Yariman Saudiyya ne ya ba da shawarar kashe Sarki Abdullah - Tsohon jami'i

Saudi Crown Prince Mohammed bin Salman gives a speech from his office in Riyadh, Saudi Arabia (23 October 2021)

Asalin hoton, Reuters

Wani tsohon jami'in leƙen asirin Saudiyya ya yi zargin cewa yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman ne ya bayar da shawarar "yin amfani da wani zobe mai guba" don kashe marigayi Sarki Abdullah.

A wata hira da tashar CBS, Saad al-Jabri ya ce Mohammed bin Salman ya shaida wa wani ɗan baffansa a shekarar 2014 cewa yana so ya aiwatar da hakan don bai wa mahaifinsa damar zama sarki.

An samu ruɗani da tashin hankali a cikin zuri'ar masarautar kan wanda zai gaji marigayin.

Sai dai gwamnatin Saudiyya ta ce Mista Jabri wani tsohon jami'i ne da aka kora wanda ya sha ƙirƙiro ƙarya.

IA cikin hirar tasa mai tsawon minti 60 a CBS Mr Jabri ya yi gargaɗi cewa Yarima Mohammed - shugaban je ka na yi kan Saudiyya kuma ɗan Sarki Salman - "mahaukaci ne, kuma makashi a Gabas ta Tsakiya, inda yake da dukkan abubuwan da ke zama barazana ga jama'arsa da Amurka da ma duniya baki ɗaya."

Ya yi zargin cewa a wani taro a 2014 yariman ya bai wa wani ɗan baffansa Yarima Mohammed bin Nayef shawara, wanda a lokacin shi ne ministan harkokin cikin gida cewa, zai iya kitsa kashe Sarki Abdullah.

Saudi Arabia's Prince Mohammed bin Salman (L) and Prince Muhammad bin Nayef (R) attend a ceremony in Riyadh (14 December 2016)

Asalin hoton, Anadolu Agency

Bayanan hoto, Mohammed bin Salman (daga hagu) shi ya maye gurbin Mohammed bin Nayef (na dama) a matsayin yarima mai jiran gado a 2017

"Ya shaida masa cewa: 'Ina so na kashe Sarki King Abdullah. Na samo wani zobe mai guba daga Rasha. Musabaha zan yi da shi kawai shi kenan tasa ta ƙare," kamar yadda Mr Jabri ya ce.

"Ko ma cika baki kawai yake yi dai... ya faɗa kuma mu mun ɗauki abin da gaske."

Ya ce an sasanta maganar a majalisar sarki. Amma ya ƙarav da cewa an naɗi yadda taron ya gudana cikin sirri kuma ya san inda bidiyon da aka naɗa ɗin suke.

Sarki Abdullah ya rasu ne a shekarar 2015 yana da shekara 90, kuma ƙaninsa da suke uba ɗaya ne ya gaje shi, wato mahaifin Mohammed bin Salman, sannan ya naɗa Mohammed bin Nayef a matsayin yarima mai jiran gado.

A shekarar 2017 aka sauke Mohammed bin Nayef aka maye gurbinsa da Mohammed bin Salman. Sannan ya rasa muƙaminsa na ministan harkokin cikin gida kana aka yi masa ɗaurin talala kafin a ɗaure shi a bara kan wasu tuhume-tuhume da ba a bayyana ba, kamar yadda rahotanni suka ce.

Bayan da aka hamɓarar da Mohammed bin Nayef ne sai Mr Jabri ya tsere Canada.

Ya ce a cikin hirar wani abokinsa da ke aiki da hukumar leƙen asiri ta Gabas ta Tsakiya ya gargaɗe shi cewa Mohammed bin Salman zai aika wata tawaga don kashe shi a watan Oktoban 2018, kwanaki kaɗan bayan da jami'an leƙen asirin Saudiyya suka yi wa ɗan jaridar nan Jamal Khashoggi kisan gilla a Turkiyya.

Ya yi zargin cewa wata tawagar mutum shida ta sauka a filin jirgin sama na Ottawa amma aka mayar da su bayan da jami'an fasa kwabri suka yi zargin cewa suna ɗauke da "wasu kayayyakin da ake zargi na gwajin ƙwayoyin halitta."

A bara, Mista Jabri ya zargi yarima mai jiran gado da ƙoƙarin yin kisan kai a wata ƙara da ya shigar wata kotun tarayya ta Amurka.

Yariman ya yi watsi da zarge-zargen. Ya kuma yi watsi da zargin hannunsa a kisan Jamal Khashoggi, duk da cewa binciken hukumomin leƙen asirin Amurka ya tabbatar da cewa ya bayar da umarnin aikata hakan.

King Abdullah bin Abdulaziz (front left) and then-Prince Salman bin Abdul Aziz (R) attend a festival on the outskirts of Riyadh, Saudi Arabia (18 March 2008)

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Sarki Abdullah (daga hagu) wanda ƙaninsa da suke uba ɗaya Salman (daga dama) ya gaje shi bayan rasuwarsa a 2015 yana da shekara 90

BBC ta tuntuɓi gwamnatin Saudiyya don jin ta bakinta a kan zarge-zargen.

A wata sanarwa da ta aika wa CBS, ofishin jakadancin Saudiyya a Washington ya bayyana Mr Jabri a matsayin "wani tsohon jami'i da aka kora da ya daɗe yana shirya ƙarerayi da jawo ruɗani kan ɓoye ayyukansa na almundahana da ya aikata, da ya suka haɗa da biliyoyin daloli da ƙawata rayuwarsa da ta iyalansa."

Ƴan Saudiyya da dama sun shigar da ƙarar Mr Jabri kan cin hanci kuma wani alƙali ɗan Canada ya rufe asusun ajiyarsa yana mai cewa "akwai shaidu da dama da suka nuna almundahana."

Ya yi watsi da zargin satar kuɗaɗen gwamnati, yana mai cewa tsoffin wuraren aikinsa ne suka yi masa kyautukan bajinta.

A watan Nuwamban da ya gabata, wata biyu bayan da mahaifinsu ya shigar da ƙarar yarima mai jiran gadon, sai wata kotun Saudiyya ta yanke wa ƴaƴan Jabri hukuncin ɗaurin shekara tara da rabi da kuma shekara shida da rabi a gidan yari, bisa laifin halatta kuɗaɗen haram da kuma "ƙoƙarin tserewa daga ƙsar."

Amma sun musanta tuhume-tuhumen.

Wasu kotunan ɗaukaka ƙara sun sake tabbatar da hukuncin a wata ƙara da aka saurara a asirce wadda ba su halarta ba.