Jemagen da ya lashe gasar tsuntsaye ta 2021 ta duniya

Long-tailed Bat

Asalin hoton, Ian Davidson-Watts

Bayanan hoto, Jemagen mai tsawon jela bai fi girman ɗan yatsa ba
Lokacin karatu: Minti 2

Wani ya lashe kyautar tsuntsu na shekara a New Zealand, abin da ya jawo cecekuce.

Jemagen mai tsawon jela ya yi nasarar ce a wata ƙuri'a da aka kaɗa ta intanet.

Waɗanda suka haɗa gasar sun saka jemagen ne, a matsayin ɗaya daga cikin dabbobin ƙasa 'yan asalin ƙasar New Zealand, domin fito da shi a matsayin halittun da ke fuskantar barazanar ƙarewa a bayan ƙasa.

Sai dai nasarar ta ɓata wa wasu rai, inda wasu ke cewa ƙasar ta "haukace".

Wasu masu ƙaunar dabbobi a dandalin Twitter sun fusata, suna kiran gasar da "shirme", ko kuma "maguɗi", da sauran kalaman da ba za a iya bayyanawa ba.

Wasu kuma na cewa nasara ce ga jemagu bayan sun daɗe suna fafatawa a gasar ba tarew da nasara ba.

Ƙungiyar Forest and Bird wadda ta shirya gasar, ta ce ba ta saka jemagen a cikin gasar ba don ta ɗaga darajarsu musamman a lokacin annobar korona.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Presentational white space

Gasar da ke zaɓo tsuntsun shekara ana shirya ta ne domin wayar da kai da kuma fitowa fili da dabbobin da ke fuskantar barazanar ƙrewa a New Zealand.

Cikin wani yunƙuri na kauce wa abin d aka saba yi a kimiyya, Forest and Bird ta yanke shawarar saka dabbobin dandariyar ƙasa a wannan shekarar a karon farko, suna masu cewa su ma sun fuskanci ƙalubale kamar sauran tsuntsaye.

Ana kiran jemagen pekapeka-tou-roa kuma bai fi girman ɗan yatsa ba. Ya doke wata aku maras tashi kafin ya yi nasara.

Jumillar fiye da mutum 56,700 ne suka kaɗa ƙuri'a a zaɓen yayin da jemagen ya samu fiye da 7,000, inda ita kuma akun ta samu 4,000 da ɗoriya bayan ta lashe gasar a shekarar da ta gabata.

Ba wannan ne karon farko da gasar ta haddasa cecekuce ba.

A 2019, an samu wasu ƙuri'u da aka kaɗa daga Rasha, abind da ake fargabar maguɗi.

Masu shirya gasar sun aminta cewa akwai yiwuwar masoya tsuntsaye ne suka jefa ƙuri'a daga Rashar, maimakon masu kutse da ke neman yin maguɗi.