Yakin Ukraine: Ana fargaba kan makomar dabbobi

Zaki

Asalin hoton, Warriors of Wildlife

Bayanan hoto, Wani zaki da wani mutum ke tsare da shi a gidansa gabanin a ceto shi a watan Janairun 2022.
    • Marubuci, Daga Navin Singh Khadka
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Environment correspondent, BBC World Service

Akwai dabbobin da ake tsare da su irin su zaki, wanda yake cikin dabbobin da aka yi watsi da su saboda rikicin da Ukraine ta samu kanta a ciki.

Yayin da kauyen Hostomel da ke kusa da babban birnin kasar Kyiv ya fara fuskantar hare-haren dakarun sojin Rasha a watan Maris, Asya Serpinska ta ga gidan makociyarta na ci da wuta.

Ta san cewa akwai dabbobin da ake tsare da su a gidan, kuma ta ga an fito da makociyarta daga cikin gidan ranga-ranga a motar asibiti, sai ta ruga da ita da kawarta domin kashe wutar.

"Mun yi maza mun bude kejin da ake tsare da su mun saki wasu tsuntsaye, da zomaye da kuma wasu kananan dila," in ji ta.

Sun san cewa akwai wata zakanya da ake kira Rura, bayan kuma sun bincika sun gano wata zakanyar mai shekara biyu a ginin karkashin kasa na gidan.

"Babu wanda zai rika ba ta abinci da ganinta a rikice take ga kuma damuwa. Don haka sai muka fara ba ta abincin kare da ruwa," in ji Ms Serpinska, mai shekara 78, wadda ke tafiyar da daya daga cikin manyan wuraren kiwon karnuna a Ukraine.

"Muna jiran hare-haren su sassauta ne mu je mu ganta, saboda babu mai lura da ita."

Asya Serpinska

Asalin hoton, Asya Serpinska

Bayanan hoto, Asya Serpinska, mai shekara 78, tana lura da karnuka 1,000 da maguna 200

Cikin kwanaki tara ta ji ba ta da kwanciyar hankali ta bar gidanta. A ranar Litinin 14 ga watan Maris, ta yanke shawarar kai wa Rura abinci da ruwa, amma sai ta yi gamo da sojojin Rasha a hanya. Suka ce sun bai wa zakanyar ruwa kwana daya kafin nan, kuma yanzu an hana kowa shiga yankin.

Masu lura da jin dadin dabbobin sun ce Rura ba wata dabba ce ta daban ba. Sun yi hasashen cewa akwai dubban dabbobi da ake tsare da su a gidajen daidaikun mutane a Ukraine, ciki har da zakuna da damisoshi da diloli da dai sauransu.

A lardin Saltivka da ke Kharkiv a arewa maso gabashin Ukraine, masu rajin kare hakkin dabbobi na son ceto wasu zakuna biyu da wasu damisoshi daga gidajen daidaikun mutane tun kafin Rasha ta fara mamaya.

"Bayan an fara yakin, masu wadannan dabbobin sun tsere daga biranensu sun kuma bar dabbobin ba tare da wata makoma ba," in ji Iryna Korobko, mai fafutukar kare hakkin dabbobi.

Luguden wutar da Rasha ta yi a yankunan ya hana kowa zuwa duba dabbobin.

"Halin da wadannan dubban dabbobin da ake tsare da su a gidajen mutane za su shiga a yayin yakin nan ba karami ba ne," in ji Ms korobko.

Akan tsare su cikin yanayi mara kyau, in ji shugabar hukumar kula da dabbobi ta Ukraine, Maria Trunova.

"Muna yawan damun hukumomi su yi abin da ya dace ko da yaushe. Amma a yanzu da ake yawan kai hare-hare ba a san wane mugun yanayi za su shiga ba saboda firgici, ga yunwa ga sanyi kuma za su iya mutuwa."

Bear in a bear sanctuary

Asalin hoton, Getty Images

Ana iya sayan dabbobi kamar su zaki da damisa kan dalar Amurka 1,500 a Ukraine, in ji yar fafutukar, kuma wannan ba wani abu ba ne matukar za su rika haihuwa.

Bayan fafutukar da masu rajin kare dabbobi ke yi, gwamnatin Ukraine ta gabatar da wata doka a bara da ta haramta amfani da dabbobin da ake kiwo a gida a wuraren sayar da abinci, inda ake amfani da su domin nishadantar da abokan hulda.

Kuma sun hana mabarata amfani da dabbobin, haka ma masu daukar hoto da ke kai su wajen masu yawon bude ido a yi hotuna da su a kan titunan Kyiv da sauran birane.

A yanzu haka akwai kyakkyawan labarin cewa akwai karnuka 1000 da maguna 200 da ke karkashin kulawar Ms Serpinska. Tana kuma ba su abincin karnuka ne duka suna ci da kuma ruwa, bayan wasu hare-hare sun lalata na'urar da ake zuko musu ruwa daga rijiya da ita.

Ms Serpinska ta ce tana tunanin sakin karnukan, " domin ba ta son su mutu a gabanta.".

Amma yanzu sojojin Rasha sun bayar da umarnin kai abincin karnuka, da kuma kayan da za a iya amfani da su domin samar musu ruwan sha.