Matar da ta haifi tagwaye mata shekara biyu cif da mutuwar 'ya'yanta mata biyu

Asalin hoton, PADMASRI HOSPITAL
Gidan Bhagyalakshmi yana garin Visakhapatnam, inda take yawan samun baƙi, maƙwabta da 'yan jarida.
Bhagyalakshmi ta mamaye kanun labarai bayan da ta haifi tagwaye mata.
Bhagyalakshmi ta ce "Na tabbata na sake haihuwar 'ya'yana ne. Idan ba haka ba, me ya sa na haife su rana ɗaya sak da ranar da 'ya'yana mata biyu suka mutu?"
Bhagyalakshmi ta haifi 'yan mata tagwaye a ranar 15 ga watan Satumba. Wato shekara biyu cif bayan mutuwar ƴaƴanta mata biyu a hatsarin jirgin ruwa ranar 15 ga Satumban 2019.
Shekarar ƴaƴanta uku da rabi a lokacin da suka rasun. Wasu daga cikin surukan Bhagyalakshmi da wasu danginta ma sun rasa rayukansu a hadarin.
"Abin da ya sa na kaɗu da lamarin shi ne ganin cewa na haifi 'yan biyun nawa da ƙarfe 8 na dare, wanda a daidai irin wannan lokacin ne na ji labarin mutuwar ya'yana a ranar 15 ga Satumban 2019," kamar yadda ta shaida wa BBC.

Asalin hoton, BHAGYALAKSHMI
'An karɓi addu'o'ina'
Iyalan na fatan haihuwar 'yan biyun ya taimaka musu wajen farfaɗowa daga rashin' ya'yansu mata da suka yi.
Bhagyalakshmi ta ce, "Jikina ya ba ni cewa Allah ya amshi addu'ata kuma ya mayar mini da 'ya'yana."
Iyayensu sun kasance talakawa sosai kuma an yi musu auren kafin su kai shekarun aure da shari'a ta gindaya.
Mijinta yana sana'ar yin gorar ruwa ta tangaran, amma a halin yanzu ita da mijinta sun mayar da hankali kan renon 'yan biyun nasu.

Ta yaya hatsarin ya faru?
'Yaƴan Bhagyalakshmi sun rasu a ranar 15 ga Satumban 2019 a hanyarsu ta zuwa wani taron ibada a Bhadrachalam.
'Ya'yan nasu sun tafi tare da kakanninsu da sauran dangi yayin da iyayen suka tsaya a gida.
A hannu guda kuma Bhagyalakshmi ta gano cewa jirgin ruwan ya nutse sai ta fara addu'a.
"Allah ya amsa addu'ata. Duniyata ta yi duhu. Na kadu sosai.
"Lamarin na da matuƙar ciwo. Mun rasa 'yan gidanmu tara a hatsari. Ta yaya za ka jure? "
Bhagyalakshmi ba ta iya samun wani taimako daga dangi ba saboda kusan kowa a dangin na cikin kaɗuwa ana cikin.
"Na daina cin abinci. Ko yaushe ina cikin tunaninsu. A duk lokacin da na rufe idanuna, sai na tuna dangina da' ya'yana.
Na kasance cikin shiru da kaɗuwa a gidana."
Dangina sun koma nakin ayyukansu na yau da kullum.

Asalin hoton, BHAGYALAKSHMI
Taimako
Bhagyalakshmi ta samu matsalar toshewar bututun mahaifa bayan haihuwar 'yarta ta biyu. A lokacin an zaci ba za ta sake haihuwa ba.
Surukan Bhagyalakshmi sun shawarci ma'auratan da su ga likita. Ta ga Dakta Padmasambhava.
Likitan ya gaya mata cewa fasahar IVF na iya taimaka mata.
"Ina iya tuna halin baƙin cikin da Bhagyalakshmi ta shiga," a cewar Dakta Padmasambhava.
"Bhagyalakshmi na da sauran ƙuruciya kuma na gamsu cewa za ta iya sake haihuwa ta hanyar IVF."

Asalin hoton, BHAGYALAKSHMI
Ma'auratan sun sami ƙwarin gwiwa sosai daga waɗannan kalmomi na Dakta Padmasari.
Ko da yake albashin mijin Bhagyalakshmi ba wani mai yawa ba ne, amma duk da haka ya samu damar biyan kudin aikin.
A cewar Padmasari, an fara bin matakin aikin a watan Fabrairu kuma Bhagyalakshmi ta sami juna biyu bayan wata daya.
Rage lokacin haihuwa
Bhagyalakshmi ta fuskanci matsalar ci gaba da ganin likita a lokacin da take renon cikin sakamakon yaduwar annobar cutar korona kar na biyu. A matsayinta na uwa dole ta kasance a gida a wannan lokacin.
"An sa ran zan haihu a ranar 20 ga Oktoba, amma a ranar 15 ga Satumba na fara naƙuda kuma zuwa tsakar rana yanayin ya tsananta," in ji ta.

Asalin hoton, BHAGYALAKSHMI
Lokacin da aka kai ta asibiti, likitan ya damu da lafiyar 'yan biyun da ke cikinta waɗanda ba su kai lokacin haihuwa ba. Duk da haka sai ya yi mata gagarumar tiyata.
Bhagyalakshmi ta yi farin cikin ganin 'ya'yanta mata biyu.
"Ban san su duka 'yan mata ba ne. Abin ba a hannuna yake ba. Shin wannan ba abin mamaki ba ne na rasa' ya'ya mata biyu kuma na sake samun wasu biyun duk a irin rana ɗaya?"
Iyalin sun koma gida tare da 'yan biyun. Sai dai Likitan ya ce, rashin nauyin 'yan biyu abin damuwa ne.

Asalin hoton, PADMASRI HOSPITALS
Bhagyalakshmi ta ce tagwayen kamarsu ɗaya da ya'yanta matan da suka rasu.
"Na adana tufafin 'ya'yan nawa da suka mutu da kayan ƙawarsu da sauran kayan ado. A yanzu zan yi amfani da su ga ƴan biyun nawa.
Bhagyalakshmi ta sake samun fitilu masu ƙawata mata gida.
Iyayen sun mayar da sunayen ƴaƴan da suka rasu ga ƴan biyun. Anasaka musu suna Gita da Ananya.
"Ina kallon su cikin farin ciki da mamaki da sha'awa. Ina fatan na ga girmansu. Ina so in ga suna tafiya, suna magana, suna wasa da karatu.
"Ba ni da kalmomin da zan nuna farin cikina."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Google YouTube suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Google YouTube da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a YouTube











