Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tsohon shugaban Gambia Jammeh 'ya yi wa sarauniyar kyau fyade'
- Marubuci, Daga Louise Dewast
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Afirka
Wata matashiya mai shekara 23 kuma tsohuwar sarauniyar kyau ta kasar Gambiya, Fatou "Toufah" Jallow, ta ce tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh ya yi mata fyade a lokacin da yake shugabanci.
Bayanan nata na kunshe ne cikin wani rahoto na hukumar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch da hadin gwiwar Trial International suka fitar inda aka yi bayanin zargin wani fyaden da Mista Jammeh ya yi.
BBC ta yi kokarin tuntubar Mista Jammeh, wanda a yanzu yake gudun hijira a kasar Equatorial Guinea, don jin ta bakinsa kan zarge-zargen.
Wani mai magana da yawun jam'iyyarsa ta APRC ya yi watsi da zarge-zargen da ake yi wa Mista Jammeh.
"A matsayinmu na jam'iyya kuma al'ummar Gambiya mun gaji da irin wadannan zarge-zarge da ake yi wa tsohon shugabanmu," kamar yadda Ousman Rambo Jatta, ya fada a sakon da ya aike wa BBC.
"Tsohon shugaban ba shi da lokacin da zai mayar da martani kan wadannan karerayi. Shi mai mutunci ne kuma mai tsoron Allah wanda yake girmama matan Gambiya," a cewar mataimakin shugaban jam'iyyar ta APRC.
Ms Jallow ta shaida wa BBC cewa tana son haduwa da Mista Jammeh, mai shekara 54, a kotu don ya fuskanci hukunci.
"Na yi matukar kokarin boye wannan labarin na kuma goge shi don ya kasance ba ya cikin tarihina.
"Amma a zahirin gaskiya na kasa yin hakan don haka na yanke shawarar yin magana a yanzu saboda lokaci ya yi da zan bayyana labarin na kuma tabbatar da cewa Yayha Jammeh ya ji abin da ya aikata."
Ta ce tana kuma so ta bayar da shaida a gaban Kwamitin Fadar Gaskiya da Sasantawa na Gambiya, (TRRC), wanda Shugaba Adama Barrow ya kafa, bayan ya lashe zabe a watan Disambar 2016.
Kwamitin yana bincike ne kan keta hakkokin bil'adam da ake zargin an yi a lokacin mulkin Mista Jammeh na shekara 22, da suka hada da rahotannin kashe-kashe ba bisa ka'ida ba, da azabtarwa da kuma kama mutane da tsare su ba da dalili ba.
An tumbuke shi daga mulki ne a watan Janairun 2017 bayan da shugabannin yankin Afirka Ta Yamma suka tura dakaru lokacin da ya ki ya mika mulki.
'Kin aure'
Ms Jallow ta ce shekararta 18 a lokacin da ta hadu da Mista Jammeh bayan da ta yi nasara a gasar sarauniyar kyau ta 2014 a babban birnin kasar, Banjul.
A watannin da suka biyo bayan nasararta, ta ce tsohon shugaban kasar ya nuna shi matsayin uba yake gare ta a lokacin da suka hadu, ya nemi ya dinga ba ta shawara da yi mata kyauta da ba ta kudi, ya kuma sa aka ja ruwan famfo a gidan iyayenta.
Ta kuma ce ya shaida mata cewa yana son aurenta a wata liyafar cin abinci da wani mai taimakawa shugaban ya shirya. Sai ta ki amincewa tare da mayar wa da mataimakin nasa kyautukan alatun da aka yi mata don ta yarda da tayin.
Yahya Jammeh a takaice
- Ya kwace mulki a wani juyin mulki da ya yi a shaekarar 1994 yana dan shekara 29
- A shekarar 2013, ya sha alwashin ci gaba da mulki tsawon biliyoyin shekaru idan Allah ya so
- Ya kuma bayar da umarnin kashe masu laifi da 'yan adawar siyaysa
- A shekarar 2007 ya yi ikirarin zai iya warkar da cutar Aids da ba da maganin haihuwa ta hanyar hada magnungunan gargajiya
- A shekarar 2008 ya ce za a dinga fille kawunan masu luwadi
- Ya musanta cewa jami'an tsaronsa sun kashe dan jarida Deyda Hydara a shekarar 2004
- Shugabannin kasashen yankin Afirka Ta Yamma sun tursasa shi barin mulki a watan Janairun bayan da ya fadi zabe a 2016
- Yana yin gudun hijira a kasar Equatorial Guinea
Mis Jallow ta ce daga nan sai mai taimaka wa shugaban ya nace sai ta halarci wani taron addini a fadar gwamnati a matsayinta na sarauniyar kyau a watan Yunin 2015. Amma a lokacin da ta isa, sai aka kai ta wani gidan shugaban na sirri.
"A bayyane yake karara kan abin da zai kasance," in ji ta, tana mai bayyana fushin Mista Jammeh na yin watsi da shi.
Ms Jallow ta ce ya mare ta ya kuma yi mata allura a damtsen hannunta.
"Ya goga gabansa a fuskta, ya kayar da ni kan gwiwowina, ya cire min rigata sannan ya sadu da ni ta baya."
''Yan matan da ke kai kawo a fadar shugaban kasa'
Matsahiyar dai ta ce bayan hakan sai ta rufe kanta a gida tsawon kwana uku daga bisani lkuma ta yanke shawarar guduwa makwabciyar kasar Senegal.
A yayin da ta isa Dakar, babban birnin kasar Senegal, Ms Jallow ta nemi taimakon kungiyoyin kare hakkin dan adam da dama. Makonni bayan nan, sai aka ba amince da ba ta kariya tare da mayar da ita Kanada, inda take zaune a can tun lokacin.
Hukumomin kare hakki na Human Rights Watch da Trial International sun ce Mista Jammeh yana da hanya ta musamman da yake cin zarafin mata, inda wasu daga cikinsu suke da tsarin albashi na musamman.
Sannan kuma suna aiki ne a matsayin "'yan matan fadar gwamnati". An zayyana ayyukan da wasu dag ciukinsu za su riuka yi amma babban aikinsu shi ne yin jima'i da shugaban kasa.
BBC ba ta iya tabbatar da wannan zzargi ba, amma wani tsohon jami'in gwamnatin kasar wanda ya ce kar a aambaci sunansa, ya ce yana da masaniyar "abubuwa marasa dadi" da ke faruwa a fadar ta shugaban kasa:
"Ma'aikatan fadar shugaban kasa akasarinsu mata ne kuma an dauke su domin su biya wa shugaban kasa bukata."
Ya ce yana iya tuna sanda ya ga Mis Jallow a gidan gwamnati "da tsakar dare".
Wata matar da aka dauke ta aiki a fadar gwamnati tana shekara 23, ta fada wa HRW cewa an tilasta mata ta yi jima'i da Mista Jammeh a 2015.
Matar wadda ta nemi da a boye sunanta, ta ce wata rana shugaban kasa ya kira ta dakinsa:
"Ya fara tube min kayana yana cewa wai yana kauna ta, kuma zai taimaka min da 'yan uwana, amma idan na sake na fada wa wani zan gaya wa jikina.
"Ba ni da wani zabi a lokacin. Ya yi jima'i da ni ba tare da wata kariya ba."
'Wasu na kaunar aikin'
Wata matar da ta yi aiki a fadar shugaban kasar ta ce sun yi amannar cewa duk wadda shugaban ya kira to kawai kjwanciya zai yi da ita.
"Wasu daga cikinmu son abin suke yi. Suna jin cewa kamar wani matsayi ne ko kuma suna son kudi," kamar yadda ta fada wa HRW.
Ta bayyana yadda shugaban kasar ya ci zarafinta a wani gidan shakatawarsa a kaunyensu na Kanilai a 2013 lokacin tana da shekara 22:
"Wata rana da yamma wata mataimakiyarsa ta musamman ta kjira niu zuwa dakinsa. Ya ce min na tube kayana.
"Ya ce min ni yarinya ce saboda haka ina bukatar kariya, domin haka zai zuba min ruwa mai tsarki."
Da su sake haduwa washe gari, bayan ya fara taba jikinta sai ta fara kuka, inda shi kuma ransa ya baci har ma ya kore ta.
Ta ce daga baya an kore ta daga aiki sannan kuma aka hana ta tallafin karatu da aka yi mata alkawari.
Babban sakataren TRRC Baba Jallow ya shaida wa BBC cewa binciken da hukumarsa ta kaddamar wata takwas da suka wuce zai mayar da hankali ne kan cin zarafin da ya faru a watan Satumba.
"Muna sane da zarge-zargen cin zarafi da ake yi wa Yahya Jammeh, amma har yanzu ba mu saurari wadanda abin ya shafa ba a hukumance.
"Tuni mun fara bincike amma ba mu kai ga matakin sanin wadanda abin ya shafa ba da kuma yawansu," in ji sakataren.
Aikin kwamnitin TRRC:
- Zai bincika zargin cin zarafin da Mista Jammeh ya aikata lokacin mulkinsa na shekara 22 - an yi zargin tsare mutane, an kori mutane, an kuma azabtar da abokan adawa.
- Masu bincike guda 11 za su bai wa wadanda abin ya shafa diyya
- Majalisar Dinkin Duniya da kuma masu taimako na kasashen waje ne suke tallafawa binciken, wanda aka fara a Nuwamban 2018
- Takensu shi ne "Ba za a kuma ba"
Mis Jallow tana so ne ta kirkiri wata hanyar bai wa mata damar tattauna cin zarafinsu da aka yi ba tare da tsangwama ba.
"Abu ne da za a bi shi mataki-mataki, kuma matakin farko shi ne a yarda da faruwarsa.
"Idan aka samu mata da yawa suna bayyana halin da suke ciki tsangwamar za ta ragu," kamar yadda ta shaida wa BBC.
Shugaban kasar The Gambia na yanzu Adama Barrow ya ce zai jira sakamakon binciken TRRC kafin ya yanke shawarar ko zai nemi Equatorial Guinea ta taso keyar jammeh zuwa gida domin a tuhume shi.