Abin da Matawalle ya gaya wa tawagar da Shugaba Buhari ya tura jaje Zamfara

Asalin hoton, ZAMFARA GOVNOR BELLO MATAWALLE/FACEBOOK
Gwamnan jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ya ce rashin hukunta ƴan bindigan da ake kamawa a yankin na cikin matsalolin da ke yin cikas wajen daƙile miyagu.
Kazalika ya ce akwai buƙatar a samar kayan yaƙi irin na zamani, kafin a murƙushe ƴan bindigan da ke halaka jama'a a shiyyar.
Gwamna Muhammad Bello matawalle na Zamfara ya yi wannan furucin ne lokacin da tawagar gwamnatin tarayya ta kai ziyarar jaje jihar dangane da kisan da ƴan bindiga suka yi wa al'ummar ƙananan hukumomin Anka da Bukkuyum, inda suka kashe mutane da dama a ƴan kwanakin nan.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa na tallafa wa jami'an tsaro da ƴan sa-kai wajen yaki da ƴan bindiga ta hanyoyi da dama, amma abin baƙin ciki shi ne yadda miyagun suke ci gaba da kai hare-hare a kan jama'a.
Sai dai ya ce sun fahimci abin da yake faruwa, "wani dalilin da ya sa wannan matsala ta ƙi ci ta ƙi cinyewa shi ne rashin hukunta miyagun da ake kamawa.
"A lokuta da dama a kan saki ƴan bindigan ba tare da an yi musu shari'a ba, kuma wannan yana ƙara wa miyagun ƙrfin hali tare da kwaɗaitawa wasu su shiga aika-aikar.
"Duk da cewa sojojinmu suna da himma, wata matsalar da muka gano ita ce rashin kayan aiki irin na zamani, kuma yaƙin zamani ba ya yiwuwa sa ida akayan aikin na zamani.
Akwai buƙatar a samar da irin waɗannan kayan faɗa na zamani idan ana so a ci nasara a wannan yaƙin a jiar Zamfara da ma shiyyar arewa maso yammacin Najeriya," in ji shi.

Ƙara wa jami'an tsaro ƙarfi
Gwamnan ya bayyana cewa akwai alamun da ke nuna cewa Najeriya ka iya faɗawa halin rashin doka da oda ko irin yanayin nan na mai-karƙi-alƙalin-ƙauye, idan ba a wadata sojoji da sauran jami'an tsaro da kayan yaƙi irin na zamani ba.
Wannan ne ya sa gwamnan ya bai wa gwamnatin tarayya shawarar cewa ta yi amfani da sabbin jiragen yaƙin nan da ta samo daga Amurka, wato Super Tucano, wajen murƙushe ƴan bindigan.
Ya jaddada cewa da gwamnati za ta samar da tankokin yaƙi kamar guda dubu daya, a rarraba su a sassan Najeriya - da babu shakka za a ci galabar miyagun.
A cewar Gwamna Matawalle, an samu wasu hujjoji na yankan shakku da ke nuna cewa akwai dangantaka tsakanin ƴan bindigan yankin da Boko Haram, saboda haka akwai buƙatar a sauya dabarun yaƙin da ake yi ta yadda za a fuskanci zahiri.
Kuma duk abin za a yi, zai yi kyau idan aka ba da fifiko ga jihar Zamfara, saboda ta kasance kamar wata tunga ga miyagu, inda suke kitsa hare-haren da suke kai wa a cikin jihar sauran jihohi makwabta.

Me tawagar gwamnatin tarayyan ta ce?
Ministan tsaron Najeriya, Janar Bashir Salihi Magashi mai ritaya, ya ce sun je jihar zamfara ne domin su wakilci shugaban ƙasa wajen jajanta wa al'ummar jihar dangane da mummunan lamarin da ya faru ga waɗansu al'ummomin ƙananan hukumomin Anka da Bukkuyum, waɗanda suka gamu da iftila'in ƴan bindiga.
"Mun yi tir da abin da ya faru, kuma gwamnatin tarayya ta yi ɗamarar yin fiye da abin da ta yi a baya don daƙile aika-aikar miyagu.
"Tabbas miyagu sun daɗe suna tafka ɓarna, musamman ma yadda abun ya fara a shiyyar arewa ta tsakiya - sannan ya bazu zuwa shiyyar arewa maso yamma da wasu sassan Najeriya.
"Makasudin zuwanmu shi ne mu ba ka tabbacin cewa gwamnati na sane da abun da ya faru. Kuma za ta yi bakin ƙoƙarinta wajen magance matsalar a jihar Zamfara," in ji ministan.
Ya ce gwamnatin tarayya ta gano bakin-zaren, kuma dole ne ta yaba da ƙoƙarin da jami'an tsaro ke yi, kuma da yardar Allah haka ba za ta sake aukuwa ba.
Wani ayarin gwamnonin jihohin Najeriya da jam'iyyar APC mai mulki su ma sun kai ziyara jihar Zamfaran, ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Kebbi, inda ayarin ya jajantawa al'ummar jihar Zamfara, har ma suka yi alwashin hada-kai ta yadda za su gudu tare su tsira tare.
A makon jiya ne ƴan bindigan suka kai hare kan al'umomin da ke ƙananan hukumomin Anka da Bukkuyum, inda suka kashe aƙalla mutum 36.














