Yadda ake tsangwamar Musulmai da muzguna musu a Sri Lanka

- Marubuci, Daga Anbarasan Ethirajan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Colombo
Bayan lura da take yi da yaronta da ya fara koyon tafiya, mafi yawan lokutan Maryam na ƙarewa ne wajen ganin ta dawo da mijinta gida.
Hejaaz Hizbullah, fitaccen lauya mai rajin kare hakkin dan adam, an ɗaure shi na tsawon watanni 20 a gidan yari, ana tuhumarsa ne ƙarƙashin dokar yaki da ta'addanci, mai gabatar da ƙara ya tuhume shi da maganganun yada kiyayya tsakanin mutane da kuma tayar da yamutsi tsakanin kabilu.
Sun yi zargin cewa Hizbullah ya rubuta wa wani matashin Musulmi wata maƙala mai cike da kalaman nuna ƙin jinin mabiya addinin Kirista.
Hizbullah wanda ya fito daga yankin Musulmai marasa rinjaye, ya shafe sama da shekara guda a gidan yari kafin a gabatr da tuhumar da ake masa a watan Afrilun 2021, kuma har zuwa wannan lokacin dai yana ɗaure a gidan yarin.
"Yana da yawan magana, yana kokari wajen kare hakkin musulmai da marasa rinjaye," ta shaida wa BBC.
Tuhume-tuhumen da ake yi wa mijinta sun hada da "tura sako ga duk wanda ke son yin magana a kan wariyar launin fata, nuna banbanci", in ji ta.
An fara kama Hizboullah ne a kan zargin harin kunar bakin waken da aka kai ranar Easter a 2019, wanda wani Musulmi dan kasar ya kai sama da mutum 260 ne suka mutu a harin.
An yi masa zargin cewa yana da alaƙa da daya daga cikin wadanda suka kai harin.
Daga baya mai gabatar da karar ya janye wadannan zarge-zargen, bayan lauyoyinsa sun gabatar da shaidar cewa ba shi da hadi da maharin, ya dai taba zuwa gaban kotu kan karar wasu filaye na mahaifin yaron, fitaccen dan kasuwa ne mahaifin.
A bara, kungiyar Amnesty ta ambaci Mista Hizbullah a matsayin mai sukar gwamnati, "fursunan da ake ɗaure da shi ba tare da haƙƙinsa ba".
Masu fafutuka sun ce kama Hizbullah wani bangare ne na matsawa marasa rinjaye da ake yi a a 'yan shekarun nan.
Rikicin labilanci na na kara zurfafa a Sri Lanka, kasar da Musulmai ba su kai kashi 10 ba cikin 100 na mutum miliyan 22 da take da su, mafi yawan mutanen mabiya addinin Budda ne.

Asalin hoton, Mahesh Shantaram
An samu ƙawance tsakanin Musulmai da gwamnati na kusan shekara 30 lokacin da take yaki da 'yan tawayen Tamil Tiger, wadanda suka yi yakin kwatar 'yancin yankin Tamil mara rinjaye.
Shugaban Musulman ya ce gama yaƙin ke da wuya sai hukumomi suka juya musu baya a watan Mayun 2009.
Masu fafutuka sun ce an ta samun zanga-zangar kin jinin Musulmai, inda aka rika kai hare-hare gidajensu da wuraren sana'arsu a hukumance, kuma wannan ya faru ne tun kafin a kai harin ranar Easter.

Asalin hoton, EPA
Yayin annobar korona, gwamnati ba ta yarda an rika binne gawar Musulmai marasa rinjaye da kuma mabiya addinin Kirista ba.
An tilasta kona gawawwaki da yawa, duk kuwa da cewa kwararru sun ce za a iya binne gawar matattun. Ƙona gawa rahamun ne a addinin Musulunci.
Hukumomi sun rika cewa idan ana binne gawawwakin za su lalata kasa da ruwan da ake sha na cikin karkashin kasa.
Bayan wata yar kwarya-kwaryar zanga-zanga da Musulmai da kuma masu fafatuka suka yi, shi ne gwamnati ta ware wani wuri da za a rika binne gawawwakin da cutar ta kashe a kudancin kasar.
A bara, gwamnati ta fitar da wata doka da hana sa nikabi da duk wani abu da zai iya rufe fuska, suna cewa saboda matsalar tsaro. Minista ya ce haka alama ce ta tsattsauran ra'ayin addini da ake fama da shi a baya-bayan nan".
Akwai kuma shirin sanar da rufe makarantu kusan 1,000 na musulmai, wadanda gwamnati ta ce suna sauya tsarin koyarwar da aka yarda da shi a kasar.
"A wani yanayi na take-take shiga yaƙi, Musulmai sun zama wasu sabbin abokan gabar gwamnati," in ji Bhavani Fonseka, lauyar kare hallin dan adam.
Mun ga yadda aka riƙa kai wa Musulmai hare-hare. Zan iya cewa al'ummar Musulmai na cikin tasku," in ji ta.

Amma gwamnati na tafiyar da lamarin tuhume-tuhumen da ake yi wa Musulman da son zuciya.
Mohan Samaranayake, wanda darakta ne a ma'aikatar yada labarai ta Sri Lanka ya shaida wa BBC cewa, "Babu wata al'umma da ake nuna wa wariya.
"Amma zan iya yarda da cewa ana samun matsala tsakanin al'ummomi ciki kuwa har da Sinhalawa.
Amma game da maganar rufe makarantu, ya ce "an gudanar da bincike kan cewa harin da aka kai ranar Easter na da alaka da irin abubuwan da ake koyarwa a mahnajar karatun makarantun Musulmai."
Gwamnati na son kara tunzuro wata rigima ta hanyar samar da dokar bai daya ga duka al'ummar kasar.
Masu suka na cewa, "wata tawagar jami'an tsaro" da shugaban kasar Rajapaksa ya kafa za ta mayar da hankali ne kan marasa rinjaye a kasar.
Kasar dai dama na fuskantar matsalar tattalin arziki, saboda yadda kudaden ajiyar kasashen ƙetare farashinsu yake tangal-tangal.
Hanin da aka sanya na shigo da kayayyaki ya janyo tashin farashin kaya da sama da kashi 30 a shekarar da ta gabata, abin da ya janyo wa gwamnatin bakin jini ko cikin mabiya addinin Budha.











