Narendra Modi: Firaiministan India ya janye dokokin noma da suka jawo ce-ce-ku-ce bayan shekara guda ana zanga-zanga

.

Asalin hoton, Getty Images

Firaiministan Indiya Narendra Modi ya sanar da batun soke dokoki uku da suka shafi noma waɗanda aka shafe shekara ana taƙaddama a kansu.

Dubban manoma ne suka yada zango a kan iyakar Delhi tun Nuwambar bara kuma gwammai daga cikinsu sun rasu sakamakon zafi da sanyi da kuma annobar korona.

Manoman sun ce dokar za ta ba wasu masu zaman kansu damar su shigo harkar noman kuma hakan zai iya kawo cikas ga ribar da suke samu.

Sanarwar da firaiministan ya fitar a ranar Juma'a mai ban mamaki tamkar an yi amai ne an lashe ganin cewa gwamnatin ƙasar ba ta fito da wasu tsare-tsare ba na tattaunawa da manoman a cikin yan watannin nan.

Haka kuma ministocin Mista Modi sun yi ta dagewa kan cewa wannan tsarin yana da kyau ga manoma kuma babu amfanin yanye dokokin.

Ƙungiyoyin manoma na kallon wannan mataki a matsayin babbar nasara. Sai dai masana na ganin cewa zaɓen jihohin da za a yi a Punjab da Uttar Pradesh ne ya sa aka soke dokar ganin cewa akwai manoma dayawa daga wurin.

Sanarwar da aka yi a safiyar Juma'a na zuwa ne a ranar da masu bin addinin Sikh - waɗanda su ke da rinjaye a Punjab - ke murnar zagayowar ranar haihuwar Guru Nanak wanda shi ne ya ƙirƙiro addinin Sikh.

Me dokokin suka tanada?

Duka dokokin sun kawo sauyi a ɓangaren sayar da amfanin gona da farashinsu da yadda za a ajiye su - inda ake ganin sabbin dokokin na barazana ga tsoffin dokokin da suka kare manoman Indiya na tsawon shekaru.

Daga cikin manyan sauye-sauyen akwai batun da ake cewa manoman za su iya sayar da kayayyakinsu ne kaɗai a farashin da aka ƙayyade ga yan kasuwa masu zaman kansu - da suka haɗa da masu sayen kayan gona da manyan shaguna da kuma masu sayar da kayayyaki ta intanet.

Akasarin manoman Indiya na sayar da kayayyakinsu ne ga kasuwannin dillalai da gwamnati ke da iko a kansu.

.

Asalin hoton, Reuters

Dokokin za su bayar da dama ga ƴan kasuwa masu zaman kansu su ɓoye kayayyaki kamar su shinkafa da alkama domin su sayar a gaba, wanda a baya waɗanda gwamnati ta amince mawa ne kaɗai za su iya haka.

Irin waɗannan sauye-sauyen, aƙalla a rubuce kan takarda zai bai wa manoma damar sayar da kayayyakin su a kasuwannin yankuna. Sai dai masu zanga-zangar sun bayyana cewa waɗannan dokokin za su sanyaya gwiwar manoma da kuma barin ƴan kasuwa masu zaman kansu su fitar da farashinsu da kuma iko da manoman.

Sun ce kasuwannin yankunan da suke da su ne ke taimaka wa manoman, waɗanda su ke taimaka musu su ci gaba da rayuwa.

Sun bayyana cewa dokokin Indiya da suka shafi sayar da kayayyakin gona sun taimaki manoma daga ƴan kasuwa na tsawon shekaru kuma babu amfanin sauya dokokin.

Sai dai gwamnatin ƙasar ta kafe kan cewa lokaci ya yi da ya kamata a ci riba da noma ko ma ga ƙananan manoma kuma sabbin dokokin da aka kawo za su tabbatar da hakan.

.

Mista Chaudhary na daga cikin ɗaruruwan manoma waɗanda suke yajin aiki a kan iyakar Delhi da Ghazipur sama da shekara guda.

Rakesh Tikait ne ya yi magana a madadinsa, wanda shi ma wani sannanen manomi ne wanda ya ce za su janye yajin aikin ne kaɗai idan an soke dokokin a lokacin hunturu a majalisa.

Wannan sanarwar ta dugunzuma masu sa ido kan harkokin siyasa a kuma waɗanda suke adawa da kuma goyon bayan waɗannan dokoki - mutane da dama sun wallafa saƙonni a shafukan Twitter inda suka ce wannan babbar nasarar ce ga manoma.

Sai dai wasu shugabannin manoma da kuma masu fashin baƙi kan tattalin arziƙi waɗanda suka hangi alfanun da ke cikin dokokin sun nuna rashin jin daɗinsu kan soke dokokin.

Anil Ghanwat, wanda shi ne shugaban ƙungiyar manoma a yammacin Indiya, ya bayanna cewa matakin abin takaici ne kuma siyasa ce ta jawo hakan.

Jam'iyyun adawa sun yi maraba da wannan matakin inda shugaban jam'iyar Congress Party, Rahul Gandhi ya kira wannan lamari da "nasara kan rashin adalci. Haka ma Babban ministan Yammacin Bengal, Mamata Banerjee ta je shafukan sada zumunta inda ta jinjina wa manoma.

Mambobin Jam'iyyar BJP mai mulki a ƙasar sun bayyana cewa matakin da aka ɗauka na dakatar da dokokin ba shi da wata alaƙa da zaɓe mai zuwa kuma an ɗauki matakin ne domin kawo ƙarshen zanga-zangar da ake yi. Haka kuma ba su bayyana ko akwai niyyar dawo da dokokin a nan gaba ba.

Presentational grey line
Analysis box by Soutik Biswas, India online correspondent

Matakin da gwamnatin Narendra Modi ta ɗauka na soke waɗannan dokoki, ana ganin cewa wani mataki ne da dabara ce a siyasance kuma tamkar gwamnatin ta yarda cewa ta yi azarɓaɓi ne wajen yin dokar.

Waɗannan dokokin sun jawo zanga-zanga a jihohin Punjab da Uttar Pradesh haka kuma sun kasance babban ƙalubale ga Modi. Sun tattara manoma da ƙungiyoyi masu zaman kansu a mabiya addinin Sikh mai rinjaye a Punjab da kuma bazuwa a yankunan Uttar Pradesh, jihohin da za a gudanar da zaɓe ba da daɗewa ba.

Jam'iyyar BJP, wadda ba ta taɓa tsammanin za ta fuskanci wannan matsala ba, na ta ƙoƙarin shawo kan mabiya addinin Sikh. Kusan duka tarurrukan da jam'iyyar ta yi a watan nan an gudanar da su ne domin kwnatar da hankalin mabiya addinin: ta hanyar ƙara kasafin kuɗi noma da kuma farashin amfanin gona, da sake buɗe ɗaya daga cikin manyan wuraren tarihi na mabiya addinin Sikh a Pakistan da kuma ƙaddamar da sabon bincike kan waɗanda suke da hannu a zanga-zangar ƙin jinin mabiya addini Sikh da aka yi a 1984.

Gwamnatin ƙasar tana fargabar ƙara tara maƙiya daga bangaren ƴan Sikh kan waɗannan dokoki.

Ta hanyar soke waɗannan dokoki, Mista Modi na da burin sake samun amincewar manoma musamman mabiya addinin Sikh. Haka kuma matakin zai ƙara jawowa Jam'iyyar BJP a zaɓe mai zuwa.

Ga waɗanda suka goyi bayan wannan doka, hakan babban darasi ne da ke nuna cewa tattalin arziƙi mai kyau a wani lokaci ya zai zama siyasa ga manoma.

Presentational grey line

Me ya jawo aka soke wannan doka?

Ƙungiyar Samyukta Kisan Morcha, wadda ƙungiya ce da ke da manoma 40, ta ƙi yarda ta janye yajin aikinta duk da roƙon da gwamnati ke yi na dakatar da zanga-zangar su.

Manoman sun ci gaba da toshe hanyoyi da ke zuwa Delhi a lokacin hunturu da bazara har a lokacin da ake tsaka da fama da matsananciyar annobar korona . Sun ta kiran a yi yajin aiki a faɗin ƙasar haka kuma gwammai daga cikinsu sun mutu.

Tun a farko dai gwamnatin ƙasar ta soma tattaunawa da su da kuma ƙoƙarin amfani da dokar ta wucin gadi na shekara biyu. Amma bayan da manoman suka yi watsi da hakan, hukumomin sai suka janye kudirin nasu inda suka ce bari su zura ido su ga ƙarshen yajin aikin manoman.

Manoma

Asalin hoton, Reuters

Sai dai abubuwa biyu sun sauya lamarin a watannin da suka gabata.

Na farko, ana zargin ɗan ministan tarayyar ƙasar da kutsa motarsa cikin masu zanga-zangar a Lakhimpur da ke Uttar Pradesh a watan Oktoba Ya musanta zargin da ake yi masa amma an kama shi. Mutum takwas ciki har da manoma biyu da ɗan jarida suka mutu a lamarin wanda ya jawo ɓacin ran jama'a a faɗin ƙasar.

Na biyu kuma Jam'iyar BJP na ƙoƙarin yaƙi da manyan jam'iyyun adawa na yankuna a zaɓe mai zuwa da za a yi a Punjab da Uttar Pradesh haka kuma ana ganin cewa manoma waɗanda suke cikin ɓacin rai za su iya jawo cikas ga Jam'iyyar BJP a zaɓen da ke tafe

Presentational grey line