Zainab Hassan: Matashiyar Bahaushiya da ke yi wa WizKid da Yemi Alade kwalliya

Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Zainab Hassan, wata matashiyar Bahaushiya da aka haifa a Birtaniya, ta bayyana abin da ya ja hankalinta ta koyi sana'ar kwalliya.

A wata hira ta musamman da BBC Hausa, matashiyar ta ce tun tana karamar yarinya take sha'awar kwalliya kuma hakan na ba ta sha'awa ko da yake ba ta iya ba.

"Amma da na girma shi ne na fara gwadawa kuma ya ba ni sha'awa sosai; shi ne nake so na kware a kai," in ji ta.

Ta kara da cewa tana yi wa fitattun mawaka irin su Wizkid da Yemi Alade kwalliya.