Matsalar tsaro: Mahara sun sace mutane a gidan wani basarake a Sokoto

h

Matsalar tsaro na ci gaba da addabar yankunan kananan hukumomi takwas da ke gabashin jihar Sakoto a arewacin Najeriya.

Ko a ranar Talata sai da aka wayi gari da aukuwar wani harin a garin Ambarura na karamar hukumar Illela, inda 'yan bindiga suka sace mutane.

Maharan dai sun yi wa garin na Ambarura dirar mikiya ce da tsakar dare, inda suka kaddamar da harin kan mai uwa da wabi.

Dan majalisar yankin Honarabul Bello Isa Ambarura, mai wakiltar karamar hukumar Illela a majalisar dokoki ta jihar Sakkwato, ya shaida wa BBC cewa maharan sun far wa gidan basaraken na Ambarura, inda suka sace yara 'yan mata tsakanin shekara 12 zuwa 13, da masu hidima sun kai mutum biyu, da kuma dattijai har da matasa.

Ya ce, ''daman mun dade mu na fuskantar matsala, musamman gabashin Sokoto, misali garuruwa kamar Gwadabawa, Raba, Wurno, Isa, Sabon Birni da sauransu, saboda dukka su na bakin iyaka ne.

Duk matan da gwamnati ke dauka su na kokari amma su kara saboda lamarin ya munana, a kuma ja kunnen jami'an tsaron da ake kai wa yankin domin tabbatar da an yi abin da ya dace.''

BBC ta yi kokarin jin ta bakin jami'in hulda da jama'a rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Sakoton, kuma ya ce zai bincika ya sake kiranmu, amma har ya zuwa lokacin wallafa wannan rahoto ba mu ji daga gare shi ba.

'Yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare a sassan jihar Sokoton, inda lamarin ke kai ga asarar rayukan jama'a da barnata dukiya.

Sai kuma uwa uba satar mutane domin neman kudin fansa, wadda ta ki ci ta ki cinyewa a yankin.