Gurbatacciyar iska na rage tsawon rayuwar Indiyawa da shekara 10

Delhi air pollution

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gurbatacciyar iska na kashe miliyoyin mutane a Indiya a kowacce shekara

Gurbatacciyar iska tana rage tsawon rayuwar mutane da shekaru 10 a birnin Delhi, na Indiya, birni mafi yawan al'umma a duniya, a cewar wani rahoton bincike na Amurka.

Binciken ya kara da cewa tsawon rai a Indiya a matsakaicin yanayi ya ragu da shekara biyar saboda yanayin iska da ake shaƙa mara kyau.

Al'ummar Indiya biliyan 1.3 na rayuwa a yankunan da ke fitar da gurɓatacciyar iska da suka gaza cimma muradan WHO na daƙile shakar iska mara tsafta, a cewar binciken.

Gurbatacciyar iska na kashe miliyoyin mutane a Indiya a kowacce shekara.

Hazon da ke mamaye sararin samaniyar Indiya a lokacin hunturu, na ƙunshe da ɓurɓushin sinadaran gubar da ake kira PM2.5 - da ke iya maƙalewa a huhun mutum da haifar da tarin cututtuka.

Kididdigar matsayin ingancin kyawun iskar da ake shaƙa na cibiyar makamashi ta EPIC a Jami'ar Chicago, na nuna cewa mutum kimanin miliyan 510 da ke rayuwa a arewacin Indiya.

Kusan kashi 40 cikin 100 na al'ummar Indiya - na hanyar rasa shekara bakwai da rabi na tsawon rayuwarsu, idan aka kwatanta da yawan al'ummarta a yanzu.

Ko da yake, rage yawan fitar da iska mai gurbata muhalli zuwa matakin da WHO ke gangami a kai, na nufin mutum miliyan 240 a arewacin jihar Uttar Pradesh a arewacin indiya tsawon ran su zai ƙaru da shekaru 10.

EPIC ta ce tun 2013, kusan kashi 44 cikin 100 na karuwar al'umma a duniya na zuwa ne daga Indiya - kasa ta biyu mafiya yawan al'umma a duniya.

Rahoton ya ce sama da kashi 63 cikin 100 na Indiyawa na rayuwa a yankunan da ba sa iya takaita iska mai gurtaba. Amma a 2019, an samu 'yan kasar da ke kokari wajen inganta iskarsu.

"Zai kasance abin gaggawa idan hallitun duniyar Mars suka zo duniyarmu ta Earth suka fesa wani abu da ke rage yawan shekarun mutane a duniya da shekara biyu," a cewar Michael Greenstone, ɗaya daga cikin mawallafin rahoton.

"Wannan kusan yanayi guda ne da ake ganin wanzuwarsa a wasu sassan duniya, inda ba wai feshi za a yi ba, ba wai wasu su yi kutse ba a duniyarmu," a cewarsa.

EPIC na cewa iska mai gurbata muhalli "na barazana sosai ga rayuwar mutane" a Indiya idan aka zo kan batun tsawon rai tun 1998.

Wannan musamman ya ƙaru da kashi 61.4 cikin 100. Wannan ya sha bamban da batun shan taba sigari da ke rage tsawon rai da kusan shekara biyu da rabi.

Ƙaruwar da ake samu na iska mai gurbata muhalli cikin shekaru 20 da suka gabata a Indiya na da alaka da masana'antu, ci gaban tattalin arziki da abubuwan da ake harbawa sararin samaniya na amfani da fetur tsagwaranta.

Yawan motoci akan tittuna sun rubanya sau hudu, a cewar rahoto.

Ya kuma shaida irin kokarin da gwamnati ke yi wajen dakile sinadarai masu gurbata muhalli.

Shirin tsafttace muhalli na NCAP na hankoron ganin an rage gurbata muhalli da kashi 20 zuwa 30 cikin 100.

"Idan Indiya za ta jajirce wajen rage fitar da wannan iska, hakan zai taimaka sosai wajen inganta lafiyar al'ummarta," a cewar rahoton.

Yana mai cewa samun raguwa da kashi 25 cikin 100 zai inganata tsawon rayuwa da shekara daya da wata hudu, zuwa shekara biyu da rabi ga mazauna birnin Delhi.

Presentational white space