Saudiyya ta amince mata su kama otal

Matan Saudiyya
Bayanan hoto, Mata a Saudiyya sun samu izinin fara tuka mota, da zuwa kallon wasan kwallon kafa duk a wani mataki na kawo sauyi da Yarima MBS ke yi a kasar

A wani mataki na janyo hankalin masu yawon bude ido, hukumomin Saudiyya sun sanar da cewa za a bai wa mata da maza 'yan kasashen waje damar kama dakin otal guda ba tare da an bukaci su bada shaidar alakar da ke tsakaninsu ba.

Amma 'yan asalin Saudiyya ba sa cikin wadanda za a bai wa wannan dama, inda su dole sai sun bayar da shaidar alakarsu.

Sai dai a yanzu dukkan mata ciki har da na kasar su na da 'yancin kama dakin otal ba tare da wata fargaba ba.

A baya dai matan Saudiyya ba su da damar yin wasu abubuwa ba tare da muharrami ba ciki har da zuwa otal.

Yarima Muhammad bin Salman na kokarin kawo sauyi a kasar, inda ko a watan da ya gabata gwamnati ta sanar da ba da Visa ga masu yawon bude ido.

Wannan wani kokarin fadada kudaden shiga ga Saudiyya tare da rage dogaro ga man fetur ne.