Zartar da hukuncin kisa ya ƙaru sosai a Iran da Saudiyya a 2021 - Amnesty

Asalin hoton, SOPA Images
- Marubuci, Daga David Gritten
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Ana nuna damuwa kan ƙaruwar aiwatar da hukuncin kisa a shekarar 2021 a yayin da aka sassauta dokokin annobar cutar korona, a cewar Amnesty International, tana mai cewa an samu ƙaruwar hakan a Iran da Saudiyya.
Wani rahoto da ƙungiyar kare hakkin ɗan adam ɗin ta fitar ta ce a ƙalla an kashe mutum 579 a ƙasashe 18 - lamarin da ya sa hakan ya ƙaru da kashi 20 cikin 100 idan aka kwatanta da na shekarar 2020.
Iran ce kan gaba a wannan lamarin. Ta yanke wa a ƙalla mutum 314 hukuncin kisa, idan aka kwatanta da 246 ɗin da aka yi a shekarar 2020.
Yawan waɗanda Saudiyya ta yanke wa hukuncin kisa ya nunku zuwa 65.
Sai dai jumullar yawan kisan a fadin duniya ya ragu a karo na biyu, bayan shekerar 2020.
Sai dai, a shekarun baya ba a haɗa da adadin China ba. Duk da cewa an yi amannar duk shekara ƙasar na aiwatar da hukuncin kisa ga dubban mutane, ba a samun bayanan hakan don wani sirri ne da ƙasar ke ɓoyewa.
Amnesty ta ce irin wannan sirri ne ya sa yake da wahala a samu rahotannin alƙaluma daga Koriya ta Arewa da Vietnam, inda ake tunanin an aiwatar da hukuncin kisa kan mutane da dama a can.

Rahoton Amnesty na shekara-shekara ya ce ana samun ƙaruwar aiwatar da hukuncin kisa a Iran tun 2017, wato shekara biyar a jere, sakamakon yanke hukuncin kisan ga laifuka masu alaƙa da shan miyagun ƙwayoyi, inda a bana aka samu 132 daga 23 na shakarar 2020.
Ƙungiyar ta kuma kira hakan da "take dokokin ƙasa da ƙasa ne ƙarara, waɗanda suka haramta yin amfani da hukuncin kisa ga duk wani laifi idan dai ba na laifin kisan kai ba ne".
A cewar Amnesty, ƙaruwar aiwatar da hukuncin kisan da kashi 140 a bara a Saudiyya, "wani lamari ne marar daɗi da ya ci gaba da faruwa har a 2022, inda a watan Maris kaɗai aka aiwatar da hukuncin kisa kan mutum 81 a rana guda."
An samu ƙaruwar aiwatar da kisan a Somaliya daga 11 a 2021 zuwa 22 a bana, da Sudan ta Kudu daga biyu zuwa tara da kuma Yemen daga biyar zuwa 14.
Rahoton ya ƙara da cewa sassauta dokokin kullen korona ya sa alkalai sun yanke hukuncin kisa 2,052 a ƙalla a ƙasashe 56.
Amnesty ta kuma nuna damuwa kan yadda gwamnatin soji ta Myanmar take miƙa lamurran laifukan fararen hula ga kotun soji inda ake yanke musu hukunci daidai da dokokin sojin.











