Zaɓen Anambra: IPOB ta ja da baya

Hukumar zaɓen Najeriya INEC ta ce komai ya kammala

Asalin hoton, Inec

Bayanan hoto, Hukumar zaɓen Najeriya INEC ta ce komai ya kammala

Ƙungiyar masu rajin kafa ƙasar Biafra ta IPOB ta lashe amanta, na alwasin hana gudanar da zaɓen gwamnan jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya da ake shirin gudanarwa ranar Asabar.

Ƙungiyar ƴan awaren ta bayyana sauya matsayin na ta ne a wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce ta janye umarnin da ta ba jama'a na zama a gida na tsawon mako guda tun daga ranar Alhamis.

Cikin wata zantawa da sashen Hausa na BBC, ƙanin jagoran ƙungiyar Nnamdi Kanu da yanzu haka ke hannun mahukunta wato Pnnce Emmanuel Kanu, ya ce sun ɗauki matakin ne sakamakon shawarwarin da jagororin yankin suka ba su, na su bari a gudanar da zaɓen cikin lumana.

''Duk wanda ke tunanin cewa mun yi hakan ne saboda wai muna shayin tarin jami'an tsaron da aka jibge to ya sani mafarki yake yi, dalilinmu shi ne mu masu girmama manya ne, kuma magabatanmu sun sa baki, tun daga malamai da sarakuna, sun ba mu tabbacin suna yin dukkan mai yiwuwa don ganin an sako Nnamdi Kanu, kuma muna ganin hakan a fili'' inji ƙanin Kanu ɗin.

Ya kara da cewa ''Mutane za su iya fita su zaɓi duk wanda suke so, wannan hakkinsu ne na Dimokraɗiyya, kuma wannan shi ke nuna cewa, kungiyar IPOB na nan kan tsarin dimokuradiyya'' a cewarsa.

Sojojin Najeriya

Asalin hoton, AFP

Sai dai tun kafin ƙungiyar ta fitar da wannan sanarwa hukumar zaɓen Najeriya wato INEC ta ce ta shirya tsaf, babu gudu ba ja da baya kan gudanar da zaɓen kamar yadda aka tsara.

Wata jami'ar hukumar Hajiya Zainab Aminu Abubakar ta bayyana cewa ''Mun kammala duk abubuwan da ya kamata mu yi gabanin zaɓe, dukkan kayan zaɓe sun isa ƙananan hukumomi, daga nan kuma za a raba su zuwa rumfunan kaɗa ƙuri'a, su ma ma'aikatan zaɓen an tura su inda za su yi aiki, babu wata matsala'' inji ta.

Wasu rahotanni daga jihar sun tabbatar wa BBC Hausa cewa an jibge tarin jami'an tsaro a jihar, kama daga kan sojoji da ƴan sanda da sauran takwarorinsu, domin ganin zaɓen da aka jima ana dako ya gudana lami lafiya.

A yanzu za a iya cewa, saura a jira a ga yadda zaben zai kaya, tun da da alama an soma shawo kan gagarumar matsalar tsaro da zaben na gwamnan jihar Anambra ke fuskanta, ga shi kuma hukumar zabe ta kammala shiri.