A karon farko an samu ɓullar nau'in cutar korona na Omicron a Najeriya

Asalin hoton, Matthew Horwood
Hukumar da ke dakile cutuka masu yaduwa ta Najeriya NCDC, ta tabbatar da samun bullar sabon na'uin cutar korona na Omicron a kasar. a karon farko tun bayan gano cutar mako guda da ya gabata.
Hukumar ta NCDC a shafinta na intanet ta ce mutanen sun je kasar Afrika ta Kudu, inda aka fara gano cutar.
Wannan dai na zuwa a dai-dai lokacin da kasar ke aiwatar da dokar hana ma'aikatan gwamnati wadanda ba a yi wa allurar riga-kafin korona ba shiga gine-ginen gwamnati.
A cikin wata sanarwar NCDC ta fitar a shafinta na sada zumunta ta ce wadanda suka harbu da sabon nau'in cutar korona na Omicron suna cikin matafiyan da suka dawo daga kasar Afrika ta Kudu a makon da muke ciki.
Sanarwar ta kuma ce duk da cewa mutanen na dauke ƙwayar da cutar amma ba su fara nuna almaun kamuwa da cutar ba, amma an wuce da su asibiti inda suke samun kulawar da ta kamata.
Ta kuma ce an soma neman mutanen da suka yi mu'amala da su.
Hukumar ta NCDC ta yi kira ga ƴan Njeriya da su tabbatar sun kiyaye dokokin yaƙi da cutar domin hana sake samuwar ɓullar annobar korona karo na hudu.
A farkon makon da muke ciki ne aka bayyana ɓullar sabon nau'in cutar ta Omicron a kasar Afrika ta Kudu, abin da ya wasu kasashe irin su Birtaniya da Amurka ɗaukar matakin hana tafiye-tafiye zuwa kasashen da ke kudancin Afrika.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ɗora alhakin ɓullar sabon nau'in cutar a kan rashin dadaito wajen rarraba alluran rigakafi.
Ta kuma yi gargadin cewa sabon nau'in cutar zai iya haifar da matsaloli a yankuna daban-daban na duniya.











