Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mene ne abu na gaba da zai faru da Boris Johnson?
Fira Ministan Birtaniya Boris Johnson ya lashe ƙuri'ar yankan ƙauna ta shugabancin jam'iyyar Conservative inda ya samu ƙuri'a 148 cikin 211.
Batun kaɗa ƙuri'ar ya kunno kai ne bayan da akalla ƴan jam'iyyar 54 suka rubuta wasiƙu suna cewa sun daina goyon bayan Mr Johnson.
Menene sakamakon ƙuri'ar da aka kaɗa?
Dukkan 'yan majalisar dokokin 359 sun kaɗa ƙuri'ansu.
Mr Jonson ya samu ƙuri'u 211, yayin da ya rasa 148 da suka juya masa baya.
Sakamakon ya nuna kenan kashi 59 cikin 100 na 'yan majalisarsa na goyon bayansa, kuma wannan sakamakon bai kai wanda Theresa May ta samu ba a lokacin da aka ƙada mata tata ƙuri'ar, saboda ita ta samu goyon bayan kashi 63 cikin 100 a 2018, to amma duk da haka ta yi murabus daga mukamin bayan watanni shida da kaɗa ƙuri'ar.
A yayin da aka kaɗa ƙuri'ar cikin sirri, 'yan majalisar ba za su iya cewa ga yadda suka kaɗa ƙuri'ar ba.
Daga cikin 'yan majalisar da suka kaɗa ƙuri'ar har da wadanda aka ce su ja baya daga majalisar bayan an zarge su da aikata fyaɗe da sauran laifukan cin zarafi ta hanyar lalata.
To me zai faru yanzu bayan Mr Johnson ya yi nasara?
Kasancewar ya samu nasara, yanzu Mr Johnson zai ci gaba da zama shugaban jam'iyyar Conservative kuma firaminista.
A karkashin tsarin mulkin yanzu, ba za a bar 'yan majalisar su ƙara kaɗa wata ƙuri'ar yankan ƙaunar ba a wannan shekarar.
To amma akwai raɗe-raɗe da ake cewa wasu daga cikinsu za su iya sauya tsarin saboda su samu damar kaɗa wata ƙuri'ar a nan kusa.
Ko da aka tambayeshi a kan batun, Sir Graham Brady, wanda ya yi nazari kan yadda abubuwa suka gudana, ya ce ba mamaki hakan zai iya yiwuwa.
Duk da kasancewa ya samu nasara a kuri'ar, har yanzu Mr Johnson zai ci gaba da fuskantar kalubale.
A ranar 23 ga watan Yuni ne za a gudanar da zaben cike gurbi na 'yan majalisar a Wakefield da Tiverton da kuma Honiton.
Dukkanin kujerun a baya 'yan majalisar Conservative din suka riƙe shi, don haka idan har a wannan karon sun rasa kujeru a wadannan mazabu to ko shakka ba bu Mr Johnson zai iske fuskantar sabon matsin lamba.
Mecece kuri'ar yankan ƙauna kuma me yasaake yinta?
Duk wani yunkuri na 'yan majalisar dokoki na tsige jagoransu shi ake cewa ƙuri'ar yankan ƙauna.
Fira ministan na kara fuskantar matsin lamba tun bayan bayanan da aka wallafa a kan liyafar da aka yi a fadar Downing street abin da ya saba da dokokin kullen korona.
Wani rahoto daga wani babban ma'aikacin gwamnati ya ce ire-iren waɗannan tarukan sun saɓawa doka.
Wannan rahoton ne ya janyo wasu 'yan majalisar suka fara kiran Mr Johnson da ya sauka.
Wasu daga cikin jagororin majalisar da suka fuskanci ƙalubale
- Theresa May: Ta samu nasara a ƙuri'ar yankar kaunar da aka kaɗa mata a kan batun manufar ɓallewar Birtaniya daga Tarayyar Turai a watan Disambar 2018. Duk da samun nasarar, ta yi murabus a matsayin firaminista bayan wata shida.
- Iain Duncan Smith: Bayan shafe watanni ana ta yaɗa jita-jita a kansa, shugaban majalisar ya yi rashin nasara a ƙuri'ar yankan ƙaunar da aka kaɗa a kansa a watan Oktoban 2003.
- John Major: Ya jawo an gudanar da zabe a 1995 bayan ya yi murabus a matsayin shugaban jam'iyya ba a matsayin firaminista ba, abin da ya janyo rashin fahimta a cikin jam'iyyar a kan batun yankin Turai. Mr Major ya yi nasara a kan Redwood, to amma shi ma ya fadi a zaɓen 1997.
- Margaret Thatcher: Ta yi murabus a matsayin firaminista a 1990 bayan ta gaza samun nasara a matsayin shugabar jam'iyya. Ta samu nasara a kan Micheal Heseltine da ƙuri'u 204.
To me zai faru da Mr Johnson ya fadi?
Da a ce Mr Johnson ya faɗi, da an buƙaci ya yi murabus.
Abin da zai janyo a yi zaɓe a jam'iyyar Conservative da ya fadi don sake zabar sabon fira minista.
Ya ake zabar shugaban jam'iyya?
Idan kana son tsayawa shugabancin jam'iyyar Conservative, dole sai ka samu goyon bayan wasu 'yan majalisa takwas daga jam'iyyar.
Idan kuwa aka samu 'yan takara fiye da biyu, to 'yan majalisar sai sun rinka gudanar da zabe har sai sun rage saura 'yan takara biyu.
Daga nan sai 'yan majalisa su zabi wanda zai yi nasara.