Gaskiyar bidiyon ƴan bindiga a wani daji da aka yaɗa cewa a Najeriya ne

Asalin hoton, Getty Images
Binciken BBC ya gano cewa wani bidiyo da aka yi ta yaɗawa a shafukan sada zumunta a Najeriya na wani jirgi maras matuƙi da aka ce na wasu ƴan bindiga ne a wani daji, ba a Najeriya ba ne.
Bidiyon ya nuna wani daji fetal marar sarƙaƙiya inda aka ga mutum biyar, wasunsu sun rufe kawunansu da wani jan mayafi, suna riƙe da manyan bindigogi kamar AK47 sun kuma haɗa wuta suna girki.
Ana kuma iya ganin dabbobi kamar su shanu da awaki da tumaki a gefen mutanen a cikin bidiyon.
Babu murya a cikin bidiyon domin haka ba za a gane yaren da mutanen ke yi ba, amma ana iya ganinsu suna murmushi yayin da suka ɗaga kai suna kallon jirgi maras matuƙin.
Ɗaya daga cikinsu ya saita jirgin da bindigarsa.
Idan aka duba sosai za a ga bargon da mutanen suka lulluɓa da shi yana kama da irin wanda wasu al'ummu a yankunan West Pokot da Samburu da Baringo da kuma Turkana na Kenya ke amfani da su.
Waɗannan yankuna ne da ke fama da rikice-rikice daban-daban.
Su kuwa ƴan bindiga a Najeriya sun fi amfani ne da kaki irin na soji da baƙaƙen rawani da suke rufe kawunansu da fuskokinsu.
Wasu daga cikin ƴan bindigar a bidiyon ba sa sanye da riguna, wasu kuma suna sanye da fararen riguna masu hula.
Sannan an gano cewa wani kamfanin tsaro da ke Nairobi, na Victory Security Africa Group ne ya fara wallafa bidiyon ne a shafinsa na Facebook, ranar 23 ga watan Fabrairun 2022.
An sanya wa bidiyon taken 'Jirgi marar matuƙi ya gano ƴan bindiga a Laikipia'.
Laikipia wani yanki ne a Kenya.
Daga nan ne sai wasu masu amfani da shafukan sada zumunta a Kenya suka fara yaɗa bidiyon da wani taken na daban.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Wani ɗan siyasa a Najeriya Jackson Ude ya yaɗa bidiyon a Tuwita, yana ikirarin cewa ƴan bindiga da Fulani Makiyaya ne a maɓoyarsu a wani daji a ƙasar.
An kalli bidiyon fiye da sau 10,000 a shafukan sada zumunta.
Sai dai tuni ya cire bidiyon daga shafinsa ya kuma bayar da haƙuri kan labarin ƙanzon kuregen da ya yaɗa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Shi ma wani ɗan siyasar, Joe Igbokwe ya wallafa bidiyon a Facebook yana cewa a wani daji a Najeriya aka ɗauki bidiyon, kuma mutanen da ke cikinsa ƴan bindiga ne da ke sace mutane a Najeriyar.
Zuwa yanzu an kalli bidiyon sau fiye da 3,000 a shafinsa, kuma ɗaruruwan mutane sun sake yaɗa shi.
Najeriya tana fama da matsalar hare-haren ƴan bindiga a arewacin ƙasa, waɗanda ke sace mutane don karɓar kuɗin fansa, ake kuma kashe mutane a garuruwa da dama.
Kwanan nan gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufa'i, jihar da ke fama da matsalar tsaro, ya ce gwamnatin ƙasar ta san wuraren da ƴan bindigar suke, amma sojoji sun ƙi kai musu hari saboda tsoron kar a kashe fararen hular da suke tsare a sansanonin ƴan bindigar.
A makon da ya gabata ne ƴan bindiga suka kai wa jirgin ƙasa mai ɗauke da fasinja 300 a kan hanyarsa daga Abuja babban birnin ƙasar zuwa Kaduna, inda mutum takwas suka mutu.











