Kalli yadda Fulanin ruga ke shagalin bikin aure

Bayanan bidiyo, Yadda ake kai amarya a bikin Fulani

Latsa hotonsama domin kallon shagalin bikin Fulani

Fulani kabila ce da kusan babu inda ba za a same su ba a dukkanin kasashen Afirka ta Yamma.

To sai dai ba kamar yadda suka yi shura ba da kiyo, suna da wata al'ada da ta sha banban da ta sauran kabilu.

Fulani a arewacin Najeriya na gudanar da shagulgulan bikin aurensu a tsakar dare, inda ake kai amarya gab da sallar asubahi.