Austria: Likitan da aka ci shi tara kan yanke lafiyayyiyar ƙafar wani

A file photo shows surgeons at work

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An gano kuskuren da aka tafka ne a lokacin da aka je sauya masa bandeji

An ci tarar wata likitar fiɗa a Austriya sakamakon yin kuskuren yanke wa wani mara lafiya ƙafar da ba ita ce mai ciwo ba a farkon shekarar nan.

An yanke wa marar lafiyan ƙafar hagu maimakon ta dama, kuma ba a gane kuskuren da aka tafka ba sai bayan kwana biyu.

A ranar Laraba ne, kotun da ke garin Linz ta kama likitar mai shekara 43 da laifin tsananin sakaci tare da cin ta tarar fan 2,296.

Matar marar lafiyan, wacce ta rasu kafin wannan lokacin ta kai ƙarar kotu, ita ma an biya ta diyyar yuro 5,000.

Marar lafiyan ya je asibitin Freistadt ne a watan Mayun da ya gabata don a yanke masa ƙafa, amma sai likitar ta yanke lafiyayyiyar ƙafar maimakon mai ciwon, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

An gano kuskuren da aka tafka ne a lokacin da aka je sauya masa bandeji, sai aka ce masa dole sai an yanke ita ma ɗaya ƙafar.

A lokacin, lamarin ya faru ne "sakamakon wasu jerin abubuwa marasa daɗi da suka faru". Daraktan asibitin ya nemi afuwa a wani tarin manema labarai.

A kotun kuwa, likitar ta ce an smau kura-kurai a wajen bayar da umarni a ɗakin tiyatar.

Da aka tambaye ta kan ko mene ne dalilin da ya sa ta sanya alamar cewa ƙafar dama za a yanke ba ta hagu ba, sai ta ce: "Ni ma ban sani ba."

Tun bayan faruwar lamarin, ta koma wani asibitin. An soke rabin tarar da aka sanya mata.

Ba a faye samun irin waɗannan lamurran ba amma a baya an sha samu.

A shekarar 1995, wani likita a Amurka yana tsaka da tiyata sai ya gano cewa yana ƙoƙarin yanke ƙafar da ba ita ce mai ciwo ba ta wani mai fama da ciwon suga.

Ala tilas ya ci ga da yanke ƙafar tun da har ya riga ya zaga tsakanin tsoka ya yi nisa.