Guinea-Bissau: Ana fargabar juyin mulki yayin da aka ji karar harbe-harbe a fadar shugaban kasar

Shugaba Umaro Sissoco Embaló

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An zabi Shugaba Umaro Sissoco Embaló a shekarar 2019

Rahotanni daga Bissau, babban birnin Guinea-Bissau, sun nuna cewa an ji karar harbe-harbe a kusa da fadar shugaban kasar.

Rahotannin da ba tabbatar da su ba sun ce sojoji sun kewaye ginin fadar shugaban kasar.

An fahimci cewa Shugaba Umaro Sissoco Embaló yana cikin fadar.

Wasu majiyoyi sun ce watakila yunkurin juyin mulki aka yi.

Lamarin na faruwa ne a yayin da Shugaba Embaló da Firaiminista Nuno Gomes Nabiam suke gudanar da taro.

Wani mazaunin birnin ya shaida wa shirin BBC Focus on Africa na rediyo cewa an kashe wani dan sanda sakamakon harbe-harben.

Wani mutum da ya shaida abin da ya faru ya gaya wa BBC cewa wasu mutane sanye da fararen-kaya rike da makamai sun bude wuta a wurin da shugaban kasar da firaiministan suke yin taro.

Mazauna Bissau sun shiga cikin firgici, yayin da kuma aka rufe makarantu da shaguna a babban birnin kasar.

Wasu majiyoyi sun ce ba a san inda shugabannin suke ba a halin yanzu.

Ministar harkokin wajen Guinea-Bissau Suzi Barboza ta shaida wa BBC cewa a halin yanzu ba ta kasar kuma tana jiran bayani game da inda shugaban kasar yake.

Kungiyar Ecowas ta yi alla-wadai da abin da ta kira "yunkurin juyin muki" a Guinea-Bissau, sannan ta yi kira ga sojoji da su koma barikokinsu.

A watan Disambar 2019 ne Mr Embalo ya yi nasara a zaben shugaban kasar, ko da yake sai da aka kai ruwa rana tsakaninsa da 'yan majalisar dokoki kafin ya soma aiki.