'Da alamu 'yan Ansaru ne suka kai hari jirgin kasa na Abuja-Kaduna - Bukarti

Masana da masu nazari kan harkokin tsaro a Yammacin Afirka sun bayyana cewa da alama 'yan kungiyar Ansaru, wacce ke ikirarin kishin Musulunci, ne suka kai hari kan jirgin kasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a watan jiya.
A ranar Laraba ne, wani bidiyo da aka fitar ya nuna wasu daga cikin maharan ɗauke da bindigogi suna iƙirarin cewa su ne suka sace fasinjojin jirgin ƙasan a ranar Litinin din makon jiya.
Bidiyon, wanda bai kai tsawon minti 1:30 ba, ya nuna huɗu cikin 'yan bindigar sanye da kakin sojoji fuskokinsu a rufe a tsaye suna iƙirarin ci gaba da riƙe fasinjojin jirgin ƙasa da suka sace a ƙarshen watan jiya.
Ba a ga fasinjojin a cikin taƙaitaccen bidiyon ba, amma mutanen da suka yi maganar sun tabbatar da cewa suna riƙe da su.
Sun yi barazanar kashe fasinjojin da suka sace matuƙar gwamnatin Najeriya ba ta biya musu buƙatunsu ba.
Hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa ta Najeriya, a wata sanarwa, ta ce fasinja 362 ne a cikin jirgin da aka kai wa hari ranar 28 ga watan Maris din da ya gabata.
"An tabbatar da cewa fasinjoji 186 da suka shiga jirgin suna cikin koshin lafiya a gidajensu. Sannan akwai karin mutum 14 da su ma yau aka tabbatar sun tsira.
Wayoyin salula na mutum 51 da suka shiga jirgin suna kashe ko kuma ba a iya samun su bayan kiran da aka yi musu tun daga ranar Talata da safe," in ji sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa fasinja 22 ne suka ɓata, kamar yadda 'yan uwansu suka bayyana wa hukumar.
'Dalilin da ya sa na ce 'yan Ansaru ne'

Asalin hoton, Other
Sai dai a bayanin da fitaccen masanin nan kan sha'anin tsaro, Barista Bulama Bukarti, ya yi wa BBC Hausa game da bidiyon, ya bayyana dalilan da suka sa ya ce 'yan Ansaru ne suka kai harin.
"Kwakkwafin takaitaccen bidiyon da suka fitar na bi, kuma na ga wasu alamu akalla uku wadanda suke alamta cewa 'yan bindigar ba irin wadanda ake kira 'bandits' ('yan fashin daji) ba ne.
"Sun fi kama da 'yan Boko Haram - kuma a cikin 'yan Boko Haram din ma, wadanda suke bangaren Ansaru, masu alaka da Al-Qaeda," in ji masanin.
Ya kara da cewa abu na farko da ya nuna cewa su ne suka kai harin shi ne yadda suka bude bidiyon da kalaman addinin Musulunci.
Yana mai cewa kungiyoyi masu da'awar Jihadi da malaman addinin Musulunci ne kawai suke bude magana da irin wadannan kalamai "kuma ba mu taba ganin bidiyon bandits sun yi irin wannan ba."
Barista Bukarti ya ce: "Abu na biyu shi ne, wadanda suka yi magana a cikin wannan bidiyo, mutum biyu, sun yi ne da karin harshen Hausar da ba irin ta bandits ba.
"Abin takaici shi ne yawancin bandits suna magana ne da Hausa mai karin harshen Fulatanci. Amma wadannan Hausarsu ta fi kama da ta Kanuri, ta Barebari."
"Dalili na uku shi ne daidaikun kalmomi da kuma yaren da aka yi amfani da su a cikin wannan bidiyon.
"Misali, a lokacin da suka yi magana a kan abin da za su yi nan gaba sai suka ce 'In Sha Allah'. Bandits ba sa haka.
"Sannan a wajen karshe da suka yi barazana ba su ce za su yi kisa ba, cewa suka yi za su mayar da mazauninsu kwata. Wannan salon magana ne na 'yan Boko Haram", a cewar Bukarti.
Ya ce ita kanta shigar da suka yi - ta kayan sojoji da yadda suka rike bindigogi - ta nuna irin yadda mayakan Boko Haram suke yi, yana mai cewa da ma "mun san akwai 'yan Boko Haram a wannan yanki na Kaduna.
'Yan Ansaru sun ci gaba da zama a yankin Arewa maso Yamma tun daga 2012 lokacin da suka ɓalle daga wajen Shekau."
A makon jiya, Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-rufai ya shaida wa manema labarai cewa 'yan Boko Haram ne da hadin gwiwar 'yan fashin daji suka kai hari kan jirgin kasan na Abuja zuwa Kaduna.











