Me ya sa 'yan bindiga suka koma kai hare-hare Sokoto?

..

Asalin hoton, Aminu Waziri Tambuwal/Facebook

    • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
  • Lokacin karatu: Minti 4

Jihohin arewa maso yammacin Najeriya na daya daga cikin yankunan Najeriya da 'ƴan bindiga suka addaba, sai dai a baya, jihar Sokoto ta kasance wadda ta fita zakka cikinsu, saboda yanayin kwanciyar hankali a Sakkwato da kewaye.

Sai dai a yanzu, wannan zance na neman sauyawa, don kuwa tuni 'yan bindiga suka fara addabar wasu kauyukan jihar.

Ko a cikin watan jiya ma, sai da daruruwan mazauna wasu kauyuka suka tsallaka iyaka zuwa Jamhuriyar Nijar don samun mafaka bayan'yan fashin daji sun fatattake su daga matsugunansu.

Kauyuka musamman da ke yankin Sabon Birni a halin yanzu za a iya cewa sun shiga wani mawuyacin hali, saboda yawan rahotannin da ake samu na fashi da makami da garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa.

A jihar Zamfara da ke makwabtaka da Sokoto ma, da irin haka ayyukan rashin tsaro suka fara lamarin da har ya zamana kananan hukumomi da dama sun fada hannun 'yan bindiga.

Jihar Katsina ma da ke cikin yankin, wasa-wasa hare-haren 'yan fashin daji na daɗa gawurta inda har yake son ya wuce yanayin da jihar Zamfara ta taɓa tsintar kanta ciki.

Jama'ar da ke yankin Sabon Birni a jihar Sokoto na ci gaba da zaman ɗar-ɗar, domin kuwa harin da aka kai na baya-bayan nan ya tayar da hankulan jihar da ma ƙasar gaba ɗaya.

Fiye da mutum 70 ne 'yan bindiga suka kashe a kauyuƙan Gwadabawa da Garki da Dan adu'a da Kuzari inda waɗanda suka shaida lamarin ke cewa maharan sun shafe tsawon sa'o'i suna ta'adi a kauyukan ba tare da jami'an tsaro sun tunkare su ba.

..

Asalin hoton, UGC

Me ke faruwa a Sokoto

Dangane da wannan lamari na jihar Sokoto, BBC ta tattauna da wasu masharhanta harkokin tsaro domin jin ko me suke gani kan abubuwan da ke faruwa.

Hange da hasashe da kuma ra'ayoyin masu sharhi kan lamarin da ke faruwa a Sokoto ya zo kusan ɗaya domin tun a farko, dukkaninsu sun bayyana cewa farmakin da sojoji ke kai wa 'yan bindiga a jihohin Zamfara da Katsina ne ya tilasta musu tserewa zuwa Sokoto.

Abubakar Yelwa, malami a sashen nazarin daƙile miyagun ɗabi'u a Kwalejin Kimiyya da Fasaha Ta Tatari Ali da ke Bauchi, ya ce "ganin irin waɗannan abubuwa ba sa faruwa a baya, wannan ne ya sa ba a yi shirin ko ta kwana ba.

Don haka 'yan bindigar suka samu sarari domin can an takura musu, nan kuma ga wata ƙofa a buɗe".

Ya bayyana cewa duk da a kullum sojoji na bayyana cewa suna samun nasara kan 'yan bindigar a wasu jihohi, amma farmakin 'yan bindigar ƙaruwa yake yi.

Shi kuma Manjo Yahaya Ibrahim Shinku murabus, wani mai sharhi kan al'amuran tsaro a Najeriya na cewa "babu wani takamaiman tsari da gwamnati ta yi na samar da rundunar tsaro a wannan yanki na Sokoto".

Hakan ya sa 'yan bindigar suke zuwa su yi barna," in ji shi.

Manjo Shinku ya kuma ce a halin yanzu babu isassun jami'an tsaro a jihar Sokoto wanda hakan ya sa 'yan bindigar ke cin karensu babu babbaka.

Sai dai ya ce yana yi wa gwamnatin kowacce jiha a Najeriya uzuri ta bangaren tsaro, domin kuwa a cewarsa "a irin tsarin mulkin Najeriya, an tattara ƙarfin tsaro an damƙa wa tarayya da shugaban ƙasa ne".

"Gwamnatin tarayya (ce) ke biyan 'yan sanda albashi da kuma ɗaukar su aiki, ita kuma ke ba su umarni, shi gwamna taimakon da yake iya yi kawai shi ne ya ce ga kayan aiki da kuma kuɗin zuba man fetur a mota," tsohon sojan ya ce.

..

Asalin hoton, Getty Images

Ina Mafita?

Abubakar Yelwa a nasa bangaren ya ce jama'ar da cutar korona ta kashe a Najeriya ba ta kai yawan mutanen da suka salwanta sanadin ɓarnar da 'yan bindiga ke yi a ƙasar ba.

Ya bayyana cewa saboda wannan cuta, an tsayar da kusan komai a ƙasa tare da kashe maƙudan kudi wajen yaƙi da ita.

Ya ce "Da an yi rabin abin da aka yi wa korona a harkar tsaro da tuni an samu ci gaba."

Duk dabarun da za a yi na kama 'yan bindigar nan da rai ya kamata a yi hakan, domin 'yan Najeriya na buƙatar su riƙa ganin 'yan bindigar da kuma hukuncin da za a yanke musu, in ji shi.

Shi kuwa Manjo Shinku cewa ya yi ya kamata shugaban ƙasa da 'yan majalisun tarayya su tashi tsaye don ganin an samu runduna ta musamman da za a tura wannan yanki kuma ta zauna dindindin ba wai na mako biyu (kawai) ba.

A cewarsa, duk wani ƙokari da gwamnati za ta yi na tabbatar da tsaro a yankin Katsina da Zamfara, idan ba a toshe bangaren Sokoto ba, abin ba zai yi wani tasiri ba.

Ya kuma ce "idan jami'an tsaro ba su mayar da hankali kan Sokoto ba, haka jama'a za su yi ta shan azaba a 'hannun yan bindiga".

A kwanakin baya ma, sai da wata ƙungiya mai bincike kan tashe-tashen hankula a kasashen duniya wato International Crisis Group, ta ce an kashe mutane fiye da dubu takwas a rikicin arewa maso yammacin Najeriya cikin shekara 10.

Kungiyar ta ce fiye da mutum dubu dari biyu ne rikice-rikice da kuma hare-haren 'yan fashin daji suka raba da muhallansu a yankin cikin wannan lokaci.

Kauce wa Facebook

Babu karin bayanai

Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.

Karshen labarin da aka sa a Facebook