Saif al-Islam Gaddafi: Tarihin dan Gaddafi da ke takarar shugabancin Libya

Saif al-Islam

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An tsare Said al-Islam Gaddafi kusan shekara shida bayan kama shi a 2011

Ɗan marigayi Mu'ammar Gaddafi mai suna Saif al-Islam ya yi rajistar tsayawa takarar shugaban ƙasar Libya a zaɓen watan Disamba mai zuwa, a cewar hukumar zaɓen ƙasar.

"Saif al-Islam ya miƙa rajistar takararsa ta shugabancin ƙasa zuwa ga hukumar zaɓe a birnin Sebha," in ji hukumar.

Ta ce ya cika "dukkan ƙa'idojin da ake buƙata" sannan kuma an ba shi katin jefa ƙuri'a na gundumar Sebha.

Wannan ne karon farko da za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a matakin gama-gari a Libya ranar 24 ga Disamba bayan Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta shiga tsakanin ɓangarorin da ke yaƙar juna a ƙasar.

A shekarar 2017 ne aka saki Saif al-Islam Gaddafi bayan ya kwashe shekaru shida a tsare.

Kamun da aka yi masa a kudancin Libya a watan Nuwambar 2011, bayan ya kwashe watanni uku yana buya kuma makonni kadan bayan kisan mahaifinsa, ya kawo karshen hasashen da aka yi cewa shi ne zai gaji Kanar Muammar Gaddafi.

Duk da cewa bai rike wani mukami ba a gwamnatin Libya, ana yi masa kallon wani mai karfin fada-a ji a gwamnatin mahaifinsa wanda ya jagoranci kasar tun shekarar 1969. Kuma shi ne ake kyautata zaton zai zama magajin mahaifinsa.

Sai dai bayan sauran iyalan gidansu sun bar kasar, ko an kashe su, Saif ya kwashe shekara shida a birnin Zintan, inda wata kotu a birnin Tripoli ta yanke masa hukuncin kisa a wancan lokacin.

A shekarar 2011 ne kotun hukunta manyan laifuka ta duniya wato ICC ta ayyana nemansa ruwa-a-jallo, saboda zarginsa da aikata laifin cin zarafin dan adam da kuma kisan masu zanga-zanga.

A matsayinsa na shugaban gidauniyar iyalan Gaddafi, an zarge shi da karkatar da kudin asusun hukumar zuba jari ta kasar (LIA) zuwa aljihunsa, sai dai ya musanta wadannan zarge-zarge. Saif al-Islam na da makudan kudade, wanda ya yi amfani da su wajen gina dangantaka tsakaninsa da kasashen yamma.

Saif Gaddafi, son of the Libyan leader, in front of one of his paintings called Challenged

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, A baya Kasashen Yamma suna kallonsa a matsayin mai son kawo sauyi amma daga bisani kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta duniya ta soma nemansa ruwa a jallo.

Alaka da kasashen Yamma

An haifi Saif al-Islam Gaddafi a shekarar 1972, kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen yaukaka dangantaka tsakanin Libya da kasashen Yamma tsakanin 2000 zuwa 2011 lokacin da aka yi wa mahaifinsa bore.

A matsayinsa na shugaban gidaunyar iyalan Gaddafi, an yi zargi ya kashe biliyoyin dalar da ke cikinta - ko da yake ya sdah musanta hakan.

Ya taka rawa a tattaunawar sulhun da aka yi wacce ta sanya mahaifinsa yi watsi da shirinsa na makamin Nukiliya, haka kuma daga baya ya taimaka wajen shiga tsakani domin sakin wasu likitoci 'yan kasar Bulgaria shida da aka zarga da yada cuta mai karya garkuwar jiki ga wasu yara a asibitin Libya.

Ya kuma taimaka wajen cimma yarjejeniyar biyan diyya ga iyalan wadanda aka kashe a harin bam din Lockerbie a shekarar 1988, da kuma na harin gidan rawar Berlin a shekarar 1986, da kuma wadanda harin jirgin saman UTA flight 772 ya rutsa da su a shekarar 1989.

Hakazalika, yana cikin tattaunawa mai cike da sarkakiyar da ta haifar da sakin wanda ake zargi da shi ne maharin bam na Lockerbie, Abdelbaset al-Megrahi, a shekarar 2009.

Muammar Gaddafi with Saif al-Islam, reviewing troops in 1989

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An kwashe shekaru ana kallon Saif a matsaytin wanda zai gaji mahaifinsa (wanda suke tare a cikin wannan hoton da aka dauka a 1989)

Bayan cimma wadannan yarjejeniyoyi, duniya ta dage wa kasar takunkumai da aka doro wa gwamnatin mahaifinsa ta bangaren tattalin arziki da siyasa, inda kasar ta samu wani gagarumin sauyi a wancan lokacin.

Libya ta fara harkokin fitar da manta, kuma ta amince ta takaita tururuwar da 'yan ci-rani ke yi ta kasar zuwa nahiyar Turai.

Mr Gaddafi yana da gida a London kuma yana da alaka da manyan 'yan siyasar Birtaniya da gidajen sarautar kasar. Sau biyu yana ganawa da Duke na York - na farko da fadar Buckingham, na biyu kuma na Tripoli.

Yayi fice wajen kiwon kuraye kuma yana son yin farauta - wani abu da Larabawa suke matukar kauna - kuma yana gwada yin fenti.

Gaddafi, wanda sunansa na farko yake nufin Takobi, ya sha musanta cewa yana neman gadar mahafinsa, yana mai cewa mulki "ba kamar gona ba ce da ake gada".

Saif al-Islam pictured in March 2011

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ya samu digirin digirgir daga Jam'iar London School of Economics a 2008

Yayi kira da a samu sauyin siyasa - wani batu da ya tabo a cikin kudin digirinsa na uku daga Jami'ar London School of Economics (LSE).

Lokacin da aka bayar da rahoton hannunsa wajen musguna wa masu zanga-zanga, daraktan LSE Howard Davies ya sauka daga mukaminsa bayan ya sha suka bisa karbar kyauta daga gidauniyar da Saif al-Islam Gaddafi yake shugabanta.

An nemi Jami'ar London ta gudanar da bincike kan sahihancin kudin digirin digirgir na Saif al-Islam Gaddafi, a yayin da ake zargin cewa ya saci bayanan ne - sai dai Jami'ar ta ki binciken tana mai cewa ya bayyana dukkan bayanan da ya samo a wasu wurare.

An kama Saif al-Islam ne ranar 19 ga watan Nuwambar shekarar 2011, wata daya bayan da dakarun 'yan tawaye suka halaka mahaifinsa a garinsa na Sirte.

'Yan tawayen sun yi ikirarin kama shi a watan Agustan 2011, lokacin da suke mazayawas zuwa Tripoli, amma daga bisani ya fito a wajen wani otal da ke babban birnin kasar, yana gaisawa da dandazon mutanen da ke goyon bayansa, kafin ya sake bacewa.

'Yan tawayen da suka kama shi a Zintan suna so a yi masa shari'a a birnin - ba a kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta duniya ba. Daga karshe dai, an yi masa shari'a ba tare da yana nan ba a shekarar 2015 a wata kotu da ke Tripoli.

"Ba na jin tsoron mutuwa amma idan kuka yanke min hukuncin kisa bayan wannan shari'ar ku sani cewa kashe ni kuka yi," a cewar Gaddafi kamar yadda lauyoyinsa suka ambato shi.