Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mata 'yan Najeriya da suka je Dubai neman aiki sun shiga tasku
Wasu mata 'yan asalin Najeriya da suka tafi neman aiki a kasashen Larabawa na yankin Gabas ta Tsakiya, sun makale a Dubai.
Da dama daga cikin matan dai na cikin mawuyacin hali bayan da suka ce ejandinsu ya zambace su tare da yaudarar cewa zai samar musu aiki amma hakan bai yiwu ba.
Wasu daga cikin wadannan mata da BBC ta tattauna da su sun ce, an yaudare su ne a kan cewa za a sama musu aiki shi ya sa suka bar kasarsu ta asali suka tafi can.
Wata daga cikinsu da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa BBC cewa, yanzu haka tana Dubai inda ta je ta sanadiyyar ejadinta don a sama mata aiki.
Ta ce, "Ya turo ni na taho kuma na shafe kwanaki amma har yanzu ban san matsayin da nake ba, don tun daga filin jirgi na fara gamuwa da matsala saboda shi wanda zai tarbe ni bai je ba haka na kasance a can dan kudin da ke hannuna gaba daya sai ya tafi a kudin mota.
Matar ta ce, a yanzu tana zaune ne a wani gidan haya, kuma ga shi ba ta ga ejan din nata ba wanda dama tuni ta ba shi kudin alkawarin samo aikin da suka yi, don sun karkare ne a kan naira miliyan daya da rabi, to ta bashi dubu 500.
Ta ce," Na ba shi kudin ne a kan idan na zo na samu aiki zan cika masa, to a gaskiya a yanzu babu aikin ga shi ba ni da ko durham daya a tare da ni, don haka ni yanzu abin da nake so shi ne idan har ban samu abin da zan dogara da kaina ba, to gara na koma kasata cikin mutuncina."
Matar ta ce, a yanzu da-na-sani take yi don ta sha kuka ba iyaka tun da ta je kasar.
Kazalika wata daga cikin matan ma da BBC ta tattauna da su, ta ce a yanzu ta shafe fiye da makonni biyu a Dubai, kuma eja dinta mace ce a Kano, ta kuma ba ta kudi har naira miliyan daya da rabi don a samo mata aikin.
Ta ce,"Eja din tawa cewa ta yi za ta samar mini aikin koyarwa a Saudiyya, to sai ga shi an kai mu Dubai, ko da muka je filin jirgin saman kasar sai da muka shafe sa'oi 26 ba abinci muna jiran mai tarbar mu."
Matar ta ce, da suna cikin otal, to amma a yanzu an kai su wani gida, ga kuncin rayuwa ba abinci ga shi ba a taimako a Dubai.
Ta ce," Mun yi karatu a kasarmu saboda rashin aikin yi ne muka fito nema, ga shi mun zo inda idan ba ka da abin yi sai ka bayar da mutuncinka za ka ci abinci."
Matan da a ya yanzu haka ke Dubai sun ce rashin aikin yi ne ya sa suka bar kasarsu suka je Dubai don su samu abin yi.