Yadda mata ke tururuwar karba wa 'ya'yansu madarar tamowa a Katsina

Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Cutar tamowa cuta ce da masana ke alakantawa da rashin samun isasshe da kuma ingataccen abinci ga kananan yara.

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya ce kusan yara miliyan biyu ne ke ke fama da tamowa a Najeriya kuma biyu cikin goma ne kawai ke samun magani.

Kungiyar samar da abinci ta IPC ta yi hasashen cewa za a samu karuwar yara da ke fama da cutar a Najeriya.

IPC ta ce mafi yawan lokuta cutar tafi kama yara 'yan kasa da shekara biyar.

A sibitin na garin Daddara ya kasance matattara ta yaran masu fama da cutar kuma iyayensu na ziyartar asibitin ko wace rana domin nemawa 'ya'yansu madarar tamowa wacce ke ta da komadar yaran.

Shugaban asibitin Ibrahim Abubakar ya ce suna bai wa yara 500 zuwa 600 maganin tamowa a kowane mako. Ibrahim ya ce kungiyar likitoci da ke ba da agaji ta Doctors Without Borders ne ke samar da maganin tamowan.

Ya kara da cewa matsalar da suke fuskanta itace ta rashin tsaro domin kuwa a wasu lokuta 'yan bindiga na kwace madarar da akayi domin yara marasa lafiya.

Sannan wasu matan ma na sayar da madarar maimakon bai wa 'ya'yansu.