Zamfara: Ƴan bindiga sun kashe 'ɗumbin jama'a' a Anka da Bukkuyum

Asalin hoton, ZAMFARA STATE GOVERNMENT
Rahotanni daga Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa ƴan bindiga sun kashe gwamman mutane a jihar.
Ƴan bindigar waɗanda suka je garuruwan Anka da Bukkuyum a kan babura masu ɗumbin yawa, sun afka ƙauyukan da ke ƙarƙashin waɗannan garuruwan inda suka rinƙa harbi kan mai uwa da wabi tare da cinna wa gidaje wuta.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa mutanen da ƴan bindigan suka kashe sun haura mutum 100. Wani wanda ya shaida lamarin ya shaida wa BBCcewa ya ga gawa ta mutum takwas a wani ƙauye.
An bayyana cewa ƴan bindigan sun soma kai harin tun daga ranar Talata da dare har zuwa Laraba inda ƴan bindigan suka ci gaba da kutsawa daga wanan ƙauye zuwa wancan.
Har zuwa yanzu ƴan sanda da sauran hukumomi a Jihar Zamfara ba su ce komai ba dangane da wannan hari.
Majiyoyi da dama sun bayar da adadi daban-daban na waɗanda aka kashe, amma kafofin watsa labarai na Najeriya sun ruwaito cewa akwai alamun cewa ƴan bindigan suna gudun hijira zuwa yammacin Zamfara inda suke guduwa daga farmakin da sojoji suke kai musu.
Rahotanni sun bayyana cewa akwai mayaƙan sa kai da dama da aka kashe a lokacin da suka je kai ɗauki domin daƙile hare-haren ƴan bindigan.
Rahotanni sun bayyana cewa ɗaruruwan mazauna yankunan da lamarin ya shafa na gudun hijira zuwa garin Anka.
Ƙauyuka da garuruwa da dama a Jihar Zamfara na fuskantar barazana da hare-hare daga ƴan bindiga. Gwamnati ta bayyana cewa an tura dubban jami'an tsaro domin yaƙar waɗannan ƴan bindigan.
A halin yanzu dai gwamnatin Najeriyar ta ayyana ƴan bindiga da ɓarayin daji a matsayin ƴan ta'adda.
Ko a bara, sai da gwamnati ta rufe layukan sadarwa a Jihar Zamfara da wasu maƙwaftanta da kuma kafa ƙungiyoyin sa kai, sai dai zuwa yanzu da alamu kwaliyya ba ta biya kuɗin sabulu ba ganin cewa matakan da aka ɗauka ba su kawo ƙarshen waɗannan hare-haren ba.











