa ne domin tabbatar da wanda zai zama shugaban ƙasar na gaba.

Babu shakka tsohon gwamnan Kano kuma wanda ya taɓa zama ministan tsaro sau ɗaya yana da mabiya na gani kashe ni a Kano da makwabciyarta ta Jigawa.

Idan har ya iya cinye duk ƙuri'un jihar Kano miliyan shida, wanda ita ke biyewa Legas a yawa, hakan zai shafi duka 'yan takarar, musamman na APC da PDP.

Kwankwaso shi ma kamar sauran 'yan siyasar Najeriya yake, ya sauya sheƙa daga wannan jam'iyya zuwa wannan, a bara ya goyi bayan PDP, kuma a yanzu ana ganin lokaci kawai yake jira ya janye wa Atiku Abubakar.

"Shi da Obi ba za su iya cin zaɓe ba, duk da dai sun fi Atiku wanda ake wa kallon ɗan kama karya," in ji Umar Yahaya wani ɗalibi a jami'a a Kaduna.

Yayin da aka rantsar da shugaba Buhari a 2016, an ta fatan cewa za a samu ci gaba a yankin arewaci, amma yanzu hakan ya zama wani abin tashin hankali ga yankin.