Sarkakiya uku da ke tattare da yi wa mutum dashen zuciyar alade

Dashen zuciyar alade

Asalin hoton, UMSOM

Bayanan hoto, An yi irin wannan aiki na farko ne a Baltomore
    • Marubuci, Daga Jack Hunter
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

Wani mutum dan kasar Amurka ya zama mutum na farko a duniya da aka dasa wa zuciyar wani alade da aka gyara ta hanyar ƙwayoyin halitta.

David Bennett, mai shekaru 57, wanda a baya likitocin suka ce ba shi da lafiya sosai, har ya fara samun lafiya kwanaki uku bayan aikin.

Mutane da yawa suna yaba aikin tiyatar a matsayin wani ci gaba a fannin likitanci wanda zai iya rage lokacin dasawa da kuma canza rayuwar marasa lafiya a duniya. Amma wasu suna tambayar ko tsarin da ake bi wajen yin aikin zai iya zama wanda ya kamata.

Sun yi nuni da yiwuwar take hakkin dabbobi da kuma yiwuwar tabo wani bangaren jiki da hakan ka iya zama mai hadari.

Don haka muhawa a kan wannan batu ta kaure.

Haɗarin aikin

Wannan tiyata ce ta gwaji, kuma tana kawo babban haɗari ga majiyyaci. Sannan ko da an yi nasarar yin dashen jikin mutum na iya karɓar zuciyar ya yi aiki da ita.

Likitoci sun yi ta ƙoƙarin fara wannan aiki na xenotransplantation na dashen wasu sassan gabobin jikin dabbobi da dan adam duk da wasu lokutan akan yi nasara wasu lokutan kuma a gaza samun nasa.

A shekara ta 1984, likitoci a California sun yi ƙoƙari su ceci rayuwar wata yarinya ta hanyar dasa mata zuciyar wani gwaggon biri, daga baya ta rasa ranta bayan kwanaki 21.

Duk da yake irin wannan jiyya na da matukar haɗari, wasu masana ilimin likitanci sun ce ya kamata a rika yi wa jama';a idan sun amince.

"Ba za ku taba sanin ko mutum zai mutu ba har sai an gama aiki, ba abun da ba kasada a cikinsa " in ji Farfesa Julian Savulescu, wani malami a Jami'ar Oxford.

Ya kara da cewa "Muddin mutum ya fahimci cikakken hadarin da ke tattare da shi, ina ganin ya kamata mutane su amince da wannan aiki."

Farfesa Savulescu ya ce yana da muhimmanci a ba su damar amfani da duk wani zabi da ake da shi.

Surgeon Bartley P Griffith with David Bennett in January

Asalin hoton, University of Maryland School of Medicine

Bayanan hoto, An ce David Bennett wanda ke hannun dama na ci gaba da samun lafiya bayan yi masa aikin

Farfesa Savulescu ya ce kafin kowacce tiyata, dole ne a yi gagarumin gwaji ga dabbar da za a ciri wani sashenta don tabbatar da cewa lafiyarta lau.

Sai dai Dr Christine Lau daga Jami'ar Maryland School of Medicine, wacce ke da hannu wajen tsara aikin da aka yi wa Mista Bennett, ta ce ba inda aka yanke a jikinsa lokacin da ake aikin.

"Mun shafe shekaru da yawa muna gwaje-gwaje, tare da ƙoƙarin ganin yadda za mu yi wannan aikin cikin nasara," kamar yadda ta shaida wa BBC.

Hakkin dabbobi

Jinyar da Mista Bennett ya yi ta kuma sake haifar da muhawara kan amfani da aladu wajen dashen dan Adam, wanda kungiyoyin kare hakkin dabbobi da dama ke adawa da shi.

Daya daga cikinsu, People for the Ethical Treatment of Animals (PETA), ta yi Allah wadai da dashen zuciyar alade na Mr Bennett da cewa: "An nuna rashin imani, da kuma almubazzaranci da dabbobin da ake da su".

"Dabbobi ba yasassu ba ne, ba shara ba ce, su ma rayayyu ne da suke da damar rayuwa cikin aminci ba tare da kowanne haɗari ba," in ji PETA.

Masu fafutuka sun ce ba dai-dai ba ne a canza ƙwayoyin halittar dabbobi domin su zama kamar mutane.

Masana kimiyya dai sun canza aƙalla ƙwayoyin halitta 10 na aladen da aka yi amfani da zuciyarsa wajen dashen da aka yi wa Mista Bennett don kada jikinsa ya ƙi karɓa.

Presentational white space

An cire zuciyar aladen ne a safiyar da za a yi tiyatar.

Wani kakakin kungiyar da ke taimaka wa dabbobin, wadda ke Burtaniya ya shaida wa BBC cewa kungiyar na adawa da yin amfani da dabbobin da aka kiwata na gidan gona domin amfani da sassan jikinsu a jikin bil'adama, a ko wane irin yanayi.

"Su kansu dabbobi suna da 'yancin yin rayuwa ba tare da ƙara musu wasu ƙwayoyin halittar da za su sanya su girma da wuri ba.

"Ga azabtar da su da ake da tashin hankalin da suke shiga yayin hakan, amma imaninsu shi ne kawai a kashe su a yi amfani da sassan jikinsu," in ji kungiyar.

Wasu kuma damuwarsu ita ce game da irin sauyin da ake samu a tare da aladun game da lafiyarsu.

Dr Katrien Devolder, wata masaniyar ƙwayoyin halitta a Jami'ar Oxord, ta ce "za mu iya amfani da irin wadannan aladun da aka jirkita kwayoyin halittarsu, idan za mu iya tabbatar da cewa ba za mu cutar da su ba, babu gaira babu dalili".

"Kiwon alade domin cin namansa ya zama matsala sama da amfani da shi domin ceton rayuka, amma hakan ba zai zama dalilin da zai sa mu hana su walwala ba," in ji ta.

Pig file photo

Asalin hoton, Getty Images

Addini

Wata fuskar da ake fama da wannan matsalar ita ce ta bangaren addinai da suke da dokoki masu tsauri a kan amfani da sassan jikin alade ga dan adam.

An zaɓi aladu domin gaɓoɓinsu sun fi kusa da na mutum, kuma suna da sauƙin kiwo da raino.

Amma yaya wannan zaɓi da aka yi wa alade ke shafar addinin Musulunci da na Yahudu, waɗanda ke da tsauraran dokoki a kan amfani da su?

Addinin Yahudawa ya hana su kiwo da kuma cin naman alade baki daya, don haka amfani da zuciyar alade ta ko wane ɓangare ya saɓawa ƙa'idojin addinin", a cewar Dr Moshe Freedman wanda ke aiki da MEGA.

"Tun da babban abin da addinin Yahudawa ya fada kenan, babbar damuwarsa shi ne ceton rayukan mutane, ko wanne irin Bayahude da yake fama da rashin lafiya zai iya karbar dashen wani bangare na jikin alade domin ceton rayuwasa," Rabbi Freedman ya shaida wa BBC.

A wurin addinin Musulunci, irin hukunci guda ne na umarnin amfani da sassan dabbobi domin ceton rayuwar dan adam.

Hukumar da ke tabbatar da hukunce-hukuncen addini ta Masar ta ce, an amince a yi amfani da zuciyar alade, "idan ana fargabar rayuwar dan adma za ta salwanta, domin idan wata gaɓa ta lalace haka rayuwarsa za ta ci gaba da ɓalɓalcewa".

Areas Savulesco ya ce idan mutum ya ƙi amincewa da a yi masa dashen zuciyar saboda dalilin addini ko al'ada, kamata ya yi kada a ba shi muhimmanci na cewa sai dai a dasa masa ta mutum dan uwansa.

"Wasu na cewa idan ka samu damar a yi maka dashen zuciya kada ka amsa wasu kuwa na cewa ka yi maza ka karɓa, amma waɗanda suke adawa da hakan zamu samu daidaitawa da su a nan gaba."