Makadan da ke taimaka wa tsofaffin almajirai a Senegal
Kungiyar 'yan rawar Sencirk, wani tsohon almajiri Modou Toure ne ya kafata, inda yake so ya rinka taimakawa almajirai irinsa kamar yadda rahotanni suka rawaito daga Dakar.

Asalin hoton, Annika Hammerschlag
An tura Mr Touré, makarantar allo a lokacin yana da shekara bakwai, a inda aka rinka azaftar da shi saboda baya karatun Al Qur'ani sosai.
Ya gudu inda ya tafi Dakar babban birnin kasar ya rinka rayuwa a titi tsawon shekaru kafin ya samu matsugunni. Wata rana, masu koyar da rawar lankwasa jiki daga Switzerland suka je birnin domin koya wa yara irin wannan lanƙwasa jiki kuma a nan ne Mr Toure ya ji yana da sha'awa.

Asalin hoton, Annika Hammerschlag

Ya samu horo a kan irin wannan rawa a Switzerland tsawon watanni uku, a nan ne ya gwanance har ya yi fice a duniya kafin daga bisani ya dawo Dakar ya kafa kungiyarsa mai suna Sencirk.
Mr Toure wanda yake shekara 31 a yanzu ya ce rawar lankwasa jiki ita ce rayuwarsa.

Asalin hoton, Annika Hammerschlag

Irin wannan rawa ta taimaka masa wajen mantawa da tsananin damuwar da yake da ita.
Sannan yin rawar ta kuma taimaka masa wajen samun karfin gwiwar taimakawa wasu kamar sa in ji sa.
Ya ce," Irin wannan rawar tana bani karfin gwiwa sannan tana taimaka mini wajen kawar da duk wata damuwata".
A kowace shekara, dubban matasa a Senegal da ma yara ana tura su birane daban-daban don su koyi karatun Al Qur'ani, to amma daga nan sai kaga sun buge da baran abinci ko kudi a kan tituna.
Idan har suka gaza samun abin da ya kamata su rinka baI wa malamansu, ko kuma suka aikata wani dan karamin laifi sai kaga an yi musu dukan tsiya sannan a saka musu ankwa.
Wasu daga cikinsu sun samu sun tsere, kamar Mr Toure bayan ya tsere sai ya samu mafaka.

Asalin hoton, Annika Hammerschlag

Daya daga cikin matasan da ke rawar lankwasa jiki da ba a sanya hotonsa anan ba, na da makamancin labari kamar na Mr Toure, in da shi ma ya gudu daga makarantar allo bayan ya sha bulalla da dauri saboda ya gaza yin karatu dai dai.
matashin mai shekara 14 ya ce yana son duk wani da ya jibanci rawar lankwasa jiki, tana matukar taimaka masa.
Ya ce, in har ya mallaki gida, to ko shakka babu zai rinka koyar da yara makaftansa rawar lankwasa jiki.
Ya ce yana fatan ya shiga kungiyar kungiyar Sencirk a matsayin daya daga cikin masu koyar da irin wannan rawar.

Asalin hoton, Annika Hammerschlag

Asalin hoton, Annika Hammerschlag
Ma'aikatan Mr Toure, kan gudanar da taron bita kyauta a wani gida da aka kebe ga yaran da ke gararanba a titi dama matan da ke neman mafaka domin taimaka musu.
Suna fada musu cewa za su daina gararanba a titi sannan su samu abin yi idan suka rungumi wannan rawar.

Asalin hoton, Annika Hammerschlag

Asalin hoton, Annika Hammerschlag

Asalin hoton, Annika Hammerschlag

Asalin hoton, Annika Hammerschlag

All pictures subject to copyright











