Korona: Kwararru sun ce ganganci ne karancin rigakafin korona a kasashe masu tasowa

Asalin hoton, Getty Images
Wata tawagar masana kimiyya da kuma kwararru a bangaren lafiya su fiye da 300 a Birtaniya, ta ce ba karamin ganganci bane a kyale mutum biliyan 3 a kasashe masu tasowa a duniya ba tare da an yi musu allurar rigakafin cutar korona ba.
Tawagar kwararrun dai na son gwamnatin Birtaniya ta goyi bayan Shirin sassauta ka'idojin da aka sanya na samar da rigakafin ta yadda kasashe masu tasowa zasu samu damar samar da ta su.
Gwamnatin Birtaniya dai ta ce tana aiki sosai wajen tabbatar da cewa kasashe masu tasowa sun samu wadatacciyar allurar rigakafin cutar koronar.
Daya daga cikin kwararrun wanda tsohon shugaban hukumar kula da inshorar lafiya ta Ingila ne Lord Crsip, ya shaida wa BBC cewa, yana da matukar muhimmanci gwamnatin Birtaniya ta yi Nazari a kan wannan batu.
Ya ce, "Akwai bukatar mu yi nazari a kan yadda karshen wannan annoba zata kasance da kuma damar da kasashe ke da ita wajen samar da allurar rigakafin ga sauran kasashen duniya".
Kwararren ya ce wannan ba ita ce annoba ta farko da aka samu ba, haka kuma bai ta ce ta karshe ba a don haka don kare yaduwar wasu annobar nan gaba akwai bukatar lallai a hada hannu da karfe wajen kare kwayar cutar tun daga tushe.
Gwamnatin Birtaniya dai ta ce ta taka muhimmiyar rawa wajen samar da shirin Covax da ke rarraba allurar rigakafin korona kyauta ga kasashe matalauta wanda tuni ya raba allurar da dama ga kashen a sassan duniya.
Kwararrun dai sun yi gargadin cewa idan har ba a yi wa kowa a fadin duniya allurar rigakafin ba, to kuwa babu wanda zai tsira don wadanda ba a yi musu ba za su rinka kamuwa da cutar sannan su rinka yadawa mutane har ma da wanda aka yi wa, haka kuma an rinka samun bullar wasu nau'ikan cutar.











