Hotunan Sarauniyar Ingila Elizabeth da ba a saba gani ba
Sarauniyar Ingila Elizabeth II tana cikin mutanen da aka fi ɗauka a hoto a faɗin duniya, amma kuma da wuya ku ga an ɗauke ta ba tare da ta shirya ba.
Albarkacin bikin cikarta shekara 70 a kan karagar mulki, ga wani kundin hotunanta da ba a saba gani ba tana gudanar da wasu ayyuka a tsawon shekaru.

Asalin hoton, Getty Images

Mai Alfarmar na cikin mutanen da suka fi yin tafiye-tafiye a faɗin duniya. Ta ziyarci ƙasashe aƙalla 117, wanda ya kai nisan jumillar kilomita miliyan 1.6. Wani abin ɗaure kai shi ne ita ce mutum ɗaya tilo da a Birtaniya da ba a buƙatar sai ta yi fasfo.

Asalin hoton, PA Media

Asalin hoton, Getty Images


Asalin hoton, Getty Images

Basarakiyar da ta fi kowa daɗewa a kan karagar mulkin Birtaniya na da 'ya'ya huɗu, da jikoki takwas da kuma tattaɓa-kunne 12.

Asalin hoton, Getty Images
Yariman Wales ne babban ɗan Sarauniya kuma wanda zai gaje ta.

Asalin hoton, Getty Images
A tsawon shekarun da ya shafe a bakin aiki, Yariman Edinburgh ya halarci dubban bukukuwa tare da Yarima Charles. Akasari sukan yi mu'amala cikin natsuwa zaune kusa da juna.
Amma wasu lokutan, wasu baƙi kan kawo cikas game da yadda lamurra ke tafiya.

Asalin hoton, PA Media

Ƙaunar doki da Sarauniya ke yi abu ne da aka sani a tsawon shekarun mulkinta. Amma ba shi kaɗai ne ke saka ta murmushi ba.

Asalin hoton, Getty Images

Dukkan hotunan na da haƙƙin mallaka











