Mata a Moroko sun zargi attajirin Faransa Jacques Bouthier da yi mu su fyade

Wasu mata hudu a kasar Maroko sun shigar da kara kan zargin cin zarafi ta hanyar lalata kan dan kasuwar nan na Faransa Jacques Bouthier.

Yanzu suna tsakanin shekara 26 zuwa 28, kuma sun yi wa kamfaninsa da ke Tangier aiki.

Matan dai sun ce an kore su ne bayan sun ki amincewa da tsangwama da kuma tursasawa.

Dan kasuwan mai shekara 75 na fuskantar bincike a hukumance a Faransa kan laifin yi wa wata karamar yarinya fyade da kuma fataucinta. Sai dai ya ce shi ne aka zalunta.

Jacques Bouthier wanda ake ganin yana daya daga cikin manyan attajiran Faransa, ya yi murabus a matsayin shugaban kamfanin inshora na Vilavi, wanda a da ake kira Assu 2000, a watan Mayu.

A ranar Juma'a, kungiyar kare hakkin wadanda aka ci zarafinsu ta Moroko ta gudanar da taron manema labarai game da zargin da ya faru a Tangier tsakanin 2018 zuwa Afrilun 2022.

Wasu daga cikin wadanda ke zargin Mista Bouthier da cin zarafinsu sun bayyana sanye da abin rufe fuska da tabarau mai duhu don kada a gane su, don su fada wa yan jarida abubuwan da suka faru.

Kamfanin dillancin labara na AFP ya ambato daya daga cikinsu tana cewa: "Ya bukaci ya kwana da ni, sai na ce a'a, sai ya ce in gabatar da shi ga wata 'yar uwa, ko kawata, ya ce zai ba ni kyauta mai kyau idan na yi hakan."

Matan sun kuma zargi wasu manyan shugabannin kamfanin 'yan Faransa da Moroko da hannu a cikin al'amarin.

"Jacques da kansa ba abin tsoro ba ne, amma tare da abokansa, musaman idan sun hadu a Tangier, a lokacin ne yake komawa wani abin tsoro. Don haka suka fara tursasa ni tare da tsangwama ta, kuma wannan ya sa na ajiye aikin," a cewar wata matar.

'Yan sandan Faransa na zargin dan kasuwar da ajiye wasu mata masu shekaru kasa da 18 su bakwai a wani gida na tsawon shekaru da dama.

Jami'ai a Faransa sun fara bincike a farkon wannan shekara lokacin da wata mata mai shekara 22 ta je ofishin 'yan sanda a babban birnin kasar, Paris, tana mai cewa ta shafe shekara biyar a hannun sa kuma ya tilasta mata yin jima'i domin ya ba ta abinci da wurin kwana.