Yahya Jammeh: Yadda aka kwace katafaren gidan tsohon shugaban Gambia na Amurka

    • Marubuci, Daga Damian Zane
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

Wasu sauye-sauye da aka samu sun taimaka wajen bankado yadda tsohon shugaban kasar Gambia ya halatta kudaden haram, tare da amfani da su wajen sayen kadarorin alfama a Amurka.

A yanzu kotu ta yanke hukuncin a kwace wani tamfatsetsen gidan alfarmar da ya saya da ya kai dala miliyan uku a Jihar Maryland da ke kusa da Washington DC.

Za a yi amfani da kudaden da za a samu idan aka sayar da gidan wajen taimaka wa wadanda tsohon shugaban ya musgunawa, karkashin mulkin "cin zarafin dan adam da cin hanci da rashawa da amfani da karfin iko fiye da kima", kamar yadda hukumomin Amurka suka bayyana.

Wani bincike da ma'aikatar shari'a ta yi ya gano cewa Jammeh ya yi amfani da kudin da ya samu ta hanyar almundahana wajen sayen gidan mai dakuna shida.

"Yankin Maryland ba wurin boye dukiyar haram da rashawa ba ne ga shugabannin da suka sace dukiyar kasashensu," kamar yadda daya daga cikin eja Selwyn Smith, da ke cikin masu tafiyar da batun ya bayyana.

Mulkin shekara 22 na Jammeh, wanda ya kare a shekarar 2017, na cike da cin hanci da rashawa, yana kuma fuskantar zarge-zargen cin zarafin dan adam, ciki har da kashewa da daure 'yan adawa a gidan kaso, da masu sukarsa.

Tun daga wancan lokacin, kwamitin da aka kafa na binciken gaskiyar abin da ya faru wato Gambia Trust, Reconciliation and Reparations Commission, ke kara samun sabbin bayanai, a wannan makon kwamitin ya bukaci a tuhumi tsohon shugaban da aikata munanan laifuka. Ya dai musanta aikata ba daidai ba.

A lokacin mulkinsa, masu fafutuka na Gambia da ke wasu kasashe na ganin hakkinsu ne su dinga wakiltar mutane da muryarsu.

A shekarar 2010, wata jaridar Gambia mai mazauni a Amurka, ta taba wallafa rahoto kan Zenab matar Mr Jammeh, tana mai zarginta da sayen wani gidan alfarma a yankin masu ido da kwalliya na Potomac, kamar yadda Ms Sallah ta shaida wa BBC.

Sai dai ba a san ainahin inda gidan yake ba.

"Mun yi bincike muka gano dukkan bayanan da muke bukata tare da gano inda gidan yake," kamar yadda mai shekara 49 ya bayyana, yana magana ne a kan mambobin kungiyar masu rajin kare hakkin dan adam a Gambia (Duga).

Sunan wanda ya saya da aka rubuta MYJ Family Trust - ya yi banbarakwai. "Mun yi tunanin: 'Wani ne ke kokarin boye batun sayen gidan da suka yi.'"

Haruffan, Y da J sun kasance haruffan farko na sunan shugaban.

Ba da jimawa ba, Ms Sallah ta fara yin zuruftu unguwar Bentcross Drive da nufin ko za ta dace da ganin wani.

"Mukan yi shawagi a mota kusa da gidan, wata rana kawai sai muka ga matarshi na shiga da mota cikin farfajiyar, sai muka yi tsalle tare da cewa: 'Yeeeeeee, wannan ne gidan,'" ta fada cike da dariya, a tattaunawar da muka yi da ita a gidanta da ke kusa da Bethesda.

Bayan nan mambobin Duga, da suke zargin an sace dukiyar Gambia ne aka sayi gidan, sai suka fara gudanar da zanga-zanga akai-akai a kofar shiga gidan.

Sun kafa tutar Gambia a jikin karfen babbar kofar shiga gidan, tare da rubuta kalmomin ''Yan Gambia sun sanya gidan nan a kasuwa."

Sun takurawa makwabta yadda har suka sanar da su zargin da ake zargin Jammeh da aikata a can gida Gambia.

Abin mamaki, ashe daya daga cikin gidajen unguwar mallakin tsohon shugaban kasar Equatorial Guinea ne da ya yi gwamman shekaru kan mulki wato Teodoro Obiang Nguema, wanda jaridar Washingtom Post ta bada rahoto aka yi a shekarar 2017, kan zargin take hakkin dan adam da cin hanci da rashawa ko da yake ya musanta.

Babu tabbacin ko mazauna unguwar attajiran, ba sa son hayani ko damunsu, tun da babu wanda ya taba korafi.

Amma mutanen da ke zaune a cikin gidan Jammeh sun damu, wasu lokutan ma sukan kira 'yan sanda, in ji Mis Sallah.

Batun kwace gidan ya faru ne, jim kadan bayan an tilasta wa Mr Jammeh sauka daga mukami tare da yin gudun hijira zuwa Equatorial Guinea, bayan shan kaye da ya yi a zaben shugaban kasa a watan Disambar 2016.

Sabuwar gwamnatin Gambia ce ta kafa kwamitin binciken almundahanar da aka aikata tsawon lokacin mulkin Jammeh.

Rahoton farko na shekarar 2019, ya bayyana irin kazamar satar dukiyar kasa da aka.

An samu kanananbindigogi samfurin pistol da aka kera da danyen gwal, na daga cikin abubuwan da aka gano a gidan Mista Jammeh na Gambia, sai dai abin da ya fi jan hankalin mutane, shi ne tarin takardun kadarorinsa.

Kwamitin ya gano, tsohon shugaban ya mallaki kadarori 281 a Gambia 98da suka hada da gidaje da filaye da wadandasu a kasashen Amurka da Morocco, da asusun ajiyar banki sama da 100.

Babu ta yadda za a yi Jammeh ya sayi tarin kadarorin da albashinsa na shugaban kasa, an kuma karkare da farashinsu ya kai sama dala miliyan 300.

Kwamitin ya kuma gano sama da dala miliyan daya da aka karkatar zuwa asusun ajiyar bankin Zenab Jammeh. Yawancin kudaden an fitar da su ne da nufin ayyukan jinkai ga kungiyoyi, ciki har da kungiyar yara ta Save the Children.

"Kusan dukkan kudaden da ya kamata a bai wa kungiyoyin agaji, an yi amfani da su wajen shirya dabdalar da ta karawa Nenab Jammeh farin jini da suna, maimakon taimakawa kananan yara," in ji shugaban da ke jagoranbar kwamitin tuhume-tuhumen da ake yi wa Jammeh.

An kuma gano Mr Jammeh ya kwashe wasu kudade da bada toshiyar baki kan samun damar fitar da wasu kayayyaki da Gambia ke samarwa zuwa kasashen waje, kamar auduga da man fetur. Rahotanni sun bayyana cewa ya yi amfani da karfin iko wajen samun lasisin da ya bashi karfi fiye da kima.

Daga wannan kudaden ne aka samu na sayen gidan alfarmar na birnin Washington DS.

A watan Yulin 2010, an shaida wa kamfanin man fetur na Gambia a shekara mai zuwa za a kwace lasisin izinin fitar da shi.

Ba da bata lokaci ba, mai kamnfanin ya tunkari shugaba Jammeh, shi kuma ya bashi tabbacin bashi damar ci gaba da aiki har zuwa shekarar 2014.

Kwanaki 11 bayan haka, dala miliyan daya ta fita daga asusun kamfanin da ke Gambian Bank Trust Bank Ltd, a dai wannan ranar shugaban kasar ya sabuntawa kamfanin lasisi.

Daga karshe an yi amfani da kudin, wajen sayen kadarori a Amurka aka kuma tura kudin asusun da ke kasar.

Jaridar Washington Post ta bayyana cewa gidan yana wata unguwa da sai manyan masu hannu da shuni ne ke iya zama a ciki, da akai wa lakabi da dan karamin garin attajirai.

Baya ga tantsama-tantsaman dakuna shida da bandakuna bakwai, gidan yana da katuwar kofa da farfajiya, da sashen maotsa jiki cike da injinan zamani daban-daban, akwai karamar silima a gida, da kwamin wanka, gidan saukar baki da lambu mai ban sha'awa.

Babu tabbacin ko Mr Jammeh na yawan zama a gidan, amma matarshi na yawan ziyara, kamar yadda Mis Sallah ta shaida mana.

Sallah, ta sha ganin Zenab Jammeh a manyan kantinan alfarma da ta ke sayayya. Amma wannan tsohon zance ne, a yanzu da alkalai ke shari'a a akai, gidan ya zama na 'yan Gambia.

"Duk da cewa tsohon shugaban Gambia Yahya Jammeh tare da matarshi sun boye wasu kudaden 'yan kasarsu tare da siyan gidan na," in ji Attorney Robert K Hur, ya ce lokacin da aka kwace kadararorin a shekarar 2020 sun tashi daga hannus.

Kwamitin ya ce kadarorin saida su za a yi, sun kuma bada shawarar ayi amfani da kudin domin yi wa 'yan Gambia ayyukan ababen more rayuwa, domin su amfana da dukiyar kasarsu da Jammeh ya handame, da azabtar da su, da cin zarafi a lokacin ya na kan mulki.

A yanzu dai, za a zuba ido a ga abin da masu fafutuka 'yan Gambia mazauna kasashen waje za su yi, domin tabbatar da cewa 'yan kasar sun amfana daga dukiyarsu da aka wawashe.