Saudiyya: Yadda aka yi Allah wadai da casun da aka yi a bakin ruwa a Jeddah

Bayanan bidiyo, Yadda casu a bakin teku a Jeddah ya haifar da ce-ce-ku-ce

Wani bidiyo da ya nuna mata da maza sanye da kayan ninkaya suna cashewa a bakin ruwan Jeddah ya haifar da ce-ce-ku-ce a Saudiyya.

Wasu ƴan ƙasar sun fito shafukan sada zumunta suna yin Allah wadai da bidiyon wanda kamfanin dillacin labarai na AFP ya yaɗa, yayin da wasu kuma ke ganin sauyi ne aka samu.

Bidiyon ya nuna maza da mata suna rawa, wasu mazan ba riga, yayin da mata kuma suke sanye da tufafi ke bai rufe jikinsu ba.

A Saudiyya ba a saba ganin cuɗanyar mata da maza ba, amma bayan shekaru huɗu, yanzu abubuwa sun sauya.

Sauye-sauyen gwamnatin Saudiyya yanzu ya ba matan ƙasar damar sanya kayan ninkaya da yin casu a bakin teku a Jeddah, wani abin da ake ganin sabon mataki da ba a saba gani ba da kuma yi wa mata sassauci a ƙasar.

Wasu ƴan Saudiyya da suka yi Allah wadai da casun, sun ce wannan abin kunya ne ga Saudiyya, wanda kuma ya saɓawa tsarin addinin Islama.

Wani mai amfani da Twitter, Bassam al-Zamel ya ce "wannan abin kunya ne ga waɗanda suka amince da wannan a ƙasarmu. Ga Allah muka dogara"

Wani mai yin tasiri a shafukan sada zumunta a Saudiyya The Boss ya kira labarin da cewa "na ƙarya ne" yana mai cewa "wannan ya nuna girman irin yadda wasu ke son ɓata sunan Saudiyya.

Wasu kuma da ke goyon baya, sun bayyana al'amarin a matsayin wani gagarumin sauyi.

Wata mai amfani da shafin Twitter Marta Hommei, ta wallafa hoton bidiyon AFP, tare da yin tsokaci cewa "Wannan ba bakin tekun Miami ba ne, amma bakin teku a Saudiyya.

A cewar Amal (John Khoj) "wannan ba komi ba ne. Duk ƙasar da aka tafi za a ga irin haka."

Hamdan ya ce: "Wannan casu ne keɓaɓɓe na baƙi, ba wuri ba ne na kowa."

Abu Saleh al-Yafei ya mayar da martani inda ya ce "gaskiya ne akwai wurare na hutawa (karkashin doka) Saudiyya alƙibla ce ta Sallah ga musulmi da addini, al'adunta ba za su bar tsaraici da karuwanci ba."