Bayanai kan 'yan takarar gwamnan Jihar Osun

A ranar Asabar 16 ga watan Yulin 2022 ne za a yi zaben gwamna a Jihar Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Gwamnan jihar mai ci Adegboyega Oyetola na jam'iyyar APC na daga cikin ƴan takarar, inda yake neman yin ta-zarce.

Akwai wasu mutum 13 da suke takarar da shi daga jam'iyyu daban-daban.

Ga dai bayanai kan wasu ƴan takarar. An zaɓe su ne bayan da BBC ta gudanar da ƙuri'ar jin ra'ayoyin jama'a na ƴan takarar da suke kan gaba-gaba a zaɓen.

Ƴan takarar gwamna na Osun

  • Sana'a: Gwamna, Ƙwararre kan sha'anin kuɗi
  • Shekaru: Shekara 68
  • Adegboyega Oyetola shi ne gwamnan Jihar Osun mai ci a yanzu.
  • Ɗan asalin Iragbiji na ƙaramar hukumar Boripe ne.
  • Yana da digiri a harkar inshora da kuma digiri na biyu daga Jami'ar Lagos.
  • Kafin ya zama gwamna a shekarar 2018, shi ne shugaban ma'aikata na Gwamna Rauf Aregbesola, wato mutumin da ya gada.
  • Sana'a: Ɗan kasuwa
  • Shekara: 62
  • A shekarar 2021 ya samu shaidar kammala karatun digiri a fannin shari'a kan manyan laifuka a Kwalejin Atlanta Metropolitan a Amurka.
  • Ya tsaya takarar sanatan Osun ta Yamma a 2017 a zaben cike gurbi bayan rasuwar ɗan uwansa Isiaka Adeleke.
  • Ya sake tsayawa takara ya fadi a zaben gwamna na 2018 na jihar Osun.
  • Dan asalin garin Ede ne.
  • Sana'a: Ƙwararren mai zanen gine-gine
  • Shekara: 58
  • An haife shi a Osogbo a 1964
  • Yana da digiri na farko da na biyu daga Jami'ar Obafemi Awolowo (OAU) a Ile-Ife.
  • Daga baya ya ƙara yin digiri na biyu har guda biyu a sha'anin gudanar da kasuwanci da a fannin safiyon ƙasa da fasahar zamani daga Jami'ar Ilorin da ta Ibadan.
  • Ya taɓa riƙe matsayin mataimakin shugaban jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).
  • Shekara: 59
  • An haifi Akin Ogunbiyi a Ile-Ogbo, Jihar Osun.
  • Ya yi karatun digiri kan tsimi da tanadi a Jami'ar Obafemi Awolowo sannan ya yi digiri na biyu a Jami'ar Navarra da ke Barcelona a Spain.
  • Mamaba ne na Cibiyar Ƙwararru kan harkar inshora ta London.
  • Ya taba zama ɗaya daga cikin daraktocin Bankin Ayyukan Raya Ƙasa da na Kamfanin Mutual Benefits Assurance da sauran wasu kamfanonin.
  • Yusuf Sulaimon Lasun ɗan asalin ƙaramar hukumar Ilobu Irepodun ta jihar Osun ne.
  • Ya yi digiri na ɗaya da na biyu a kan injiniya a Jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ibadan.
  • Shi ne kuma jami'in hulɗa da jama'a na jam'iyyar AD na jihar a lokacin mulkin Cif Bisi Akande. An naɗa shi shugaban hukumar raya da cigaban babban birnin jihar Osun OSCTDA a 2014.
  • Sau biyu yana riƙe muƙamin ɗan majalisar wakilan tarayya,sannan ya yi mataimakin kakakin majalisa daga 2015 zuwa 2019.

Kalli jerin sunayen 'yan takarar tare da jam'iyyunsu da hukumar zaben kasar ta fitar

  • A: Akinade Akanmu Ogunbiyi
  • AAC: Awojide Peter Segun
  • ADP: Kehinde Munirudeen Olumuyiwa A Atanda
  • APC: Adegboyega Isiaka Oyetola
  • APM: Awoyemi Oluwatayo Lukuman
  • APP: Adebayo Adeolu Elisha
  • BP: Adeleke Adesoji Masilo Aderemi Adedapo
  • LP: Yussuff Sulaimon Lasun
  • NNPP: Rasaq Oyelami Saliu
  • NRM: Abede Adetona Samuel
  • PDP: Adeleke Ademola Jackson Nurudeen
  • PRP: Ayowole Olubusuyi Adedeji
  • SDP: Omigbodun Oyegoke Akinrinola
  • YPP: Ademola Bayonle Adeseye
  • ZLP: Adesuyi John Olufemi

Babu 'yar takara mace

'Yan takara 15 ne za su fatata a zaben na gwamnan jihar Osun, kuma babu mace ko daya a cikinsu.

Haka kuma a cikin 'yan takarar 15, shida ne kawai daga ciki suka dauki mata a matsayin mataimaka.

Batun rashin 'yar takara mace a zaben na gwamnan Osun, ya kara nuna karara cewa maza ne suka mamaye fagen siyasar Najeriya, kuma wakilcin mata a fagen kullum raguwa yake, duk da kiraye-kirayen da kungiyoyi ke yi ne cewa mata su shiga a dama da su domin gina kasa.

Tun da aka kirkiri jihar, ba a taba zabar mace a matsayin gwamna ba.

Tarihin zabukan gwamna bakwai a jihar osun

Zaben gwamnan shi ne irinsa na bakwai da aka taba yi jihar.

An kirkiri jihar Osun karkashin mulkin soji na Ibrahim Babangida, daga tsohuwar jihar Oyo a ranar 27 ga watan Agustan 1991.

Isiaka Adeleke, dan uwa ga dan takarar jam'iyyar PDP ne ya fara zama gwamnan jihar a watan Janairun 1992 zuwa Nuwamban 1993, lokacin da gwamnatin mulkin soji karkashin Ibrahim Babangida ta rusa mukaman siyasa bayan soke zaben June 12

Ya ake lashe zaben gwamnan?

Tsarin hukumar zaben ya tanadi zagaye biyu, da fari kafin dan takara ya lashe zaben, yana bukatar samun rinjayen yawan kuri'un da aka kada, sannan ya samu kashi 25 cikin dari na kuri'un da aka kada a biyu bisa uku na kananan hukumomin jihar.

Idan babu dan takarar da ya samu nasara a wannan matakin, sai a je zagaye na biyu tsakanin 'yan takara biyu da suka fi samun rinjayen kuri'un.

A zagaye na biyun, duk mutumin da ya samu rinjayen kuri'un a mafi yawan kananan hukumomin jihar shi ne ya lashe zaben.

Jerin sunayen tsoffin gwamnonin jihar

  • Isiaka Adeleke: daga Janairun 1992 zuwa 1 ga watan Nuwmban 1993
  • Adebisi Akande: Daga 29 ga watan Mayun 1999 zuwa 29 ga watan Mayun 2003
  • Olagunsoye Oyinlola: daga 29 ga watan Mayun 2003 zuwa 26 ga watan Nuwamban 2010
  • Rauf Aregbesola: Daga 26 ga watan Nuwamban 2010 zuwa 26 ga watan Nuwamban 2018
  • Adegboyega Oyetola: Daga 26 ga watanNuwamban 2018 zuwa yanzu.

Wa'adin mulkin gwamna Gboyega Oyetola zai kare a karshen watan Nuwamban 2022, daga nan ne kuma wa'adin sabon zababben gwamna zai fara.

Osun candidates guber

Asalin hoton, Others