Real Madrid ta hau teburin La Liga duk da kasa cin Osasuna

Real Madrid ta tashi wasa da Osasuna 0-0 a karawar mako na 11 a gasar La Liga da suka fafata ranar Laraba a Santiago Bernabeu.

Da wannan sakamakon Real Madrid tana daga cikin kungiyoyi hudu da ke da maki 21 a mataki na daya da ya hada da Sevilla da Real Betis da kuma Real Sociedad.

Osasuna tana mataki na shida da maki 19 iri daya da na Rayo Vallecano, wadda ta ci Barcelona 1-0 ranar Laraba. Real Madrid tana da kwantan wasa.

Wannan shine karon farko da Osasuna ta samu maki a gidan Real Madrid tun bayan 2005 ta kuma kawo karshen wasa 11 ana doke ta.

Kungiyoyin biyu sun kara a kakar 2020/2021 a La Liga, inda suka tashi 0-0 a gidan Osasuna ranar 9 ga watan Janairun 2021.

A wasa na biyu kuwa Real Madrid ce ta yi nasara da ci 2-0 a gida ranar 1 ga watan Mayun 2021.

'Yan wasan da Carlo Ancelotti ya fuskanci Osasuna a Santiago Bernabeu.

'Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Courtois, Lunin, Fuidias.

Masu tsaron baya: Carvajal, E. Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Marcelo, Mendy.

Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Casemiro, Lucas V., Camavinga, Blanco.

Masu cin kwallaye: Hazard, Benzema, Asensio, Jović, Vini Jr., Rodrygo, Mariano.