Yadda gwamnatin Buhari ta karya alkadarin Twitter

    • Marubuci, Daga Nduka Orjinmo
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja

Twitter ya amince da wasu jerin sharuda domin kawo karshen dakatar da shi a Najeriya, wanda ake ganin hakan wata babbar nasara ce ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a kokarinta na takaita abubuwan da ake yi da intanet, in ji wasu masana.

Yanzu dai Najeriya ta bi sahun kasashe irin su India da Indonesia da kuma Turkiyya, wadanda suka tsaurara dokoki a kan ayyukan kamfanonin intanet. Wannan wani abu ne da wasu kasashen Afirka za su iya kwaikwayo wajen hana 'yan hamayya amfani da shafukan sada zumunta da muhawara wajen janyo kungiyoyin da ba sa jituwa da gwamnati.

Wasu daga cikin dokokin da Twitter ya amince da su sun sanya tunani da fargaba a kan yadda ayyukan shafin za su iya kasancewa a nan gaba a kasar.

"Lalle abin damuwa ne ganin yadda Twitter ya amince da yarjejeniyar da za ta iya sa shi daukar matakin da Najeriya za ta iya matsa masa ya dauka a nan gaba, in ji David Greene, daraktan wata kungiya mai zaman kanta a Amurka, Electronic Frontier Foundation (EFF), a tattaunawarsa da BBC.

Ya ce abin da ya kamata Twitter ya yi shi ne, da kamata ya yi ya yarda da dokokin cikin gida na kasar, wadanda suka kare hakkin dan adam kawai. To amma abin da ya kasance yanzu shi ne yarjejeniyar ta sa gwamnatin ta ba wa kamfanin umarni da kuma neman bayanai a kan kamfanin, in ji Mr Greene.

Sauya matsaya bayan watsi da Najeriya

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun ce gwamnatin Buhari tana da tarihin take doka da 'yancin fadin albarkacin baki, inda ta tsare 'yan jarida da masu raji da ke sukar gwamnati.

Yanzu ana fargabar cewa hukumomi za su kara daukar matakan sanya tarnaki a kan masu amfani da shafukan intanet, kuma Twitter zai rika janye wasu sakonnin.

Twitter ya ki ya ce komai a kan yarjejeniyar da ya cimma da gwamnatin Buhari, abin da ya harzuka da dama.

Abin da kamafanin ya ce kawai shi ne yana murnar dawowa bakin aiki kuma ya damu da Najeriya ainun.

Sai dai BBC ta fahimci cewa sai da kamfanin ya amince da dokokin kafin a dawo da ayyukansa a Najeriya.

Abin ya zama kamar wani gagarumin sauyi na matsayar kamfanin da a shekarar da ta wuce ya ce bude babban ofishinsa na Afirka a Ghana, yana mai bayyana kasar ta Ghana a matsayin jigon dumokuradiyya da goyon bayan 'yancin fadin albarkacin baki da 'yancin amfani da intanet.

Mutane da yawa sun dauki wannan a matsayin cin-fuska ga Najeriya, kasa mafi girman tattalin arziki a Afirka.

Yanzu dai Twitter ya kasance daya daga cikin kamfanonin intanet da aka sanya wa tarnaki a karkashin sabon harajin intanet da aka amince da shi a 2020.

A farkon watan nan Ministar kudi Zainab Ahmed ta ce kamfanonin da ba a Najeriya suke ba za su rika biyan kashi shida cikin dari na cinikin da suke yi a kasar daga wannan shekara domin taimaka wa tattalin arikin kasar wanda ke fama da matsala.

Twitter ya amince ya biya haraji a Najeriya, sannan kuma ya bude ofis, ko da yake ba a san wane irin ofis zai bude ba ko zai yi rijista ne kawai karkashin wani kamfani.

"Kila a ga gagarumin bambanci dangne da irin matsin lambar da Najeriya za ta rika yi wa Twitter a nan gaba, da kuma yadda Twitter za ta iya jure wa bukatun Najeriya wadnda ba su dace ba, in ji Mr Greene.

Matasan 'yan Najeriya musamman ma wadanda suka kware da amfani da intanet, suna son Twitter sosai, saboda shafi ne da ya kunshi kusan komai, kama daga batun aiki da cigiyar mutanen da suka bata da kuma matsa wa ko binciken jami'an gwamnati.

Twitter ya yi babban tasirinsa ne a lokacin zanga-zangar neman kawo karshen rundunar musamman ta 'yan sanda mai yaki da 'yan fashi da makami#EndSars a 2020, a lokacin da shafin ya kasance dandalin da matasa masu zanga-zangar suka matsa wa Shugaba Buhari ya soke rundunar ta SARS, wadda ta yi kaurin suna wurin gana akuba.

Zanga-zangar #EndSars ta rikide ta zama ta yaki da gurbatacciyar gwamnti a Najeriya, abin da ya sa Shugaba Buhari ya ce masu zanga-zangr na neman hambare shi daga mulki ne.

Gwamnati ta zargi Twitter da rura wutar zanga-zangar kuma ta dora laifin a kan tsohon shugabanta, Jack Dorsey, wanda ya goyi bayan masu zanga-zangar, wadda ta rikide ta zama ta bannata kayan gwamnati bayan da bata-gari suka shige ta.

Masu goyon bayan gwamnati na murna

Ta fannoni da dama ana ganin halin da Twitter ya samu kansa a ciki a Najeriya, a matsayi kamar wani rikici tsakanin Mista Dorsey da Shugaba Buhari, abin da ya sa har aka goge sakon Buhari a tuwita a watan Yuni.

Sakon na nuni ne da tunatarwa a kan yakin basasa na Najeriyar na 1967-70, na ykin Biyafara, inda yake gargadin 'yan awaren Biayafaran na yanzu da ya ce suna rashin da'a da cewa za a fuskance su yadda ya dace.

Da wannan mataki da hukumomin Najeriya suka duka a kan Twitter, abu ne mai wuya a ce an iya sake shirya zanga-zanga irin ta #EndSars a shafin ba tare da hukumomin sun zargi shafin da saba dokokin kasar ba na neman angiza rikici.

To amma a wurin Gbenga Sesan na kungiyar kare 'yancin masu amfani da intanet Paradigm Initiative) shi yana ganin gwamnatin Najeriya ce ta yi asara a duk tsawon wlokacin wannan dambarwa ta wata bakawai, saboda ba ta samu damar yada sakonninta ba.

Ya ce manyan wadanda suka yi nasara su ne Twitter da kuma mutanen Najeriya, yayin da gwamnati ta kasance babbar wadda ta yi asara, in ji shi.

Kungiyarsa na daga cikin wadanda suka kalubalanci hanawar kuma Mista Sesan yana ganin gwamnati ta yi gaggawar dage haramcin ne domin gudun jin kunya, yayin da ake sa ran yanke hukunci a kotun kasashen yammacin Afirka, Ecowas a wannan makon.

''Ya [Shugaba Buhari] ji kunya saboda wannan abu ne na tarihi, rufewa ta farko a Najeriya," in ji shi.

Sai dai kuma masu goyon bayan gwamnati na muran da cewa hukumomin sun tilasta Twitter mika wuya.

Da yawa suna ganin goge sakon shugaban kasar shi ne shiga-sharo-ba-shanu mafi girma na siyasa da wani kamfani ya yi, saboda haka suna goyon bayan haramcin da aka yi wa kamfanin na Twitter.

A yanzu ana yi wa kamfanin shagube kan yadda ya amince da sharuddan na gwamnati da komawa bakin aiki domin zaben shugaban kasa na shekara mai zuwa.

Yakin neman zabe a Najeriya na daga cikin mafiya tsada a duniya. 'Yan takarar shugaban kasa za su iya kashe har kusan naira biliyan 15 (dala miliyan 36 ko fam miliyan 26) a yakin neman zabe kuma tallata kansu a shafukan intanet ya fi cin kudi.

Wannan abu ne da kamfanin Twitter, kamfanin da ke son ya ci gajiyar wannan garabasa ta samun karin kudi a Afirka, ba zai so damar ta wuce shi ba, in ji masu goyon bayan gwamnati.

Ko da yake dawowar kamfanin na Twitter a lokaci ta zo wa 'yan siyasar Najeriya daga dukkanin jam'iyyu a daidai.