Ƙayatattun hotunan Afrika: Daga 12 zuwa18 ga watan Nuwambar 2021

Wasu daga cikin zaɓaɓɓun hotuna daga Afrika da na ƴan Afrika daga wasu sassan duniya

Short presentational grey line
Wani kenan da ke sanye da kayayyakin al'ada a babban filin wasa na Guinea Bissau yayin da ake murnar zagayowar ranar samun ƴancin kai a ranar Talata

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani mutum da ke sanye da kayayyakin al'ada a babban filin wasa na Guinea-Bissau yayin da ake murnar zagayowar ranar samun ƴancin kai a ranar Talata
Wasu daga cikin masu kaɗa ganga na sojin ƙasar Guinea-Bissau yayin da suke sararawa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu daga cikin masu kaɗa ganga na sojin ƙasar Guinea-Bissau yayin da suke sararawa
Daga cikin shagulgulan da ake yi a kan titi a Bissau babban birnin ƙasar, mata ne ke murnar buɗe wani titi da aka saka masa sunan Shugaban Senegal, Macky Sall.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Daga cikin shagulgulan da ake yi a kan titi a Bissau babban birnin ƙasar, mata ne ke murnar buɗe wani titi da aka saka masa sunan Shugaban Senegal, Macky Sall.
Masu zanga-zangar adawa da juyin mulki a Khartoum babban birnin Sudan kenan ke taimakawa domin ɗaukar abokin gwagwarmayarsu da ya ji ciwo a ranar Asabar. Daga baya a cikin makon jami'an tsaron ƙasar sun yi sanadin mutuwar aƙalla masu zanga-zangar 15.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Masu zanga-zangar adawa da juyin mulki a Khartoum babban birnin Sudan kenan ke taimakawa domin ɗaukar abokin gwagwarmayarsu da ya ji ciwo a ranar Asabar. Daga baya a cikin makon jami'an tsaron ƙasar sun yi sanadin mutuwar aƙalla masu zanga-zangar 15.
Masu zanga-zanga kenan da suka fito a Tunis babban birnin ƙasar Tunisia a ranar Lahadi inda suke ƙorafi kan Shugaba Kais Saied wanda suke zargi da yin juyin mulki bayan ya kori firaiminista da kum dakatar da majalisar ƙasar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu zanga-zanga kenan da suka fito a Tunis babban birnin ƙasar Tunisia a ranar Lahadi inda suke ƙorafi kan Shugaba Kais Saied wanda suke zargi da yin juyin mulki bayan ya kori firaiminista da kuma dakatar da majalisar ƙasar.
Jami'in sashen ƴan sanda masu kwance bam kenan a Kampala babban birnin Uganda ke dubawa ko akwai wani abu kan titi da ba a yarda da shi bayan harin ƙunar baƙin waken da aka kai a ranar Talata wanda mutum shida suka mutu ciki har da masu tayar da bam ɗin.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Jami'in sashen ƴan sanda masu kwance bam kenan a Kampala babban birnin Uganda sanye da garkuwa yayin da yake dubawa ko akwai wani abu kan titi da ba a yarda da shi ba bayan harin ƙunar baƙin waken da aka kai a ranar Talata wanda mutum shida suka mutu ciki har da masu tayar da bam ɗin.
Wani mutum kenan bayan ya fito daga wasan ruwan da ya yi a cikin teku a ranar asabar a Monrovia babbn birnin Liberia.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani mutum kenan bayan ya fito daga wasan ruwan da ya yi a cikin teku a ranar asabar a Monrovia babbn birnin Liberia.
A Guinea-Bissau, wani yaro ne mai shekara 11 ya saka kayansa na gargajiya masu kyau a ranar Lahadi domin yi masa kaciya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A Guinea-Bissau, wani yaro ne mai shekara 11 ya saka kayansa na gargajiya masu kyau a ranar Lahadi domin yi masa kaciya
Wani ɗan dambe ɗan asalin Congo Marc Diakiese a yayin da yake shirin fuskantar abokin karawarsa na Brazil Rafael Alves a Las Vegas a daren Asabar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani ɗan dambe ɗan asalin Congo Marc Diakiese a yayin da yake shirin fuskantar abokin karawarsa na Brazil Rafael Alves a Las Vegas a daren Asabar.
Wani mawaƙi kenan Jelili Atiku a yayin da yake gaisawa da jama'a a Legas babbar cibiyar kasuwanci ta Najeriya a yayin wani biki a ranar Talata.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wani mawaƙi kenan Jelili Atiku a yayin da yake gaisawa da jama'a a Legas babbar cibiyar kasuwanci ta Najeriya a yayin wani biki a ranar Talata.
A ranar Litinin, likitoci ne ke tantance ƴan gudun hijira a filin jirgin sama na Bangui babban birnin Jamhuriyyar Tsakiyar Afrika waɗanda aka dawo da su daga Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Litinin, likitoci ne ke tantance ƴan gudun hijira a filin jirgin sama na Bangui babban birnin Jamhuriyyar Tsakiyar Afrika waɗanda aka dawo da su daga Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo.
A caretaker uses a leaf blower between two new bronze sculptures by South African artist Nandipha Mntambo at the Circa Gallery as part of the Keyes Art Mile in Johannesburg, South Africa, 18 November 2021.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A caretaker cleans up the area in the South African city of Johannesburg on Thursday where two new works by artist Nandipha Mntambo have gone on display.
A yayin da ake shirin Ranar Ɓanɗaki Ta Duniya, wani mai ɗaukar hoto ne yake duba wani banɗaki a yammacin birnin Monrovia da ke Liberia.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A yayin da ake shirin Ranar Ɓanɗaki Ta Duniya, wani mai ɗaukar hoto ne yake duba wani banɗaki a yammacin birnin Monrovia da ke Liberia.
Yadda aka yi baje kolin sabbin ƴaƴan zaitun a birnin Tebourba na Tunisia a ranar Laraba a yayin da ake ci gaba da girbin ƴaƴan zaitun a ƙasar.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Yadda aka yi baje kolin sabbin ƴaƴan zaitun a birnin Tebourba na Tunisia a ranar Laraba a yayin da ake ci gaba da girbin ƴaƴan zaitun a ƙasar.

Duka waɗannan hotunan suna da haƙƙin mallaka