Jihohi mafi yawan daliget da wadanda suke da karancin su a Jam'iyyar APC

Asalin hoton, Twitter/@APCSpecialCon
A ranar Talatar nan ne daliget-daliget na Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ke kada kuri'unsu domin fitar da gwani a tsakanin masu neman takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar.
Ana sa ran daliget 2322 daga Jihohi 36 na fadin kasar da Abuja za su zabi wanda zai yi wa jam'iyyar takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023.
Tuni dai daliget-daliget din suka isa Abuja, babban birnin tarayyar kasar inda ake tantance su domin soma kada kuri'a da misalin karfe shida na yammacin Talata, kamar yadda jam'iyyar ta sanar.
Jam'iyyar ta APC ta sake fadawa cikin rudani kwana guda kafin a gudanar da babban taronta tun bayan da shugaban jam'iyyar Sanata Abdullahi Adamu ya bayyana cewa sun zabi shugaban majalisar dattawan kasar Sanata Ahmad Lawan a matsayin takarar sulhu na jam'iyyar gabanin zaben fitar da gwanin.
A cewarsa, sun dauki matakin ne bayan sun gana da shugaban kasar Muhammadu Buhari.
Sai dai shugaban kasar ya fitar da sanarwar da ya nesanta kansa daga kalaman shugaban jam'iyyar ta APC.
A sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasar, Malam Garba Shehu ya aike wa manema labarai, ya ambato Shugaba Buhari yana cewa babu wanda ya zaba a matsayin dan takarar APC na shugaban kasa a zaben 2023.

Asalin hoton, OTHER
"Shugaba Muhammadu Buhari, ranar Litinin da rana, ya warware zare da abawa game da matsayarsa kan zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, inda ya bayyana a gaban gwamnoni 14 na jihohin arewacin Najeriya na jam'iyyar kan cewa ba shi da dan takarar da ya zaba, da kuma shafaffe da mai kuma a shirye yake ya tabbatar ba a yi dauki-dora a jam'iyyar ba," in ji sanarwar.
Kazalika Sakataren tsare-tsare na jam'iyyar, Suleiman M. Argungu, ya yi fatali da matsayar ta Sanata Adamu inda ya ce shi kadai ne ya yi gaban kansa.
Haka kuma gwamnonin arewacin kasar karkashin Jam'iyyar APC sun nesanta kansu da matsayin shugaban Jam'iyyar APC inda suka jaddada cewa ya kamata mulki ya koma kudancin kasar bayan ya kwashe shekaru takwas a arewa.
Kano tumbin giwa
Kididdiga ta nuna cewa Arewa maso yammacin kasar ne ya fi yawan daliget inda yake da daliget 558. Kazalika Jihar Kano ce ta fi yawan daliget inda take da mutum 132. Abuja ce ke da mafi karancin daliget inda take da mutum 18.
Ga jerin jihohi Najeriya dangane da shiyya da kuma yawan daliget ɗinsu:

Arewa maso yamma: 558
Kano - 132
Katsina - 102
Jigawa - 81
Kaduna - 69
Sokoto - 69
Kebbi - 63
Zamfara - 42.
Yankin kudu maso yamma shi ne na biyu da ya fi yawan daliget kamar haka: 411
Oyo - 99
Osun - 90
Ogun - 60
Legas - 60
Ondo - 54
Ekiti - 48
Kudu maso kudancin Najeriya shi ne na uku a yawan daliget kamar haka : 372
Akwa Ibom - 93
Delta - 75
Rivers - 69
Edo - 57
Cross River - 54
Bayelsa - 24
Arewa ta tsakiya ne na hudu inda yake da daliget: 360
Neja - 75
Benue - 66
Kogi - 63
Filato - 51
Kwara - 48
Nasarawa - 39
Abuja - 18
Arewa maso gabas ce ta biyar da ke da daliget: 336
Borno - 81
Adamawa - 63
Bauchi - 60
Yobe - 51
Taraba - 48
Gombe - 33
Sai kuma yankin kudu maso gabas da ke da daliget: 285
Imo - 81
Anambra - 63
Abia - 51
Enugu - 51
Ebonyi - 39










