Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hamzah bin Hussein: Wane ne ɗan Sarkin da ba ya so a kira shi Yarima a Jordan?
Yarima Hamzah bin Hussein, tsohon mai jiran gadon sarautar Jordan, ya ce ya yi watsi da matsayinsa na Yarima.
Yarima Hamzah ya ce "matakin na ƙashin kansa" bai tafi daidai da "tsarin zamani na hukumomin gwamnati ba."
Yariman shi ne ɗan Sarki Hussein na huɗu, kuma ƙani ga Sarki Abdallah da ke mulki a yanzu.
An yi masa ɗaurin-talala a bara bayan ya zargi shugabannin ƙasar da rasha da rashin iya shugabanci.
A watan Maris, Jordan ta wallafa takardar afuwa da aka ce mai ɗauke da sa hannun Hamzah yana neman gafarar Sarki Abdullah.
A wata sanarwa da aka wallafa a twitter a ranar Lahadi, Hamzah ya ce: "Sakamakon abubuwan da na tabbatar a shekarun baya, na yanke hukunci na kaina kan abin da mahaifina ya ɗora ni akai, wanda na yi ƙoƙari na ginu akai, ba su dace da hanyoyin da ake bi ba, da tsarin da ake bi na hanyoyin zamani da cibiyoyinmu.
"Daga maganar gaskiya ga Allah, babu abin da nake gani illa na yi watsi da matsayina na Yarima. Na samu babban damar yi wa ƙasa ta mai daraja aiki da kuma al'ummata a tsawon shekarun rayuwata.
"Zan ci gaba kamar yadda nake har tsawon rayuwata, mai yin biyayya ga ƙasata Jordan.
Wane ne Yarima Hamzah?
Babban ɗan Sarki Hussein da matarsa Sarauniya Noor, Yarima Hamzah ya kammala karatunsa a Birtaniya Makarantar Harrow da kuma makarantar sojoji ta Royal Military Academy da ke Sandhurst.
Ya yi karatu a Jami'ar Harvard a Amurka, kuma ya yi aiki a rundunar sojin Jordan.
A 1999 aka naɗa shi Yarima mai jiran gado, kuma wanda Sarki Hussein ke son ya gaje shi, wanda yake yawan bayyana shi a matsayin "farin cikin ido na."
Amma ana ganin yayi yaro kuma da rashin ƙwarewa a bayyana shi a matsayin magajin Sarki Hussien, lokacin mutuwarsa.
Maimakon haka yayansa wanda ba mahaifiyarsu ɗaya ba, Abdullah, ya ɗare kan gadon sarautar Jordan tare da tuɓe Hamzah daga sarautarsa ta Yarima mai jiran gado a 2004.
Matakin ana ganin ɓaraka ce ga Sarauniya Noor, da ke fatan babban ɗanta ya zama sarki.
A watan Afrilun 2021, Hamzah ya fitar da wani saƙon bidiyo inda ya yi iƙirarin cewa yana cikin ɗaurin talala a wani mataki na gwmanati na murkushe masu adawa da gwamnati tare da zargin shugabannin Jordan da Rashawa da rashin iya shugabanci.
Wannan na zuwa bayan kama manyan mutane da aka alaƙanta da zargin juyin mulki.
Yarima Hamzah ya musanta aikata abin da bai dace ba yana mai nesanta kan shi da ƙulla wani makirci.
Rundunar sojin Jordan ta musanta yi wa Hamzah ɗaurin talala, amma ta ce an ba shi umarnin daina yin duk wasu ayyukan da za su zama barazana ga tsaron Jordan.
Abdullah a cikin wani jawabi da ya yi wa ƴan ƙasa ta kafar talabijin ya ce komi ya daidaita Hamzah yana tare cikin iyalinsa kuma yana cikin kulawar fadarsa.
Wasu manyan jami'an Jordan daga baya an yanke masu hukuncin shekara 15 a gidan yari kan zargin juyin mulki, ko da yake dukkaninsu sun musunta.
Prince Hamzah ba a cika ganinsa ba a bainar jama'a ba tun faruwar al'amarin, amma wata takarda da masarautar Jordan ta fitar da ke zargin cewa Hamzah ne ya rubutawa ɗan uwansa.
"A bara, ƙasarmu Jordan ta fuskanci lokaci mafi ƙalubale a tarihi," kamar yadda aka ruwaito takardar ta bayyana.
"Watannin da suka gabata sun ba ni damar dibawa cikin gaskiya na rubuta maka.. tare da fatan za mu sauya wannan babin a ƙasarmu da kuma tarihin gidanmu."
"Na yi kuskure, Mai Martaba, kuma kuskuren na kan kowa, don haka ni ke da alhakin matsayar da na dauka da laifukan da na yi wa Mai Martaba da kasarmu tsawon shekaru da suka wuce, wanda ya kai ga faruwar saɓani.
"Ina neman gafarar Mai Martaba, tare da sanin cewa kai mai yafiya ne."