Barcelona ta kori Koeman

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta kori kocinta Ronald Koeman.

Ya fara aiki da ƙungiyar ne watanni goma sha hudu kacal da suka gabata.

Maki goma sha takwas kawai ƙungiyar ta samu a wasanni goma da ta buga a gasar Laliga ta bana.

A halin da ake ciki ƙungiyar ce ta tara a gasar ta bana, abun da ke zaman wani babban ƙalubale da ya sa magoya bayanta a faɗin duniya ke sukar salon kocin na jagorancin ƙungiyar.

Cikin wata sanarwa da kulob ɗin ya fitar, ya ce shugabansa Joan Laporta ya sanar da Koeman ɗaukar wannan mataki bayan kashin da kungiyar ta sha a hannun Rayo Vallecano.

Ranar Talata tuɓaɓɓen kocin zai yi bankwana da ƙungiyar da ƴan wasanta a hukumance.