Yarima Charles ya bi sahun sauran mutanen duniya wajen jinjina wa mahaifiyarsa

The Queen

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Sarauniya Elizabeth

Yariman Wales ya jinjina wa Sarauniya Elizabeth game da "gagarumar nasarar" da ta samu a bikin cikarta shekara 70 a kan karagar mulki.

Yarima Charles ya yi maraba da fatan mahaifiyarsa cewa Camilla, wadda ita ce Duchess ta Cornwall, a ba ta mukamin Uwargida Sarauniya idan ya zama Sarki.

Ya ce shi da matarsa ​​"suna matukar sane da karramawar".

Sarauniyar ita ce yar sarautar Biritaniya ta farko da ta yi bikin cikar shekara 70 a kan mulki, inda ta shafe ranar a keɓe.

A cikin sakon bikin cika shekara 70 na mulkinta, Sarauniyar ta ce "burinta na gaske" ne Camilla ta sami wannan mukami.

A cikin wata sanarwa da Yarima Charles ya fitar ya ce: "Sadaukarwar da sarauniya ta yi don jin dadin jama'arta na kara janyo mata farin jini a kowace shekara.

"Muna matukar sane da irin karramawar da uwata ta yi mana. A yayin da muka tsaya tare domin mara mata baya tare da yin hidima da tallafa wa al'ummar yankinmu, uwargidana ta kasance mai goyon bayana a duk tsawon lokacin."

The Queen

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Sarauniya Elizabeth

Sarauniyar ta soma mulki tana da shekaru 25, bayan rasuwar mahaifinta, George VI, a ranar 6 ga Fabrairun 1952.

Sarauniyar ta ce, shekaru 70 kenan, kuma wannan rana ce da ba za ta manta da ita ba "kamar rasuwar mahaifina, Sarki George na shida, dangane da farkon sarautata".

Sarauniyar mai shekara 95 a duniya ta fada a cikin rubutaccen sakon da ta aike wa al'ummar kasar cewa: "Ina so in mika godiyata a gare ku duka bisa goyon bayan da kuke ba ni. ."

Wannan shi ne biki na farko da sarauniyar za ta yi ba tare da mijinta Duke of Edinburgh ba, wanda suka yi shekaru 73 da aure, wanda ya mutu a bara.

Ta yi la'akari da irin nasarorin da ta samu daga tallafin da Yarima Philip ya ba ta "ba tare da son kai" ba kuma ta gode wa irin kyakkyawar niyya da "dukkan al'ummomi da addinai da shekaru a kasar nan suka nuna mata".

Mutane da yawa sun taya Sarauniya murna a wannan rana mai cike da tarihi, ciki har da Boris Johnson, Theresa May da David Cameron - uku daga cikin firaministan Birtaniya 14 da suka yi a fadar firaminista ta No 10 a lokacin mulkinta.

Mista Johnson ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: "Ina jinjina mata da yawa na hidimar da ta yi, kuma ina fatan za mu kai a matsayin wajan taya ta gudanar da bikin cika shekaru 70 a kan mulki a lokacin bazara."

Matar da ta gabace shi, Misis May, ta bayyana sarauniyar a matsayin "mace mai ban mamaki, wadda ta sadaukar da rayuwarta wajen yi wa jama'arta hidima da kuma danginmu na kasa".

Mista Cameron ya ce : "Ba za a iya samun kyakkyawan misali na aikin jama'a mai daraja da hidima ba."

Jagoran 'yan hammaya, Sir Keir Starmer, ya yi na'am da wadannan ra'ayoyin, yana mai cewa zai so ya mika godiyarsa ta tsawon shekaru 70 da ta yi na hidimar jama'a mara misaltuwa.

Shugaban kungiyar ta Labour ya kara da cewa: "Sarauniyar ta kasance mai matukar muhimmanci kuma mai kima a cikin duniyar da ke canzawa, wanda ke wakiltar tsaro da kwanciyar hankali ga kasarmu, a cikin abubuwan da suka faru a cikin shekaru saba'in da suka gabata."