Bayanai kan ƴan takarar gwamnan jihar Ekiti na 2022

Asalin hoton, Others
A ranar Asabar 18 ga watan Yuni ne za a yi zaɓen gwamnan jihar Ekiti na 2022.
Duk wanda ya yi nasara a zaɓen zai maye gurbin gwamna mai barin gado Kayode Fayemi na jam'iyyar APC, wanda a cikin shekarar nan wa'adin mulkinsa zai ƙare.
Tun a watan Janairu ne jam'iyyu suka gudanar da zaɓukan fitar da gwanayensu, kuma sunayen waɗanda hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasar INEC ta tantance ne kawai za su kasance a kan ƙuri'ar zaɓen.
Ga dai bayanan wasu ƴan takarar da INEC ɗin ta tantance. An zaɓe su ne bisa waɗanda BBC ta iya samun su ko bayanansu a intanet, ba don wani ya fi wani ba.







