Sri Lanka: Bambance-bambancen da suka haifar da zanga-zangar da suka hada kan 'yan kasar

Sri Lankan retired soldiers held national flags and placards protesting on April 9, 2022, at Galle Face, Colombo.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An rika yin zanga-zangar nuna bacin rai ga gwamnati a birnin Colombo cikin 'yan makwannin nan
    • Marubuci, Daga Nick Marsh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC a Colombo

"Yan kallo na nan: Musulmai na nan, mabiya Hindu na nan kuma 'yan Katolika ma na nan. Dukka jininsu guda ne."

"Wannan ita ce Sri Lanka ta ainihi."

Lukshan Wattuhewa ke nan ke nuna masu zanga-zanga a gabar tekun birnin Colombo, wurin da dubban masu zanga-zanga ke taruwa a kullum.

Yana fatan gagarumar zanga-zangar nuna bacin rai ga gwamnatin kasar - wadda mummunar matsalar tattalin arziki ta haifar - na iya samar da sabuwar alkibla ga gomman shekarun da aka shafe ana rikice-rikicen kabilanci da na addini da suka illata al'umomin kasar masu yawa.

Wani malamin addinin Bhudda ya yarda da abin da ya ke cewa: "Jama'a na ajiye bambancin addini da na kabilanci suna shiga wannan gwagawarmayar. Sri ta zama dunkulalliyar kasa."

Dukkansu 'yan kabilar Sinhala masu rinjaye cikin al'ummar kasar ne, wadanda su ne kashi uku cikin hudu na jama'ar kasar. 'Yan Tamil Hindu da Musulmi da Kiristoci na cikin al'umomin kasar marasa rinjaye.

Sai dai an shafe makonni 'yan kasar na zanga-zanga a titunan biranen Sri Lanka suna aika wannan sakon: "Koma gida Gota".

"Gota" shi ne Gotabaya Rajapaksa wanda shi ne shugaban kasar, wanda ya lashe zabe watanni kadan bayan mummunan harin bam da aka kai ranar Easter, harin da aka ce masu kishin Islama ne suka kai shi.

Amma a yanzu goyon bayan da yake da shi ya kare. matsalar tattalin arziki ya sa wadanda suka zabe shi sun koma suna kiransa ya ajiye mukamin nasa. baya ga wannan matsalar, 'yan Sri Lanka na tuhumar shugaban nasu da nuna bambancin launin fata.

Sri Lankan catholic nuns shield the protesters during a protest near the president's office at Colombo, Sri Lanka. 24 April 2022.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Zanga-zangar da ake yi a Sri lanka ta hada kan al'umomin kasar mabiya addinai mabambanta kuma masu kabilu daban-daban

Siyasar nuna cewa 'yan kabilar Sinhala ne mafi daraja ba sabuwa ba ce a Sri Lanka, inda aka rika kai wa 'yan Tamil hare-hare. Gotabaya Rajapaksa ya rike mukamin ministan tsaron kasar a 2009, lokacin da gwamnatin kasar ta kawo karshen yakin gomman shekaru da ta yi da 'yan aware na LTTE ko Tamil Tigers.

Yawancin 'yan Sinhala sun goya ma sa baya, suna kallonsa a matsayin wani jarumi a lokacin, amma wasu sun rika neman a kama shi saboda yadda gwamnatin lokacin ta fahe da kawo karshen yakin amma ta rika take hakkin dan Adam.

Masu sukarsa na cewa a madadin ya nemi sasantawa da al'ummar Tamil, Rajapaksas ya ci gaba da mayar da 'yan Tamil tamkar shanun ware.

Amma tun bayan harin bam na ranar Easter da kuma zaben da aka yi wa Rajapaksas a matsayin shugaban kasa, Musulmin kasar ma suna fuskantar cin mutunci.

Nonpartisan Demonstrators held a May Rally regarding the ongoing Economy Crisis in Colombo, Sri Lanka on May 1, 2022,

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu zanga-zangar na kira ga Shugaba Gotabaya Rajapaksas da ya sauka daga mukaminsa

Yayin da zanga-zangar ke gudana a cikin birane kamar Colombo cikin yanayi kamar na biki, ba ahaka lamarin yake ba a gabashin kasar, yankin da yawancin 'yan Tamil suka fi yawa.

Ba a cika yin zanga-zanga a wadannan yankunan ba, duk da rashin jituwa da ke tsakanin gwamnatin kasar da al'umomin yankin.

Masu fafutukar kare muradun 'yan Tamil na cewa jami'an tsaro a yanki ba za su nuna dattaku kan 'yan Tamil ba kamar yadda suke yi a babban birnin kasar Colombo.

Buddhist monks arrive for a meeting at Colombo's Independence Memorial hall in Colombo on April 30, 2022, to express their solidarity with countrymen demonstrating against the government over the country's crippling economic crisis.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Malamai mabiya addinin Bhudda ma sun nuna goyon bayansu ga jerin zanga-zangar da ake yi

A can gabar tekun birnin Colombo, wani jerin gwanon malamai mabiya addinin Bhudda na maci zuwa fadar shugaban kasar. A bayansu wasu mata mabiya addinin Katolika na bi masu, wata alama ta hadin kai tsakanin mabiya addinan kasar.

Wani mai zanga-zangar mai suna Luckshan Wattuhewa ya ce yawancin 'yan kasar na fuskantar matsaloli iri daya: magance yunwa da karancin man fetur da magani domin iyalansu.

ya ce yana fatan yaga an bude wani sabon babi a tarihin kasarsa.

"Mun shafe shekara 30 na rikici da yaki kuma mun sha wahala sosai. Mun gaji - muna bukatar zaman lafiya ne a kasar na tamu."