Gotabaya Rajapaksa: Abin da ya sa fusatattun 'yan Sri Lanka suke neman shugaban kasar ya sauka

Masu zanga zanga aColombo
Bayanan hoto, Wani mai zanga-zanga rike da tutar kasar Sri Lanka lokacin gangamin a birnin Colombo
    • Marubuci, Daga Rajini Vaidyanathan
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC South Asia Correspondent

Ministoci da gwamnan babban bankin kasar Sri Lanka duka sun sauka daga mukamansu sakamakon karuwar fusata kan hauhawar farashin kayan abinci da man fetur a kasar.

Shugaba Gotabaya Rajapaksa ya gayyaci duka jam'iyun da su kasance a cikin sabuwar gwamnatin.

Amma a yayin da matsalar tattalin arziki ta kara muni, wadanda suka fita zanga-zanga kan tituna sun ce ba za su ja da baya ba har sai Mista Rajapaksa ya yi murabus.

A fadin wani tsibiri cike da fusata da damuwa, ana danganta rera waka da rubutun da ke jikin kwalaye kan mutum guda ne.

"Ka sauka Go Gota ka sauka," "Ka sauka Gota ka sauka," suke cewa.

Gota a gajarce na nufin Gotabaya Rajapaksa, shugaban kasar mai janyi ce-ce-ku-ce, da mutane da dama ke dora wa alhakin mummunan yanayin da jama'a suka shiga.

"Ya kamata ya sauka, ya hana mu komai na jin dadi,'' in ji Nadhie Wandurgala wacce ta kauce wa dokar hana fita a fadin kasar don yin zanga-zanga a ranar Lahadi tare da mijinta da 'yayanta mata biyu.

A yayin da take rike da wani kwali mai dauke da rubutu da aka yi da hannu, ta bayyana mummunan halin da iyalanta suka shiga, daga zaman jin dadi da wadatar da suka saba a baya zuwa rashin wadata - daukewar wutar lantarki ta kusan sa'oi 17, da fafutukar neman gas din girki a kullum, da kuma dogayen laukan man fetur da motarsu.

"Su kan su asibitoci na fama da karancin magunguna, makarantu na fama da karancin takardun jarrabawa, amma 'yan siyasa na samun wutar lantarki a ko da yaushe."

"Ba su taba tsayawa a kan dogayen layuka don sayen gas ko kalanzir ba,'' ta ce, muryarta cike da raina kurar wadanda ke kan mulkin.

Nadhie ba mai fafutuka ba ce ko wata cikakkiyar mai zanga-zanga. Tana aiki a wani coci, kuma ta gwammace nisantar harkokin siyasa. Amma mai bin ra'yin masu sukar lamirin gwamnati ce da ke hada kawunan mutane daga bangarori daban-daban na addinai da shekaru.

A yayin da Sri Lanka ta fara fuskantar karancin kudaden kasar waje a asusun rarar ajiyarta, ta kasa biyan kudaden shigo da muhimman kayayyaki kamar su danyen mai.

Raguwar masu yawon bude ido saboda annobar korona daya daga cikin matsalolin, amma mutane da dama na cewa shugaban kasar ya gaza wajen shawo kan matsalolin.

Kwararru sun bayyana cewa manufofin gwamnati da Mista Rajapaksa ya bullo da su bayan da aka zabe shi a shekarar 2019 - zaftare kudin haraji da haramta shigowa da kaya - sun kara ta'azzara matsalolin, baya kin yarda da neman taimako daga Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF).

Mista Rajapaksa ya zargi gwamnatocin da suka shude kan halin da kasar ta shiga, amma da dama irin su 'yar Nadhie, Anjalee ta bayyana cewa lokaci ya yi a gare shin a ya sauka daga kan mulki ba tare da wata-wata ba, kana ya amsa daukacin laifinsa.

Nadhie Wandurgala with da iyalinta
Bayanan hoto, Nadhie Wandurgala ta kauce wa dokar hana fita a fadin kasar don yin zanga-zanga a ranar Lahadi tare da mijinta da 'yayanta mata biyu.

A yayin da damuwa ta karu, haka ma fargaba cewa gwamnatinsa na kokarin dakile ta wata suka a kanta.

Dokar hana fita ta ranar Lahadi mataki daya daga cikin matakn da aka tsara ne na hana mutane taruwa wuri guda.

Har ila yau an toshe hanyoyin shafukan sada zumunta da kuma sanarwar fadar shugaban kasa ta haramta wa mutane ''kasancewa a kan tituna, da wuraren shakatawa, da jiragen kasa da kuma bakin teku'' muddin ba a ba su takardar izini daga hukumomi ba.

Nadhie da Anjalee kadan ne daga cikin daruruwan mutane da suka tari aradu da ka wajen halartar zanga-zangar, a kan titina duk kywa da umarnin da aka bayar na kasancewa a cikin gida.

"Na fito a yau ne saboda an kwace min 'yancina. Ba mu da wata asarar da za mu y a daidai wannan lokaci.''

"Me ya sa ma suka kafa wannan dokar hana fita? Shin don su ba mu kariya ne?" Anjalee ta yi gaste. '' Babu wata ma'ana ko kadan"

Wani dan . Sri Lanka
Bayanan hoto, Da dama sun yi kira ga Mista Rajapaksa da ya sauka daga mulki

"Zan iya kiran wannan a matsayin mulkin kama-karya, da mulkin mallaka da kuma matakai masu tsauri,'' jagoran adawa Sajith Premadasa ya shaida min a lokacin zanga-zangar ranar Lahadi.

An dakatar da Mista Premadasa da sauran 'ya'yan jam'iyarsa a wani shingen binciken kwakwaf na 'yan sanda a lokacin da suke kokarin shiga cikin dandalin Independence na birnin.

"Babban dokar kasar na yin kariya ga mutanen da ke da ra'yoyi iri daya, na yin zanga-zanga kana na yin harkokin siyasa cikin lumana, don haka bai kamata a haramta wannan dama na.''

Wannan ba shi ne karon farko da ake zargin Shugaba Gotabaya Rajapaksa, wanda ke mulkar kasar tare da kanensa Firaminista Mahinda Rajapaksa da hana 'yancin fadin albarkacin baki ba.

'Yan uwan junan biyu na da tarihin da ya wuce samun galabar zabensu a shekarar 2019.

Mahinda Rajapaksa ya zama shugaban kasar har sau biyu, a yayin Gotabaya Rajapaksa sananne ne a matsayinsa na sakataren harkokin tsaro lokacin da aka zarge shi da kitsa mummunan cin zarafin biladama a lokacin matakin karshe nay akin basasar kasar Sri Lanka.

Dukanninsu biyu na da shaidar gallazawa wadanda suka bijire musu.

A shekarar 2019, watanni bayan harin bama-bamai na ranar Lahadin Easter a kasar.

Sri Lanka, Gotabaya Rajapaksa ya samu goyon baya mafi rinjaye, bayan alkawarin da ya yin a mulkar kasar ta Sri Lanka '' da karfin niyya".

"Mutane sun yi tsammani za su samar mana da ingantaccen tsaron kasa, amma bas u yi komai ba.. sun gaza a ko wane bangare,'' in ji Roshinta, wacce ta ce ba ta zabe shi ba.

"Ba na so in ga kasata a lalace saboda wadannan iyalai. Ba su damu ba, kana ga kwadayin mulkin ba watakila za su cigaba a kai.''

A ranar Alhamis, fusatar da ake nunawa kai tsaye kan Shugaba Rajapaksa ta kai har kofar gudansa, a yayin da masu zanga-zangar a wajen gidansa a birnin Colombo suka kara kaimi.

Yansanda sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla da ruwan zafi wajen tarwatsa taron, kana mahukuntan sun cafke gwamman masu zanga-zangar har ma da wasu manema lanarai da ke daukar rahoton abubuwan da ke faruwa.

'Yan sanda
Bayanan hoto, Akwai 'yan sanda da dama a wurin zanga-zangar.

A shafin Twitter, tawagar Kungiyar Tarayyar Turai EU a birnin Colombo ta yi kira ga mahukuntan kasar Sri Lanka da su '' kare 'yancin dimokaradiyya ga ko wane dan kasa, da suka hada da 'yancin taruwa wuri guda da kuma sabanin ra'ayi, wanda zai kasance cikin kwanciyar hankali."

Kungiyoyin kare hakkin biladama da suka hada da Amnesty International sun ce an gallaza wa da dama da ake tsare da su.

Jdaukar matakin cafkewa tare da tsare mutane - mahukuntan sun ce wani mataki ne na tabbatar da doka da oda.

Da tsakar dare daga ranar Asabar zuwa Lahadi, hukumomi a Lardin Yamamcin Sri Lanka sun bayyana cewa sun cafke fiye da mutane 600 kan karya dokar hana fita.

A ranar Lahadi yamma lokacin da muka ziyarci wurin zanga-zangar a Colombo, 'yansanda dauke da garkuwa daga nesa da masuz anga-zangar na kallon abubuwan da ke faruwa.

"Wannan shi ne karon farko da na taba shiga zanga-zanga a rayuwata,'' in ji Sathsara yayin da yake tsaye a gefen wurin shakatawa yana sanye da riga mai gajeren hannu.

A wata zanga-zangar da akasari iyalai ne matasa, Suchitra, rungume da dan sa mai watanni 15, ya shaida min cewa ya gaji da yawan daukewar wutar lantarki da ke hana dan sa barci.

"'Yan siyasar da ke majalisar dokoki bas u cancanta ba. Sun jefa kasar cikin rudani,'' in ji shi.

"Ba su cika alkawarinsu ba, bai kamata mutane su rika shan wahala ba, mutane ba za su cigaba da shan wahala ba."