Sauya fasalin Nigeria tamkar samun kasar Biafra ne - Ohaneze

IPOB

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dubban matasa 'yan kabilar Igbo suna bin kungiyra IPOB mai fafatukar kafa kasar Biafra

Shugaban kungiyar 'yan kabilar Igbo ta Ohaneze Ngigbo, John Nwodo ya ce Najeriyar da aka sauya wa Fasali, tamkar Biafra ce.

A hirar da aka yi da shi a shirin Newsday na sashen Turanci na BBC, Mista Nwodo, wanda ya shaida yakin basasar Najeriya, ya ce bai kamata a sake tayar da maganar yakin ko kuma sunan Bifra ba.

Ya bayyana cewar sauya fasalin Najeriya shi ya fi dacewa da muradun 'yan kabilar Igbo na nan gaba maimakon fafatukar kafa kasar Biafra.

Ga fassarar hirar da aka yi da shi a shirin Newsday:

Bana tunanin ya kamata mu sake tayar da yakin (basasar Najeriya) kuma ko kuma maganar Bifara a yanzu.

Tambaya: Me kake nufi da a yanzu? IPOB ta ce Najeriya ba ta kiyaye hakkokin 'yan kabilar Igbo dake kudu maso gabashin Najeriya, kuma saboda haka suna son kasarsu. Shin baka yarda da haka bane ko kuma ka yarda?

Nwodo:Dukkanmu mun yarda da ginshikin lamarin. Inda muka yi sabani shi ne hanyar da za a bi (a dakile matsalar). Na yi imanin cewar in aka sauya fasalin Najeriya, tamkar an samar da Biafra ne.

A Najeriyar da aka sauya wa fasali, za su samu 'yancin kai na tattalin arziki da na siyasa a yankunansu kamar yadda muka samu a 1963.

Tambaya: Abin da kake so shine abin da ake kira cikakkiyar tarayya?

Nwodo: Wannan haka yake.

Tambaya: Amma ba kasa mai cin gashin kanta ba?

Nwodo:A'a.

Ta yaya za ka tinkari dubban matasan da ke gudanar da zanga-zangar goyon bayan IPOB da ke son kasa mai cin gashin kanta?

Nwodo: E, na ji haka a shekarar 1967. Na wuce irin wannan tunanin a yanzu, kuma na san abin da suke nema na da wuyar samu yanzu. Kuma na biyu,fafutukar Biafra din ba alheri ba ne a gare su nan gaba.

Idan kana son kasar Biafra mai cin gashin kanta, sai ka bi wadannan hanyoyin. Sai ka bi ta hanyar zaben raba gardama. Kundin tsarin mulkin Najeriya bai ba da damar zaben raba gardama ba.

Zan iya ba ka wasu misalai kadan da suka zamo hargitsi kuma har yanzu suna fama. A Sudan yawan kashe-kashe ya tilasta musu su bai wa Sudan ta Kudu 'yanci tun kafin a gudanar da zaben raba gardama.

A kasar Ethiopia da Eritria irin wannan lamarin ne ya faru. Kuma gabar da ke tsakanin bangarorin biyu na haddasa hasarar rayuka har yanzu a wadannan wuraren biyu.

A daya bangaren na Maroko da Kamaru kuma, har yanzu ba a san yadda za ta kaya ba.

Gaskiyar maganar ita ce bin daya daga cikin wadannan hanyoyin yana da wuyar gaske. Kuma in ka samu kudirin kan lamarin a kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ko kuma Majalisar Dinkin Duniya, za ka bukaci majalisar dokokin kasarmu ta amince da dokar.

Kuma bayan haka za ka bukaci a ware wa hukumar zaben kasarmu saboda ta samu ta shirya zabe. Wannan wani abu ne mai wuya.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da wasu jagorori a al'ummar Igbo ke nesanta kansu da ayyukan fafutukar kungiyar IPOB ba, ko a farkon wannan watan ma, gwamnonin yankin Igbo sun haramta IPOB.