Wasu muhimman abubuwan da suka faru na tarihin Musulunci a watan Ramadan

Yakin Badr

Asalin hoton, Haramain Sharifain

Bayanan hoto, Sahabban Annabi 14 ne suka yi shahada a yaƙin Badr

Ga musulmin duniya, watan Ramadan, wata ne mai alfarma kuma wanda abubuwa suka faru a cikin watan tarihin Musulunci.

Ramadan wata ne mai alfarma da Musulmai ke shafe tsawon watan suna Ibadar azumi, ɗaya daga cikin shika-shikan Musulunci.

Baya ga kasancewa watan Ibadah, abubuwan tarihi da dama sun faru a cikin Ramadan, wanda shi ne wata na tara a kalandar Musulunci.

Sheikh Muhammad Mashhud ya yi wa BBC bayani kan wasu muhimman abubuwan da suka faru a watan Ramadan, duk da cewa akwai abubuwa da dama na tarihi da suka faru a watan mai alfarma.

Saukar da Al Kur'ani

Babban muhimmin abu da ya faru a watan Ramadan, kuma mafi muhimmanci ga Musulmi a watan shi ne saukar da Al Kur'ani mai tsarki ga Annabi Muhammad SAW.

Allah ya bayar da labarin saukar da Al Kur'ai kuma an fara saukar da Al Kur'ani ne a daren Laylatul Kadr a watan Ramadan.

Daren Laylatul-Ƙadr a watan Ramadan darajarsa ta fi ta wata dubu.

Yaƙin Badar

Yaƙin Badar ya faru ne a ranar 17 ga watan Ramadan, shekara biyu bayan Hijrar Manzon Allah daga Makkah zuwa Madina.

A yaƙin ne Musulmi suka yi nasara, duk da maƙiya sun fi su yawa.

Sahabban Annabi 14 ne suka yi shahada a ranar.

A yaƙin ne aka kashe Abu Jahl, ɗaya daga cikin manyan maƙiyan manzon Allah.

Kwace Makkah

Shekara takwas bayan Hijra a ranar 18 ga Ramadan Annabi SAW ya shiga Makkah tare da runduna domin karɓe ikon Makkah, wanda kuma aka yi nasara cikin lumana, duk da cewa ba a yi fito na fito ba.

Kama wannan ne ya kawo ƙarshen bautar gumaka a Makkah, ɗaya daga cikin lokuta mafi muhimmanci a tarihin addinin Islama.

Mutane da dama ne suka karɓi addinin Musulunci bayan samun nasarar.

Rasuwar Nana Khadija RA

Wannan ne kabarin Nana Khadija R.A, matar Manzon Allah S.A.W ta farko, a gefe kuma kabarin babban dansa ne Kasim R.A.

Asalin hoton, Haramain Sharifain

Bayanan hoto, Wannan ne kabarin Nana Khadija R.A, matar Manzon Allah S.A.W ta farko, a gefe kuma kabarin babban dansa ne Kasim R.A.

Nana Khadija RA ta rasu ne a ranar 10 ga watan Ramadana.

Ita ce matar Manzon Allah ta farko, kuma ta farko da ta karɓi addinin Musulunci.

Ta kasance mafi karfi da goyon baya ga kafuwar Musulunci.

Rasuwar Nana Aisha RA

A ciki shekara ta 58 bayan Hijra, Nana Aisha RA matar Manzon Allah ta rasu.

Ta rasu ne 17 ga watan a Ramadan.

Ta taka muhimmiyyar rawa a Musulunci. Wasu malamai sun tafi akan cewa kashi ɗaya bisa hudu na koyarwar Musulunci Nana 'Aisha RA ce ta ruwaito.

Rasuwar Sayyidina Ali

A ranar 19 ga watan Ramadan aka sari Sayyidina Ali Ibn Abi Talib (RA) da takobi.

Ya rasu a ranar 21 ga Ramadan shekara 40 bayan Hijrah saboda raunin da ya samu daga harin da aka kai masa.

Sayyidina Ali shi ne na hudu cikin Khulafur Rashidun Khalifofin Manzn Allah.

Yaƙin Tabuk

Yaƙin Tabuk na cikin muhimman abubuwan da suka faru a tarihin Musulunci a watan Ramadan

Annabi SAW ya tura Sayyidina Ali RA a matsayin jagoran rundunar yaƙi zuwa Yemen.

Mutane da dama ne suka musulunta kuma suka ƙara yawan rundunar Musulmai.